Thirty-three

6.9K 348 34
                                    

    
It was narrated from Abu Hurairah that the Messenger of Allah (pbuh) said "Every good deed of the son of Adam will be multiplied manifold. A good deed will be multiplied ten times up to as many as seven hundred times, or as much as Allah wills. Allah says: 'Except for fasting, which is for Me and I shall reward for it. He gives up his desire and his food for My sake.' The fasting person has two joys, one when he breaks his fast and another when he meets his Lord. The smell that comes from the mouth of a fasting person is better before Allah than the fragrance of musk."

*****
Bayan wata uku.....

  Cikin Husna yana nan daram babu inda yaje, ko kunyan idanu batayi balle tsoron Allah. Haka taketa rainon shege cikin gidan TK. Gashi sai dankarin wahala yake bata kamar zata rasu
    Hajja Zee tana mata bala’in kara, ga laulayin bala’i data keyi. Kullum kafin ta tafi shago takan shiga ɗakin Husna ta dubata.
     Shima TK hankali ya tashi sosai yanda Husna ke ciwo kala kala, shifa ya riga yayi dangana akan cewa bazai samu yaron kansa a duniya ba.
    Indai rainon ɗa ne ya taɓa yi saboda last two years suka aurar da yarinyar sister dinsa wanda suka fara rikewa tun tana shekara takwas a duniya.
    Yanzu Indai cikin nan zaiyi sanadin salwantuwan ran Husna gwara a cire kawai kowa ya huta.
     Koda ya kawo mata shawara ta daka tsalle wai dama haka ciki ya gada babu mai cire mata abinta.
  Kyaleta yayi da abinta saboda taimaka mata zaiyi, haka kuwa take shan dankarin wuya kusan kowane mako sai Nurse tazo har gida ta saka mata ledan ruwa da allurai.
     Momee kam hankalinta ya tashi sosai  yanda Husna take wahala, itama tana zuwa dubata akai akai.
   TK yana blaming kansa saboda da bai yarda da zancen zuwa asibiti ba da yar mutane bata wahala ba. 
    Itama tasan tana wahala amma Lubie ta jaddada mata cewa idan ta jure nanda watanni kadan ne zata haihu komai ya zama labari.
       Balle dama ance good things don’t come easy, dole tasha wahala yanzu kafin taji dadi nan gaba. Ta samu kwarin gwiwa sosai bayan Lubie tayi mata maganar nan.
   Kuma tabbas Lubie ta fita hangen nesa, idan za’a barta  da sakarcinta ne bazata iya duk abubuwan nanba.
     Ta hakura zata jure duk wani wahala da zai sameta cikin lokacin nan, tabbas wata rana zata mance da komai musamman idan tana cikin dollars a Bahamas tana holewa.
  Shikuma Goje Scofield tun sanda ya kasance da Husna ya kasa barin tunaninta, yana neman hanyar da zaibi yanzu ya sake mallakar ta saboda gaskiya bata gundure shiba.
    Wani rana suna lambu suna shan sholisho, wani former Pump attendant ne wanda yayi ma TK aiki amma aka sallame shi saboda shaye shaye, magana ya rinka yi magana mara kan gado.
   Anan ne yabada labarin rashin haihuwar TK da kuma auren wata karamar yarinya domin zalunci.
     Nan take Goje yayi adding 1+1 ya gane Husna ne amaryar. Murmushi yayi saiya dauko wiwi yayi wrapping sannan ya soma busa. Yanda yake murmushi na keta kasan cewa ‘karen bana ne zaiyi maganin zomon banaballe ma yanzu ya samu tsuntsu daga sama gasarshe harda guntun yaji.
