Chapter 33

6K 380 24
                                    


"Sai safa da marwa kawai takeyi a tsakar falo, ta rasa ina zata saka kanta dan fargaba da damuwa, yanzu mai zata fadawa inna kenan? Tayi aure yanzu a kalla watanni 6 kenan amma bata sanar da ita ba a matsayin mahaifiyarta? Taja lumfashi hade da shafa fuskarta da har zufa ta fara keto mata.

Adyan ne yayi sallama ya shigo cikin saurinsa, kiran sa da tayi ne dazun daya dawo gida akwai matsala shine yasa shi barin aikin dake gabansa ya taho a zaton sa ko wani abun ne babba ya faru da ita, jin muryarta kamata razane.

Ganinta a tsaye yasa shi karasawa da saurin sa yana fadin, whats going on? Siddiqa ta juyo ta rungume shi da saurinsa tana sakin kuka, hankalinsa ya kara tashi sosai, lafiya my special mai ya farune wai? Ki fada min mana.

Ta dago tana rike da hannunsa tace, wai inna ce tamin waya ta shigo abuja...
Adyan ya wani banka mata harara, sai kuma akayi mai?miye abun tashin hankali anan?

Ta tsaya kallonsa, bata fa san nayi aure ba ya ady..
Ya girgiza kansa, wallahi har yanzu yarinta na damunki, miye abun tashin hankali a nan? Inna tazo sai muje mu gaishe ta kiyi introducing dina a wajenta, wato shiyasa dana ce muje katsina mu gaishe ta kika ce mu bari sai mun dawo next month ko? Yasa hannu yaja kunnenta, ta saki kara cike da shagwaba wallahi ni kunyar inna nakeji shiyasa, adyan yace ke ce ai kejin kunyar, ni kam ban gane miye na kin fada mata ba,ya rungumo ta, kada ki damu kinji inna zata fahimce ki, ta gyada masa kai, yace yanzu muje gidan neelam tunda suna canko? Ta sake gyada masa kai tana murmushi.

Neelam ma dai hankalinta a tashen yake, tasan cewa ta wuce wuri dayawa, daga bata amanar yarinya sai ta bingire da aurar da ita, dakin data sauke su ta shiga dauke da tray a hannunta, zuwaira tayi saurin mikewa taje ta amshe ta, sannu anty neelam, neelam tayi murmushi kune da sannnu zuwaira ta duka har kasa ta gaishe da inna dake saman darduma tana jan carbi.

Ina wuni inna kunzo lafiya? Inna ta ce lafiya neelam mun same ku kalau? Neelam tace lafiya lau inna, gashi kuma mai gidan nawa baya nan hakama murad dan nawa.
Itama dai siddiqa bata nan a yanzu amma dai suna hanya, inna tace ai babu damuwa tunda mune mukayi muku zuwan ba zata.

Sai yamma sosai ne su siddiqa suka iso, ta makale a cikin mota taki fitowa gabanta na faduwa, da kyal adyan ya shawo kanta ta fito ya riko hannunta , kirjinta sai bugawa yakeyi, idan inna bata amince da wannan auren ba ya zatayi kenan,? Ita dai tasan cewa bazata iya rayuwa babu adyan ba.

A falo sukayi kicibis da su a zaune, zuwaira ta rungume siddiqa tana farin cikin ganin ta, inna kuwa na gefe a zaune tana ta faman washe baki taga autarta, adyan dake bakin kofa ya shigo shima hade da sallama.

Maganar zuwaira ta katse ganin adyan malaminsu mai kyawun nan, siddiqa ta karasa wajen inna ta haye jikinta tana fadin, innata sannu da zuwa nayi kewarki sau ba adadi.
Inna tayi dariya, kedai yar inna banga ranar da zaki girma ba, ta kalli adyan gashi kin bar bako a tsaye ma, siddiqa gabanta na faduwa tace, ai gidan ba bakonsa bane inna.

Adyan yayi murmushi sannan yazo ya duka har kasa ya gaishe da innar, ta amsa masa a sake dan a tunanin ta ko saurayin yar inna ne ko kuma kanin neelam ne, gashi kyakkyawa dashi.

Bayan sun zauna ne neelam ta shigo falon, sunyi magana da mijinta yana hanya kuma ya kara mata karfin gwiwar ta fadawa innna gaskiya komai ya wuce.

Inna ta kalla tace, ki yafe ni inna nayi miki babban laifi da kuma shishshigi, inna tace ban fahimce ki ba yar nan, neelam ta nuna adyan, wannan shine mijin siddiqa......!!!!!!!

Ras ras ras gaban inna ya fadi, hakama na zuwaira dake zaune abun kamar a mafarki take jin shi...

Inna ta mike da sauri, miji fa kika ce neelam yaushe akayi auren? Yaushe siddiqa tayi aure bamu sani ba?
Neelam ta mike da sauri ita da siddiqa, inna ki yafe mu wallahi bamu so mu boye miki komai ba, inna ta daure fuska tayi daki abunta.

Boyayyar soyayyaحيث تعيش القصص. اكتشف الآن