chapter 7

6.8K 405 3
                                    


Allah ya jikan musulman da suka rasu amin

"A Haka rayuwa taci gaba da tafiya tsakanin Adyan wanda yake cikin holewar sa a kasar canada,  tare da budurwar sa kuma son ransa wato SARA,hankalinsa  a kwance yake dan a yanzu har ya fara shiga company dinsu a matsayin normal staff,dan daddy dinsa yace sai yaga kwarewarsa a fagen aikin nasu kafin ya bashi CEO din da yake kwadayi,duk da adyan mai girman kai ne da son girma haka yake ta kokari copping dan yasan daddy dinsa baya magana biyu.

A bangaren siddiqa kuwa, itama dai rayuwa ta dan ci gaba duk da dai ba wani ci gaban a nata bangaren,a halin yanzu dai har sun zana jarabawar su ta waec kuma suna ta shirin bikin zuwaira kawarta kuma aminiyarta ta hannun dama.
A wannan lokacin al'amarin siddiqa ba karamin saka inna damuwa yayi ba,samari dai gasu nan  suna cewa suna son ta kuma dukkansu yan gidan mutumcine,amma sai ta bin'gire tace ai ita karatun ta zatayi,duk da tasan cewa basu da wani hali na daukar nauyin karatun jami'ar.
ya idriss kuwa har yanzu yana nan yana ta faman jiranta,shi a wajen sa siddiqa na mutukar burge shi dan kuwa ba duka yaran garin bane suke kwadayin ci gaba da karatu har matsayin jami'a,ya cike mata form na jamb kuma ta samu maki mai kyan gaske,a halin yanzu dai results kawai ake jira ya fito ya waec.

"Yau sukeyin party dan haka gaba daya siddiqa na cikin busy sosai,tun safe sukaje gidan lalle sune basu dawo ba har sai da azahar,ya idriss ne ya saka a kira masa ita,tana zaune a tsakar gida,dan a nan gidan nasu dama suke zaman sitting dinsu.
   Yarone ya shigo dan wajen su zuwaira,ya kalli siddiqa dake ta faman kyalkyata dariya yace,ya siddiqa wai kizo inji ya idriss yana kiranki a waje..

   Gaba daya yan matan dake wajen suka shiga ihu suna janta, matar lecturer matar babban yaya,ta kaiwa zuwaira duka a baya,ke dama ba'a sirri dake koh munafuka,zuwaira ta kwashe da dariya,kidai gama yangar taki ta gulma dan dole ne a yarda da yayana ko ya kuka ce,ta kalli kawayensu,suka hau shewa,siddiqa ta girgiza kai ta jawo hijabinta ta saka ta fice tana fadin,ku dai wallahi anyi ja'irai nidai nayi tafiyata sai ku zolayi ku'rata...

"A tsaye ta tarar dashi can wajen wata bishiyar mangoro dake kusa da gidansu,tana jin nauyin ya idriss sosai,a sanyaye ta karasa hade dayi masa sallama,ya amsa a sake yana murmushi har yar wushiryarsa ta bayyana.

    A natse yake kallonta kafin nan yace,ya shirin partyn naku? Siddiqa tace a takaice,lafiya lau ai har mun gama duk wani shirye shiryen mu,ya idriss yace to madallah ga wannan ko ya miko mata wata bakar leda,ta dan kalleshi miye wannan din?yace amsa mana idan kin bude ai kya gani ko?tasa hannu cike da girmamawa ta amsa tana fadin nagode Allah ya kara bu'di mai albarka,ya girgiza kai babu komai siddiqa tawa,tayi saurin kallonsa,yana murmusawa yace,ko ba tawan bace ba huh?ta sauke kai kasa da sauri,yayi dariya kada na tsayar dake anan kije ku gama shirin naku,ta gyada kai kawai ta fice abunta.
Tana zuwa zuwaira ta jata zuwa daki tana kwace ledar hannunta,mu gani mai aka samo mana dan ya idriss ke kadai ke cin kudinsa,siddiqa ta fada kan katifa tana sauke lumfashi,lah lah ashe ango din ne yayi miki,zuwaira ta bude kayan anyi musu dinkin zamani,sai sabulu da kuma turare da mayafi,ita dai siddiqa ta rasa ya zatayi da ya idriss yaki sakar mata ma'ra kullum tana kokarin fahimtar dashi,amma a banza.

Washe gari da karfe 12:30 aka daura  auren zuwaira tare da saurayin nan nata yusuf mai shagon kayan kwalliya.
   Ankai amarya gidan ta lafiya dan madaidaici,siddiqa kawai aka bari tare da ita dan siyen baki,sai zolayarta takeyi,toh matar yusufa asha kwalliya har ayi amai hoda da janbaki,zuwaira tadan leko daga cikin mayafin ta,ke yar duniya bansan sa idon banza,siddiqa ta rike baki,yanzun nan ke dama duk kukan karya kike yi?zuwaira tace,toh ya na iya idan banyi ba ace son aure da miji,kinga gara kawai nayi na karyar na zauna lafiya da surutun mutane,siddiqa ta kwashe da dariya,a haka ango da abokansa suka shigo,suka biya kudin siyen baki sannan siddiqa ta fice zuwa gida,duk da samarin ba karamin rudewa sukayi ba da sukaga kyakkyawar budurwa wato siddiqa kenan, sai rokonta sukeyi wai zasu ajiye ta a gida amma inaa tace musu ai su barshi kawai ita matar aure ma ce..

Boyayyar soyayyaWhere stories live. Discover now