   Ita kuma Lubna duk yanda taso bikinta da Minister abin ya faskara, iyalinsa sun dage sosai da addu’a.
    Maganar aure yaki kankama tsakanin su, yana bata kudi yadda ya dace amma yaki tura kowa gidansu.
     Ita kuma ta gaji da zaman gantali, duk ta kagu tayi aure amma abu yaci tura, kuma Sam bazata iya auren talaka ba koda wasa.
      Kannenta biyu sunyi aure cikin rufin asiri abinsu amma ita shiru babu wani labari mai dadi, gashi sai banka ma Minister sihiri takeyi amma abu yaci tura.
    Sukam Malaman Mai martaba suna nan suna taya Daddy da addu’a akan tarkon Anty Bilkisu.
   Tun auren Bilkisu Daddy sau ɗaya yaje Zaria kuma abin yayima mai martaba ciwo, haka ya saka fadawa mota guda suje gidansu suga Daddy sannan su taho tareda shi tunda ina Zaria ina Kaduna.
   Bataso a tafi da Daddy ba shine itama ta ɗauki mayafin ta zata bisu. Basu hanata ba tunda bazata ragesu da komai ba.
   Ita kam tsoron yaje shi kadai ne ayi masa wani addu’a karyanta ya kare.
   Mai martaba yana ganinta ya murtuke fuska yayita mata masifa, ga uwa uba fadawa sai zugashi sukeyi maimakon bashi hakuri.
   Rokon gafara tayi tareda alkawarin zasu rinka zuwa akai akai, daga nan Mai martaba yace ta shiga cikin gida ta gaida matansa shi bari ya zanta da Daddy.
     Rai baiso ba ta shiga cikin gidan, sasa ɗaya ta shiga tayi zamanta. Cizan yatsa takeyi saboda batasan me za’a mashi ba.
     Shikuma Mai Martaba sakawa yayi wani Malami daga Gidan Zuma na Zaria yayi ma Daddy wasu addu’a tareda bashi magunguna.
   Basu suka bar Zaria ba sai bayan isha’i. Aikuwa Bilkisu tayi fam lokacin, batace mashi komai ba har sai sanda motar daya kawo su taga sun juya.
   Nan ta saka ya tube cikin tsakar gida daga shi sai boxers, anan ta kwashe duk maganin da aka bashi takai bola kafin tace su shiga.
        Haka ya kwashe kayansa dake kasa suka nufa falo, ita Mermer gida nata babu kowa. Kaza ta soya da chips tana ci sannan ta haɗa shayi mai uban kauri wanda yasha madara da milo.
    Tanaci tana jin Tafsir ɗin Mallam Kabiru Gombe, siɗe hannu takeyi ta gama cin kashin karshe sai gasu Daddy sun shiga.
   Yanayin sa duk a tube sai kajeran wando ya bata kunya amma saita basar kamar bata gansu ba. Kitchen taje ta ajiye kwano sannan ta koma daki.
     Shikuma Daddy suna shiga ɗaki Anty Bilkisu ta sakashi kneel down, nan ta zage shi tas babu abinda batace masa ba, kuma tace duk randa aka sake bashi wani abu mai sunar magani bai nuna mata ba saita saɓa mashi.
   Haka yayita bata hakuri ita kuma inda take shiga banan take fita ba, anan tayi banza dashi ta shiga bayi tayi wanka sannan ta saka wani figigin rigar barci yar yayee.
  Fridge ta buɗe ta dauko ruwan data saba bashi, saida ya shanye tukun saita ce ya mike tsaye kada ya kara. Hakuri ya cigaba da bata jikinsa yana rawa.
   Ita kuma tana tunanin dole ta koma wajen Tsanani saboda kada ta tsaya sanya sanya Mai Martaba ya shammace ta.

