Chapter 34

5.4K 367 13
                                    





"Inna na farfadowa ta rirrike siddiqa ta shiga kuka mai tsuma zuciyar mai saurare, hankalin siddiqa ya tashi kwarai da gaske, ta shiga shafa bayanta tana fadin, inna mai ya faru? Mai yasa kike kuka haka? Inna ta dago tana kallon daddy dake zaune a gabansu duk zufa ta jike shi tsab, ta nuna shi da yatsan ta, wannan...

Wannan.... muryarta ta hau rawa, adyan gaba daya ya rasa wai ke faruwa ne?haka..
Kamar saukar aradu sukaji inna tace, SHINE ABBANKI shine mahiafinki daya tafi ya barmu shekaru 19 kenan da suka wuce....!!!!!!!!!!!!!

Gaba daya falon sai da suka girgiza wutar su a take ta dauke... adyan zubewa yayi kawai jagwab a kasa hakama najwa da mom, zuwaira kuwa ware ido tayi tana dafe kirjinta.

Siddiqa ta mike da sauri tana girgiza kanta, ya zakice daddy ne mahaifina inna? Hakan ai bazai taba yiwuwa ba ta dafe kanta dake sara mata.
Inna taja lumfashi shine ya haidar shine mahaifinki siddiqa shine wanda kika fito nema.. .

Mom ta mike a harzuge,wannan ai zancen banza ne ya za'ayi kice mahaifin adyan shine mahaifin siddiqa....
Daddy ya tsaida ita da fadin, ya isa! Duk abunda ta fada haka yake! Adyan gaba daya ya rasa mai ma zayyi, this cant not be possible!!!!

Zaune suke duka a falo bayan minti sha biyar da suka shude ana ta kacenace..

Daddy ya kalli sashen mom da adyan da najwa yace dasu,tabbas na auri Jiddah a kasar niger shekaru sha tara da suka wuce, gaban Adyan ya shiga lugude hakama na siddiqa dake rakube tana goge hawaye hankalinta a tashe.

Mom tace kuma ka tabbatar da cewa ita siddiqa yar kace?
Daddy ya sauke kai kasa, kafin na baro kasar nasan da cikin JIDDA(kuyi hakuri idan kunji canjin sunan INNa)
Indai har siddiqa yar tace toh tabbas nine mahaifinta .....

A tare siddiqa da adyan suka mike gaba daya kalmomin daddy jinsu sukeyi tamkar a mafarki, siddiqa ta dafe kanta dake juyamata, ita da adyan mahaifinsu daya, a take ta sulale ta fadi kasa a sume.

Farfadowar da zatayi kawai taga kanta a gadon asibiti zagaye da mutane, suna ganin ta bude ido ne suka hau yi mata sannu, daddy na gefe mom na bakin kofa adyan na tsaye a kusa daita, sannu a hankali duk abunda ya faru ya shiga dawo mata a kwakwalwa.

Azabure ta mike zaune tana rirrike adyan ta fashe dakuka, ya ady yanzu yazamuyi kenan huh? Bazaka sake ni ba ko? Ni bazan iya rayuwa babu kai ba, ba karamin tausaya mata sukayi ba, idanuwan adyan sunyi ja yama rasa taya zayyi controling kansa, wannan wane irin jarabtane ya same su?

Dr ne ya shigo dauke da murmushinsa, ya kallesu yana fadin, kaine mijinta? Ya gyada kai a sanyayensa, daddy yace da fatan komai lafiya, inna ta buga tagumi,dr yace well komai lafiya stress ne kawai suka sauke ajiyar zuciya a tare, dr ya mikawa adyan takarda, sai dai kuma... Adyan yace tell me dr Please!
Dr yace Congratulations your wife is pragnant, tana dauke da ciki wata biyu.....

Dam gaba daya sai da hancin cikinsu ya kada, adyan ya yi waje da sauri dan yama rasa wai maike faruwa ne! Wannan wacce irin kaddara ce? Ya auri kanwarsa!!nooo it bee!!

Najwa ce rike da siddiqa har suka shiga gidan mom, inna dai da zuwaira neelam tazo ta dauke su, itama dai zancen ya girgiza ta sosai.

Mom ta kalli daddy... kada ka fara alhaji! Bazan taba yin abunda kake so ba, nayi alkawarin ajiye wannan sirrin har karshen rayuwata ko ka manta alkawarin daka dauka ne? , daddy ya dafe kansa, yanzu bazaki tausayawa wadan nan yaran ba? Mom ta mike a harzuge, i prefer to be the villain stay out of my way...ta fice daga dakin tana banko kofar, daddy yaja lumfashi yana tausayawa halin daya ga inna aciki lallai dolene ya taimaka musu tunda siddiqa diyarsa ce dolene ya zamo uba mai kulawa a gareta.

