chapter13

5.4K 359 4
                                    

The Messenger of Allah (blessings of Allah be upon him and his family) has said: "The superiority of the Qur'an over the rest of words, is like the superiority of Allah over His creations."

Neelam cike da mamaki sosai ta tarbi su jabir,gaba daya sunyi surprising dinta bare ma adyan datayi shekaru bata gansa ba.

Ta kallesu tana fadin,oh my gosh guys you really surprised me,adyan yayi dariya,jabir yace well can you offer us a sit?tayi saurin karasawa wajen wani empty table ta nuna musu su zauna,suka zauna hade da bata gift din da suka zo mata dashi,ta amsa tana fadin,adyan manya sai yau aka tuna dani ko?

Yayi murmushi yana hade hannayensa,am really sorry madam,tayi murmushi tana mikewa,kayan kwalama ta kawo musu dayawa,gaba daya wajen sai kallon su akeyi,bare ma yan matan dake wajen,dan a gaskiya adyan da jabir sun iya gayu na karshe ga kwarjini da kuma kyawu,samari ne masu cin zamanin su sosai..

Basu wani dade ba sukayi mata sallama akan inshaAllahu gobe zasu sake dawowa a gaisa sosai,dan basu hadu da mijinta ba da kuma danta .

Zaitun ce ta fada kan gado in da siddiqa take a zaune tana shafa wa murad mai a jikinsa gama masa wanka kenan da tayi,ai an barki a baya sosai siddi!you don miss in fada miki!

Siddiqa ta ware ido da sauri tace kada kice min nayi missing ganin couple dance dinsu anty neel...
Zaitun ta kwashe da dariya tana gyara zamanta a kan bed din tace, kinsan yau wasu handsomes ne friends din ya neel suka zo,kin gansu kuwa,ta rungume hannayenta,oh m.g ahhh so cute...

Afreen ce ta shigo tana fadin,zaituna maza tashi ki shirya arfat yana jiran mu a waje..
Zaitun tace,yauwa ya afreen kin gane wadan nan handsomes friends din ya neel dinnan na dazu?ni na gane faces dinsu dan tare da ya arfat sukayi graduating a university...
Afreen tadan daga kai sama kamar mai tunani,can tace uhmm ya neel always talked about them,yama sunan su?siddiqa dai har ta sakawa murad kayansa suna maganganinsu na shirme da take biye masa..
Kafin ta ankare sai dai kawai taji afreen na fadin,yauwa JABIR DA ADYAN..!

Wani irin faduwar gaba ne ya tsinkayi siddiqa,cike da sauri ta mike tsaye tana kallon zaitun,ina suke?jikinta na rawa kawai ta fice daga dakin cikin saurin ta...

Da gudu ta karasa waje ta shiga neme neme,addu'ar ta kawai Allah yasa ta ga adyan,lumfashi take ta saukewa tamkar wadda ta hadiye kunama,tasha neman amma inaa,gaba daya ma duk an watse daga gidan..
Muryar uncle taji mijin neelam a bayanta,yace siddi mai kikeyi ana ke daya?ta juyo a firgice tana fadin,babu komai dama dankunne na ne ya fadi shine nazo na duba shi,yace,no ki koma ciki gobe da safe tunda akwai haske sai kizo ki duba ko,ta gyada masa kai kafin nan tabi bayansa..

Gaba daya adyan ya rasa mai ke damunsa,why is he still thinking about that half face girl?yaja tsaki yana jan blanket a jikinsa,tunda yake a rayuwarsa bai taba zama yayi tunanin wata ya mace haka ba,sai dai yabar matan suyi ta fama da tunanin sa..

Ya shafa kasumbar sa dake karawa fuskarsa kyawu,who's she?ya tambaya kansa,mtswww..
What the hell is wrong with you Adyan!!!!ya shafa gashin kansa,mikewa yayi kawai ya bude side drawer dinsa ya dauko kwayoyi,bai tsaya wani tunani ba kawai ya watsa su a baki ya hadiye,kafin kace mai har barci mai nauyi ya dauke sa.

A bangaren siddiqa kuwa,gaba daya barci yayi kaura a idanunta,tunanin adyan ya dawo mata danye a cikin zuciyarta,ta mike daga kwanciyar da tayi,tunda dai har adyan yazo yau dinnan tasan gamuwar su na nan a kusa,ta dauko al'qurni ta zauna taci gaba da karanta,har asubahi akayi kiran sallah,tayi sallah sannan ne barci ma yadan dauke ta...

