chapter 10

6.1K 407 4
                                    

*The Messenger of Allah (blessings of Allah be upon him and his family) has said: "Brighten up your houses through the recitation of the Qur'an, and do not make them (your homes) like graves, similar to what the Jews and Christians have done (by not performing the prayers and worship of God in their house and limiting this to the Synagogues and Churches)."*

"Bai tsaya ko ina ba sai usual club dinsu da suke zuwa, ya saka kiran jabir,fuskarsa gaba daya ta canza launi zuwa ja saboda fushi da takaicin dake damunsa.

Yan matane biyu ke ta eyeing dinsa daga can gefe inda suke tsaye sanye cikin shiga ta tsaraici,dago da idanuwansa yayi masu kyawu da kwarjini ya kallo su da bad boy side dinsa,ganin suna ta aiko masa da kallon su na yan duniya sai kawai yaja tsaki,mayu kawai am not in the mood today,dai dai lokacin ne jabir ya shigo wajen yana karasowa shima sanye da kananan kaya da suka karbe sa sosai.

Zama yayi a kusa dashi yana fadin,how far dude daga dawowarka sai kayo nan?
Adyan yaja tsaki,kashe wuta kawai abokina am in frustration yau dinnan wallahi,sai naji dama ban dawo ba wallah,jabir ya mike yaje ya dauko musu drinks ya dawo ya mikawa adyan glass daya yana cewa,I guess is something serious do you wanna share?
Adyan ya dafe kansa,sannan ya sanar wa abokinsa komai dangane da sharadin da mahaifinsa ya gindaya masa,jabir ya saki murmushi,ai ni daddy yamin dai dai ma wallahi,adyan ya wurga masa harara,hey local man kasan cewa fa am not anything close to you,jabir ya kwashe da dariya hakane amma kaga ai your dream since childhood is at stake koh?
Adyan ya lunshe idonsa ya bude cike da damuwa yace,I know that jabir amma bazan iya ba indai daddy bai amince da Sara ba toh a gaskiya I cannot marry any girl from Nigeria thats final.

"Wai ni siddiqa ya akayi kika iya wainar nan haka?wasila dake saka lomar ma'sa take tambayar siddiqa dake can gefe zaune, rike take da yusra tana mata wasa,dariya tayi dan har ta gaji da santin wainar da wasila takeyi mata,wasila tace ai dama dole kiyi min dariya,siddiqa tace,a wajen innata nake gani tanayi,kinsan har sana'arta tayi shekarun baya,wasila tace haba nidai da ince,suna ta firar su har abban yusra ya shigo gidan cike da murnar sa..

Wasila ta mike da sauri tana fadin,yadai abban yusra murna haka kamar an biya maka kujerar hajji?yana kokarin zama a kujera yace,kai wasila kin cika zolaya yanzu dama sai an biya wa mutum kujerar hajji yake murna haka a wannan zamanin? Siddiqa tayi murmushi tana fadin,ai kuwa dai,wasila ta kallesu duka tana cewa,ai dama dole ku hade mun kai tunda kun mayar danI Aku sarkin surutu...

Abban yusra yace,yi hakuri matas dama sakone daga hajiya balaraba daga abuja,wasila na kokarin zama a kusa dashi tace,Allah sarki tun bukin mu bamu sake ji daga gare su ba ashe sun dawo kasar?

Abban yusra yace eh ai munyi waya dashi arfat din month ago kenan yake ce min dukkan su sun dawo kuma jikin hajiya balaraba yayi sauki,kin ma ga katin buki ne aka aiko dashi..
Wasila tace Allah dai yayi arfat an kusan zama ango,abban yusra ya mike yana fadin,sai kuyi shiri dan sati mai zuwane daurin auren..

Da daddare wasila ta tir'ke siddiqa akan cewa sai ta bisu zuwa garin abuja sun sha bikin,siddiqa gaba daya hankalinta na wajen kiran da mai gadi yace zai musu yake,duk da an kusan hada sati kenan babu wani labari daga garesa,amma duk da haka bata cire rai ba..

Wasila ta lura da damuwar siddiqa dan haka tace da ita,kada ki damu siddiqa ko muna abujan ne ya kira ai sai mu dawo ko?duka awa ne daga nan zuwa can,siddiqa taja lunfashi,toh shikenan Allah ya kaimu lafiya.

"Sati na zagayowa suka hau shiri,wasila da kanta tajata zuwa kasuwa tadan siyo mata atamfofi masu arha ba laifi ta dinka mata dogayen riguna na fita kunya,ganin irin suturun da take dasu gashi kuma inda zasuje garin manyan mutane ne..
Sun shigo garin abuja karfe uku na rana,sai kunga kallo wajen siddiqa dan kuwa tunda take a rayuwarta bata taba fita daga jahar katsina ba,yau dai gata a birnin tarayya habuja ,ta lumshe idanuwanta tana shakar iska daga window ,adyan ne kawai ya fado mata a rai,duk da sallolin da take tayi dan Allah ya cire mata son sa amma kamar batayi,dan kuwa kullum da tunaninsa take kwana dashi take tashi..

Boyayyar soyayyaNơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