Chapter 25

6K 373 13
                                    


Alhamdulillah sisters am done with my exams... 🤓

"Inna ta kalli zuwaira dake zaune a saman taburma tana cin masa, wai ni zuwaira ya na ganki ke daya ne ina ummy din uwar kuka? Zuwaira tace, mun hadu dasu inusa ne,sune suka sure ta wajen wasa amma ina tunanin tana gidan mu yanzu(ummy diyar zuwaira ce)

Inna tace haba shiyasa banji kukanta ba, gashi ma har halawa na ajiye mata da aka bamu na wajen sunan jikar halima ne, zuwaira tayi murmushi, gata kuwa sai kace shazumami wajen son zakin tsiya, nayi nayi da babanta ya daina dirko mata kayan zakin nan amma ina yaki ya dainawa.

Inna tace ai dama shi yaro indai akace miki ya saba da shan zakin nan toh sai anyi da gaske suke dainawa, zuwaira tace ai kuwa dai nidai ma na gaji ne ma inna.

Inna ta mika mata yar wayarta tocila rakani kashi tace, amsa nan ki naimo min yar inna, tun jiya da daddare nake faman nemanta na sanar da ita dan'uwanta na wajen halima ya shigo garin nasu amma wayar bata shiga, ko nice ne ban iya ba oho.

Zuwaira ta amsa tana fadin, kinsan inna kwana biyu garin nan Service din MTN sai a slow, nima nan sai da baban ummy ya bani aton wayarsa ne na samu kiranta shekaran jiya, ta lalobo numbar siddiqa ta dankara mata kira, shiru bai shiga ba, inna tace, ina jin ko bata da caji ne ko, zuwaira tace anya kuwa inna, kinsan habuja fa ance basa rabo da wutan lantarki ba kamar nan bane ba, inna tadan yi jim kafin ta mike, toh dai kinsan halin kawar taki da rashin kula in ma da kwai din lalacin zai iya hanata sakawa cajin, zuwaira tayi dariya haba inna ai nasan birni ya canza ta.

"A cikin barcinta ne taji kamar ana ruwan sama a kanta, a firgice ta mike da saurin ta tana gwale idanuwanta.

Adyan ne a tsaye rike da robar ruwa a hannunsa, fuskar nan a tamke,a kasalance tace dashi, ina kwana ya...
Bai bari ta karasa ba ya hau ta da masifa, ke wacce irin gidahuma ce ne? An fada miki kinzo kasar nan dan kisha barcin kine?

Ta kura masa ido tana tunanin laifin da tayi dan kawai tayi barcin gajiya shine yake mata masifa haka.
Katse mata tunani yayi, maza tashi kiyi shiri dan nikam bani da lokacin batawa, ta kallesa tace shiri? Ina kuma zamu je?

Ya galla mata harara, mai yasa kika shiga nacin tambaya ne, koma ina zamuje ai zakije ki gani ko?
Ya wuce abunsa ta mike ita kuma, wai maike damun adyan ne? Sai kace wanda aljanu suka shiga? Mtsww lallai so na wahalar da ita.

Cikin riga da zaninta tayi shirinta tsab, ta dauko hijabi kalar kayan ta saka sannan ta fito zuwa falo.
A tsaye ta tarar dashi yana gyara zaman tie dinsa, yayi kyansa sosai cikin work attire dinsa, na kammala ta fada tana karasawa wajensa, ya juyo yana kallonta, ina zakije a haka?

Ya nuna ta sama da kasa, ta kalleshi cike da mamaki, inda zamuje mana, ya karasa gabanta, har ni nayi miki kama da wanda zai fita da mace sanye da irin wadan nan kaya a wannan kasar? An fada miki nan ma kauyen ku ne?

Siddiqa ta girgiza kai, lallai al'amarin adyan da gaske yake, ta juya a sanyaye ta koma daki, abaya ta sanyo baka da gyelenta silk mai fulawowi tana shirin fita ya leko dakin, ki dauko takardun ki, ta gyada kai sannan ta jawo akwatin ta ta fito da envolop din ta saka a cikin hand bag dinta.

A wani school mai kyan gaske da girma yayi parking, sannan ya kalleta, idan muka shiga kada ki kuskura ki bude wannan bakin naki okay?siddiqa dake ta kallon yanayin makarantar tace toh.

Anyi musu kwatance har office din shugaban makarantar, yana gaba tana biye dashi a baya, bayan ya fadawa shugaban makarantar cewa daddy ne ya aiko sa sai a take taga ya shiga murnar ganinsu har yana fadin a kawo musu coffee, adyan ne ya zauna yana gabatar da bukatar su, ya amsa takardunta ya mika masa,bayan ya duba ne a take ya bata admission bayan yayi mata dan gajeren interview, dayake makarantar kudi ce cewa yayi kawai ta fara zuwa gobe dan sun danyi nisa a semester yanzu.

Boyayyar soyayyaWhere stories live. Discover now