Washe gari da safe da ciwon kai ta tashi,dan haka neelam ce tayi wa murad wanka ta basa abinci ta shirya shi,siddiqa na daki a kwance tana fama da ciwon kai na gefe daya ,neelam ta shigo dauke da tire ta ajiye mata a kan bed din,tashi kici abinci kisha magani,siddiqa a kasalance ta mike tana fadin,ai anty da baki wahalar da kanki ba zan iya zuwa kitchen din ma da kaina,neelam tadan harare ta,yadda kike a haka?siddiqa tayi murmushi,neelam tace yau ma bazaki samu zuwa lessons din naki ba,tunda dama baki fara ba sai a bari sai gobe ko?siddiqa ta matse baki,ah ah zan iya tafiya,neelam taja hancinta,stubborn girl toh dear yace bazaki je ba..
Har neelam takai bakin kofa tace,yauwa zanyi ma baki anjima,idan cook yazo kice ya kara yawan dish din,dan dinner zasu zo,siddiqa ta gyada kai,neelam tace zan tafi da murad dan haka you just rest okay?tace yes ma,sukayi dariya a tare kafin nan ta fice.

Adyan ya kalli mom dake ta faman jibga masa abinci,har daki taje ta jawo sa ya sauko dan yaci abincin.
Ganin yarda take ta tula masa abincin sai yace,mom mom ya isa! I can't finish all this,ya kalli cikinsa yana sake fadin,look here mom I only have one stomach to feed not two...

Tayi murmushi,okay fine please eat alot my son okay?ta shafa gashin kansa,adyan yadan yamutse fuska,no mom kadan zanci,kinsan ina watching diet dina..
Mom ta zauna a kujerar dake gefensa,toh shikenan bodybuilder ni dai adan taimaka min aci ko kadan ne,tunda yau kausar zata zo bana son tayi min korafi na rashin kula dakai..

Adyan ya kai slice din kaza a bakinsa yana fadin,anty kausar zatazo what's the occasion mom?

Mom ta dafa kafadar shi,I really want to help you my son,wannan sharadin da daddy dinku daya baka nasan is not a small decision for you..
Ya ajiye fork din hannunsa,so what are planning on doing,nasan dai ba zaki iya convincing din daddy ba..
Mom tace eh hakane shiyasa na kira kausar dan ta taimaka mana da solution,ya gyada kai kawai sannan yaci gaba da cin abincinsa..

Ta wuni shiru a gida ita daya,sai karfe biyar na yamma ne neelam ta dawo gidan,ta kara shirya dinning sannan ta leko wajen siddiqa,tayi mata ya jikI sannan ta fice.
Karfe 8 siddiqa na zaune tare da murad suna games neelam ta leko dakin tana fadin,bakina sunzo nan da minti goma kizo da murad zasu ganshi,siddiqa tace toh shikenan anty.

Adyan da jabir zaune a falon neelam mai kyau da tsari,sai farin cikin ganin su takeyi,jabir yace ya kamata ku sasanta,neelam tace,ai ni bani da tacewa,adyan yayi dariya yana cewa,kinsan harkokin yau da kullum kuma balle na dade bana kasar ne,am sorry,ya hade hannayensa..
Neelam tayi murmushi,ni na isa nayi fushi da CEO guda!

A take yanayin fuskar adyan ya canza,jabir ma dai sai da jikinsa yayi sanyi,neelam ta nutsu tana kallonsu,kafin nan tace hope everything is fine?
Jabir yaja lumfashi,well adyan bai samu kujerar CEO dinsa ba har yanzu..

Neelam ta ware ido tana kallon su cike da mamaki,dan kuwa tasan long time dream din adyan kenan....

Siddiqa ta mike tana gyarawa murad zaman wandon sa,ya kalleta yace,anty kin yi wanka?
Siddiqa tayi saurin kallonsa,lah murad wari nake yi ne?ta shiga shinshina jikinta..
Ya girgiza kai,you didn't change your clothes today..

Tayi saurin kallon kayanta,zani ne da Tshirt sai hijabin data sanya,tunda tayi wanka da rana kasala ta hanata sauya wasu kayan,tayi murmushin da ban kai ciki ba,well murad mu tafi mommy is waiting...taja hannunsa da sauri tayi falo...

Gabanta ne ya fadi rass sakamakon wanda idanuwanta suka gane mata..
ADYAN ta fada a cikin zuciyarta,kirjinta na bugawa da sauri da sauri,dadi ne,tsoro ne,fargaba ne,duk suka lullube ta..
Kafin ta ankara tajiyo jabir na karawa neelam wani labari...

Neelam data gama sauraron jabir tace,yanzu ya kenan?adyan ya kamata kawai kabi umarnin daddy..
Adyan ya dago da idonsa da suka fara canza nauyi yace,haba neelam kinfi kowa fa sanin yadda na tsara rayuwarta,am not ready for any marriage now..
Neelam taja lumfashi..
Siddiqa ji tayi kawai an dafa kafadarta,tayi firfigit ta juyo,uncle ta fada da murya mai rawa..
Yace come on muje ciki mana,ta gyada masa kai hade da bin bayan sa..

Please vote
And share

Boyayyar soyayyaWhere stories live. Discover now