chapter 3

6.6K 534 10
                                    

Juma'at mubarak♥
May Allah forgive us our sins and guides us to the right path AMEEN

Da kyal jabir da neelam suka bawa malam garba hakuri yayi wa sidduqa uzuri.

   Siddiqa ta mike da sauri zata fice sakamakon tsawar da malam garba ya daka mata.
   Tadan kyallo sashen da adyan yake sannan ta fice da saurin ta.

"Inna wallahi jummai ba zata bamu aron tan'dar(masa pan) ta ba fa,kinsan tun lokacin da maman ramla tayi aronta ta ba ta mata shi da soson karfe,tun lokacin ta daina bayarwa mutane,siddiqa ke fadar haka,ahalin yanzu du'ke take tana faman wankin uniform dinta.

Inna dake faman wanke wanken kwanoni tace, ni da Allah can yimin shiru,sai kace bansan ki da lalacin banza,nasan tafiyar ce kawai bakya so,kuma kindai san dole ke din ce zakije,dan rabe ma bazai shigo yau dinnan ba sunje gona da kawunsa.

     Siddiqa tadan turo baki,wallahi inna lungun nan nasu ya cika kwata dayawa ga jama'a yan sa ido..

Inna tayi dariya,gadai zancen nan ya fito ai,nidai ki taimaka kije dan yau wainar nan nake so ki fita da ita,ko zuwaira ce kiyi wa magana kuje tare mana nasan zata raka ki.
    Siddiqa ta ajiye kayan wankinta ta tsame hannunta ta shige daki tana fadin,ga wankin nan ki taya ni dauraye wa toh dan Allah,batayi minti uku ba sai gata sanye da hijabin tasha fa'ci dama kayan jikinta duguwar riga ce ta atamfa data kode sosai ,ta zura silifas dinta tayiwa innarta sallama ta fice.

"Gidansu zuwaira ta shiga dan dama makwaftane su dan gida dayane a tsakaninsu.

    Gidansu zuwaira gidane mai jama'a sosai dan dakuna sunkai goma aciki.
   Tana shiga taci karo da ya idriss,tayi saurin dukawa ta gaisar dashi,ya amsa a sake yana tambayarta ya karatu,tace alhamdulillahi,yayi mata fatan alkhairi sannan ya fice, a da tana ganin kyan ya idriss sosai dan yana mutukar burgeta sosai yadda yake shigarsa da kuma nutsuwarsa gashi kuma yana lecturing a university,amma bata san mai yasa ba? yanzu gaba daya wannan copper din ya tafi da tunaninta..
   
Umma ladi kawai ce a tsakar gidan tana tuka tuwu,siddiqa ta karasa wajenta tana kokarin amsar muciyar,umma ladi kawo na miki..
   Umma ladi tayi murmushi,ah ah barshi kawai siddiqa wannan aikin ya miki girma,ya innar taki?
  Siddiqa tace tana lafiya lau,zuwaira na gida kuwa?umma ladi tace eh tana nan ki shiga dakin rabi suna ciki..

Sun cika dakin tab suna ta faman kallon hausa film mai suna "kalan dangi",siddiqa ta kwalawa zuwaira kira,ta mike da saurinta da daurin kirji a jikinta ta fito suka shiga dakin mahaifiyarta.
    Siddiqa tace,nazo kimin rakiya dan Allah,zuwaira ta daka tsalle ta dire,wayyo Allah naji dadi wallahi,kamar kinsan dama a kan ka'ya nake..
Siddiqa ta kura mata ido,ban gane ba kawalli?

Zuwaira ta shiga neman kayan da zata saka tana fadin,kinsan wannan yusuf din da nake baki labari?siddiqa tace,eh ba wannan sabon saurayin naki ba mai shagon kayan kwalliya?zuwaira tace,shi din fa,yau zamu hadu dashi a lowcost kuma dama mama taje kaduna biki tamin kashedi akan kada na kuskura na fita daga gidan nan, har ya idriss ta fadawa kada ya barni naje ko ina,amma kinga tunda dakene zamu fita ba damuwa nasan bazatayi fada ba.

Siddiqa ta tabe baki,kedai wallahi kin gama zurmawa a cikin soyayyar wannan yusuf din.
  Zuwaira ta kwashe dariya,taja hannun siddiqa suka fice.

Sai da sukaje aiken inna sannan suka wuce ganawa da saurayin zuwaira.
  Unguwa ce mai dauke da manyan manyan gidaje na masu dashi,tafe suke siddiqa na faman yiwa zuwaira korafin,kan cewa yamma tayi su koma gida..
   Zuwaira ta kalleta,wai ke siddiqa mai yasa kika cika kauyancine huh?siddiqa ta harare ta naji ni bakauyar ce amma dan Allah kiyi sauri dan inna yau na tabbatar sai tayi min fada..
   Suna shan kwana zuwaira ta jawo siddiqa da sauri,siddiqa tace kin hango shine?ina yake?
Zuwaira ta nunawa sidiiqa wani gida mai kyan gaske da gani ba'a dade da gama ginin,kinga wancan gidan wai anan wadan nan yan NYSC din suke zama na makarantar mu,siddiqa ta saki baki tana kallon gidan,kai dan Allah?
  Zuwaira tace,kwarai kuwa,kinsan wannan mai dan jikin acikinsu,ya ma naji su senior khadija ke kiransa,ta daga kanta sama,yauwa uncle jabir,babansa dan siyasa ne a habuja kuma dan asalin katsina ne,toh gidan sane wannan...
  
Siddiqa ta kurawa gidan ido,dai dai lokacin sukaji an musu sallama a bayansu,yusuf ne saurayin zuwaira.
   Bayan sun gaisa siddiqa ta basu wuri,can kofar wannan gidan taje ta tsaya..
   Tana leke take fadin,yanzu wannan mai kyan yana cikin wannan gidan?
   Ta shiga leke tana tunanin saurayin nan,can taji muryar su kamar zasu fito,tayi saurin gudu ta boye bayan wata bishiya tana sauke lumfashi.

Sanye suke da kananan kaya,da gani football zasuje, adyan na kokarin saka wayarsa a cikin aljihu yace, jabir wai ina neelam da Daniel ne?
  Jabir yace, I don't know either,adyan ya tabe baki,jabir ya kai dubansa wajen su zuwaira,Dan Allah just look at that kid,duka nawa take har ta fara tsayuwa da samari..
  Adyan yaja tsaki,shi yasa nake fada maka ai,I will never marry a girl from Nigeria,gaba daya basa burgeni..
  Jabir ya kwashe da dariya,dude koya halinsu yake wallahi sunfi wadan nan fararen fatar tarbiyya.
Adyan ya yamutse fuska  yayi gaba abunsa..

Please
Vote
And
Comment
Instagram
@ dija_bature

Boyayyar soyayyaМесто, где живут истории. Откройте их для себя