   *****
    Amaturahman itama yanzu tanada juna biyu, kazanta ya ninka nada ga kuma kwadayi.
   Kamar yanda ta saba Nawaz yana fita take saka kafa ta shiga gidan Maman Eemaad, ko wanka batayi balle kimsta kanta, uwa uba ayi wani maganar gyara gadon kwanciya ko kawar da kwanon breakfast, shifa da kansa yake cire Shargi dake kan gado idan zasu kwanta sannan ya kakkabe.
   Ita kuma anan gidan Maman Eemaad take aika almajirai su siyo mata su gyada, masara, awara da kuma rake.
   Haka zatayi taci tana surutu, ita kuma Maman Eemaad tana aikace aikace da ba’a rasa ba.
   Daga nan wajen 11am taje ta dauko su nama ko kifi wanda Nawaz ya siya tareda su kayan cefane ta jibge a gaban Maman Eemaad.
    Abin yana bala’in bama Maman Eemaad haushi amma babu yanda zatayi. Ita bataga dalilin wannan neman sunar ba, wai ace kowa bazai ci abincin da mijinsa ya siya ba sai an haɗa girki.
   Ita yanzu kawai tana tolerating Ama ne amma ta bala’in gunduran ta, sau ɗaya ta taɓa zuwa gidanta tunda take amma ita kam a nata take yini.
    Abin bayama Maman Eemaad daɗi wai ace duk sirrinta a idon Ama yake, yasa kwata-kwata bata sake mata fuska ba akan ta rinka shiga mata dakuna.
   Iyakacin ta falo sai dining area, ko kitchen Sai idan ta kama take barinta ta shiga ciki.
  Duk abinda Ama keyi a idon Nawaz, babu abinda bai ji ba kawai yana Kyaleta ne. Gashi kuma duk yan unguwa suna tsegumi akan abin.
    Kowa maganar yadda an kawo amarya mara kintsi sukeyi, wasu ma wanda sukayi bincike sun gano cewa dama haka halin Ama yake, ko Nawaz saida ta rinka sintiri gidansu kafin aka yarda da auren.
  Aiko abin yayi bala’in ɓata mashi rai, baiga dalilin dazata rinka ɗebo masa magana a gari babu gaira babu dalili.
   Wasu ma cewa sukayi wai tana shishigi gidansu Maman Eemaad ne saboda mijinta yanada kumban susa tanaso ta kashe aurenta ta koma chan, wasu kuma cewa sukayi a’a tana neman ma kanwarta auren Baban Eemaad.
    Gashi idan tana jin gari kuma Maman Eemaad batayi girki da ita ba, ranar soya kwai takeyi da shayi shi zasu ci. Idan Nawaz yayi korafi akan shayi bazai kaishi asuba ba.
   Hasala takeyi ta kirasa Dan kauye wanda kullum saiya girba abinci, takance bai lura da Larabawa da turawa ba yanda suke shan shayi ba tareda korafi ba.
  Baya tankata saidai idan yaje sallar Isha saiya biya dakalin Mai Indomie yaci yayi nat. Wata sa’in gidansu yake zuwa yaci.
   A kalla cikin sati yana zuwa gidansu wajen sau uku ko hudu, amma Gwaggo ta mance rabon dataga Ama yar albarka.
     sanda taje gidan, Nawaz ne ya ajiye ta da safe da niyar idan ya dawo zai ɗauke ta.
     Uwar dakan Gwaggo ta shiga ta naɗe kafa, Hassatu ne ta kawo mata koko da kosai. Koda ta gama ci bata kawar ba tana buga Candy Crush a sabon wayan data saka Nawaz ya siyan mata watau Infinix Hot.
   Gwaggo ta shiga zatayi sallar walha sai taga kwano da kofi a wajen, gashi kosan duk an ɓare bayan an bar totuwan ciki duk kyama.
    Da kanta ta fita dashi waje ta kai kitchen, kafin ta dawo Ama ta fito da chewing-gum ɗin Orbit tana ci Kas kas kas tana hura balan balan.
     “yan mata adon gari cingam ake cine haka?” Gwaggo tace
    Murmushi Ama tayi saita hura wani balan balan mai girman gaske saita fasashi kafin tace, “Wallahi Gwaggo Kinsan lalurar danake cike yana sani ciye ciye, bari ma rana ya fito Hassatu ta samo min masara gasarshe naci
    “uhmGwaggo ta iya cewa sabida abin yafi karfinta. Kawai kabbara sallah tayi tunda ta lura Ama ta koya rashin kunya.
     Hassatu tana kitchen tana jefa Dan wake saboda Ama tace shi takeso taci da rana kuma Gwaggo tace dole ayi, gashi Baba da Hassatu duk basu ci.
  Dole yanzu ta ɗaura masu nasu abincin daban, