Chapter 35

9.5K 489 37
                                    

Last chapter 😁

"Kallonsu takeyi tamkar a mafarki, ta runtse idonta ta bude tana sauke su akan adyan dake facing dinta ya kura mata mayun idanuwansa masu hargitsa mata lissafi, inna tace da ita, ah ah autar inna ya haka kuma? baki ga baki bane ba? Siddiqa tadan rusuna kasa tana dafe cikinta tace, ina wunin ku mom? Ta kallo sashen daddy, a zuciyarta tace, yanzu daddy ne dama mahaifina?a sanyaye tace ina wuni daddy kunzo lfy? Ya gyada kai cike da kwarjinin sa yace lafiya kalau siddiqa mun same ku lafiya? Tace lafiya lau, ta samu waje kusa da najwa ta zauna sun sakarwa juna murmushi , duk motsin da tayi akan idon adyan takeyinsa, shi gaba daya ma har ya manta da cikin dake jikinta ji yakeyi kawai kamar ya rungume ta yaji duminta.

Mom ta sauke ajiyar zuciya sannan tace kai tsaye, jidda munzo ne tafiya da siddiqa....!

Inna ta ware ido dan a tunaninta ma ko takardar saki ce suka kawo musu, tace ban gane kunzo ku tafi da siddiqa ba hajiya? Sanin kanki ne aure tsakanin siddiqa da adyan ya haramta, kada fa wannan kafewar tasu tasa ka ku aikata sa'bon Allah mana...

Daddy yace, jidda akwai aure a tsakanin adgan da siddiqa..!
Gaba daya sai da gabansu ya fadi, idanuwansu tsak akansa.
Mom ta kalli adyan kwalla sun ciko mata a ido sannan ta riko hannunsa tace, adyan ba daddy bane mahaifinka.....!

Idanuwansa kamar zasu zazzago kasa, kirjinsa yahau bugawa, siddiqa kuwa sai da cikinta ya katsa saboda tsananin mamaki, najwa tace cike da tsananin mamaki, mom what are you saying? Idan ba daddy bane ya haifi ya adyan waye ya haifesa?

Mom ta fashe da kuka, mahaifinka shine yayan daddy dinku,daddy yace ya isa haka ya juyo ya kalli adyan dake zubarda hawaye, wato dama ba daddy ne ya haife sa ba? Dama duk wannan lokacin rikonsa kawai yakeyi?

Kada kasa a ranka cewa bani ne mahaifinka ba, haihuwarka ne kawai banyi ba amma nine na raine ka, ya al'amin ya bani kai tun kana dan shekara daya, ya kalli inna, ki yafe ni jidda, kamar yarda nayi alkawari na dawo amma a kurarren lokaci, saboda na tarar da yayana a cikin ciwo rai a hannun Allah, kasar Germany mukaje kaishi wajen likita dan ance mana yana fama ne da brain cancer, ya runtse idonta muna isa Allah yadauki ransa, ya bar min wasiyya akan na auri matarsa sannan na rike masa adyan tamkar dana dana haifa,........

Kukane kawai ya subuce wa adyan, siddiqa ma hawaye takeyi, a wani sashen na zuciyarta dadine cike taf zata komawa rabin ranta adyan.

Bayan watanni hudu.

Canada.

A yaune nakuda ta riski siddiqa gashi ita kadaice a gidan, da kyal ta karasa dakinta ta jawo waya ta saka kiran adyan, yana cikin wani meeting ne kiran ya shigo masa, bai dauka ba sakamakon shine ya saka roles na kada a dauki waya idan har ana cikin urgent meeting , jin bai amsa ba sai siddiqa ta cije bakinta, ta saka kiran dr arjun kira daya ya dauka, dakyal take magana kafin daga bisani ta saki wayar tana dafe katoton cikinta, minti goma kacal sai ga dr arjun da saiham sun iso, daukarta sukayi kawai zuwa hospital.....

Adyan ya fito meeting direct office dinsa yaje ya zauna yana sakin lumfashi text ne ya shigo masa ya duba a kasalance, mikewa yayi kamar wani zararre yabar company din hankalinsa a mutukar tashe..

Yana zuwa ya tarar da bouncing baby boy dinsa mai mutukar kama dashi, duk features din babansa ya dauko, siddiqa dake kwance a gadon asibiti ta gama jigatuwa sai barcin gajiya takeyi, ya dawo kusa da ita ya zauna yana shafa gefen fuskarta yana kara jin sonta na shigar shi, ahankali ta bude idanuwanta da sukayi nauyi,ta sakar masa murmushi mai sanyi, ya dago mata baby yace, this is our sign of love, ta kurawa yaron ido, adyan sak,tace Allah ya raya mana shi, adyan yace amin ya rabbih.

Washe gari mom tayi ta masa fada akan ya maido siddiqa gida a bata kulawa mai kyau ita da baby, adyan ba dan son ransa ba dan kuwa bashi da wani hutu CONTRACTs ne dayawa a kansa, hakanan ya kira jabir ya fada masa zai sako siddiqa da baby a jirgi yaje ya dauke su.

Boyayyar soyayyaWhere stories live. Discover now