Chapter 22

6K 380 10
                                    

Salamu'alaikum.. Sorry kunjini kwana biyu, well manage this small chappy, nadan samu intervalne.


"Ware idanuwanta tayi tana kallon adyan cike da tsananin mamaki, kunya ce ta lullubeta ganin yadda duk jama'an dake wajen suke kallon su.
Kirjinta na bugawa da sauri tayi kokarin fadin, uhm..... daka da daka saukarto ani zan iya tafiyar da kaina..

Adyan ya sauke lumsassun idanuwansa a kanta, bai furta komai ba sai shiiiiiish da yace mata Kawai,
Siddiqa tayi lamo abunta tana jin wani irin yanayi da bata taba jin irinsa ba a rayuwarta..

Har cikin mota ya kaita sannan suka koma gida.
A daren ranar dai na takaice muku sai da siddiqa taga another good side din adyan, dan kuwa zama yayi kawai ya kula da ita sosai, taji dadi kwarai da kulawar da yayi mata, son sa kowa sai linkuwa yakeyi a cikin zuciyarta.

Da safe a kasalance ta bude idanuwanta da sukayi mata nauyi sakamakon barcin da tayi late..

Hango shi tayi kwance a gefenta yana faman barcinsa mai cike da gajiya,matsawa tayi kusa dashi tana karewa handsome face dinsa kallo, adyan namiji ne wanda yake wahalar samu,takai fuskarta daf da tashi tana kurawa idanuwansa dake rufe ido, she still cant believe it wai yau itace tare da adyan a haka..

Ji takeyi tamkar ta rungume sa dan so da kaunar da takeyi masa...
Runtse ido tayi kawai...tana faman imaginations dinta.

Bude idon da zatayi kenan sukayi ido hudu da adyan daya zuba mata nasa mayun idanuwan..
Wani irin ja tayi baya cike da tsoro da kuma kunyar kamata da adyan yayi...

Adyan ya mike zaune yana kallonta cike da tsananin mamakin kamata da yayi tana kallonsa whats she doing? ..

A firgice bata ma ko ankara ba ta taka kafarfa dake daure. Wani irin azabar zafi taji sakamakon tsamin da kafar tayi mata. .

Wayyo Allah na..
Ta fada tana komawa ta zauna cikin saurinta tana matse lip dinta.
Adyan ya girgiza kai, so inmatured.. Mike yayi kawai ya shige toilet abunsa ko lura da nuke nuken ta bayyi ba.

A dinning ta tarar dasu duka suna faman cin breakfast, ta karasa itama tana dan'gyasa kafarta.
Mom ta mike da sauri tana tambayarta mai ya faru da kafarta, siddiqa ta zauna tana gaishe da su, najwa ta riko hannunta mai ya same ki haka ya siddi?you where perfectly ok jiya.
Tayi murmushi tace, babu komai kawai naji dan ciwo ne..

Dan ciwo ma kikaji ko! Sukaji muryar adyan a mamakin su, mom tace wai mai ya faru ne?
Adyan ya wani shafa gemon sa yana fadin, mom this girl is so grumpy, and careless she hurt her self with the bed jiya.. And she calls it dan ciwo! Harfa hospital mukaje.

Mom da anty kausar sukace ash sha sannan suka shiga tambayar siddiqa ya jikinta..
Ita dai sai kallon adyan takeyi cike da mamakinsa, shi kuwa mikewa yayi kawai yayi tafiyarsa.

Karfe uku na yamma suka koma gidan su, marwa ma ta bisu dan bata taba zuwa ba.
Karfe hudu jabir yazo ya maiyar da ita gidan mom shida adyan.
Da daddare najwa ta samu siddiqa a kitchen sai faman hada girki takeyi tana dan gyasa kafarta.

Najwa ta girgiza kai, come on ya siddi nace miki kada ki wahalar da kanki i will buy us dinner a waje..

Siddiqa ta juyo tana fadin, ni fa kinsan ban iya wani cin irin wadan nan kayayyakin naku ba, ki barni kawai nayi dan wake na naci... Tunda ke bakya cinsa sai kije ki siyo naki kayan turawan..

Najwa ta turo baki, kin cika gardama wallah, siddiqa na wanke hannunta tace, naji din ai gara naci wanda zan koshi..
Najwa tace, toh ni zan fita naje na siyo nawa,tadan riko rigar siddiqa ko zaki rakani please? .

Boyayyar soyayyaWhere stories live. Discover now