"Bayan kwanaki uku, a halin yanzu inna ta tarkata diyarta sun dawo katsina, duk wani taimako da daddy yake sonyi musu tace bataso ya barshi tunda har suka iya rayuwa babu taimakon kowa a baya yanzu ma zasu iya basa son taimakon kowa, adyan kuwa rayuwa tayi masa zafi kullum yana cikin dakinsa yana fama da tunane tunane, jin wannan al'amarin yakeyi tamkar wani almara,.

Bayan watanni uku.

A wannan lokacin idan har kuga halin da adyan yake aciki sai kun tausaya masa mutuka, a kowane safiya sai mom ta riske shi da maganar Sakin siddiqa tayi ta convincing dinshi akan aurensa da siddiqa ya haramta, dolene su hakura da junansu shine kawai mafita, he have to move on with his life, shiru kawai yakeyi mata dan ya zama mutum mutumi najwa kadai ce ke iya basa abinci yaci, ya rame ya lalace, ya koma tamkar wani mai fama da ciwon hauka, idan kuwa yana barci mafarkan siddiqa yakeyi masu muni, daddy shima dai ba kanta dan kuwa ciwon zuciyarsa kullum sati sai ya kwanta a asibiti, mom duk wannan bai hana ta karaya ba, anty kausar ma tazo kwana biyu ta tarar da family din cike da abun tausayawa, jabir ma yana hanyar dawowa daga Spain 🇪🇸 tare da marwa dan ceto abokinsa da matarsa.

A wajen siddiqa kuwa damuwa da kuka sun zaman mata jiki, tun inna na faman lallashinta harta gaji tayi mata wa'azin harta gaji, tana so diyarta ta fahimci cewa dolene auren su da adyan yazo karshe, yanzu kam cikinta ya fara dan girma tana masifar son cikin nan dan kullum zakaga hunnanta akansa tana shafawa, karatu kuwa tama cire ranta ganin har lokacin shiru babu wani bayani daga adyan, neelam da afreen sunzo sau biyu ganinta harma da zaitun.

Yaudai a sume mom ta tarar da adyan a bakin kofar toilet ba rai, hankalinta yayi masifar tashi, bayan sun kaishi asibiti ne doctor yace ai yakamu da ciwon zuciya, hankalin mom ya tashi atake ta sulale kasa tana kuka cike da nadama, daddy ya duka wajenta yana fadin, kin ga dai inda taurin kan ki ya kai ki ko, yanzu dan Allah a haka kike so muyi rashin dan mu?
Ta fashe da kuka naji alhaji zan fayyace wa kowa gaskiya, idan har adyan ya farfado zamuje katsina....

Washe gari daga asibiti direct hanyar katsina sukayi, adyan na kwance a baya yana fama da zugin da zuciyarsa ke masa, idan har akwai abunda yake son ganin toh kowa fuskar siddiqa ce.

Sai yamma likis suka isa, najwa ta tabo shi muje ko ya ady, ya kalleta kawai sannan yayi yunkurin fitowa, ganinsu a kauye sai kansa ya daure, najwa tayi murmushi inshaAllahu your sorrows will soon all be gone ya ady, ya kalleta cike da mamaki.

Kika buga wani uban tagumi? Zuwaira ke fadin haka tana kokarin zama a kusa da siddiqa dake tayata yanka kubewa.
Zawaira tace, wallahi ki daina wannan zaman zugum din, kindai san bake kadai bace ba yanzu ko?

Siddiqa taja dan tsaki, wayace miki wai tunani nakeyi ne huh? Daga mutum yadan huta bakinsa daga magana sai ki hau wani basa darasi, zuwaira tace maida wukar ni bani kubewa ta indai ke zaki yankata ai inaga sai gobe ne zamu ci tuwon, siddiqa ta tura mata bowl din gabanta, yaro ne yayi sallama, zuwaira tace ah ah sama'ila anty murja ce ta aiko ka ko?

Yaro yace ah ah anty zuwaira dama innar anty siddiqa ce tace wai nayi kiranta taje gida yanzu, suka kalli juna, zuwaira tace sai ki tashi kije kin baro inna ita daya, siddiqa ta mike tace naso babyna ta dawo islamiya na kwashe ta muje gidan inna tare, dan nadan sha dariyar shirmen ta, zuwaira tayi dariya kada ki damu zan turo miki ita, ta dauki hijabin ta ta saka tayi gidansu tana mamakin kiran miye haka inna ke mata cikin gangawa haka?


Please
Vote
And
Comments
Instagram @ am dija

Boyayyar soyayyaWhere stories live. Discover now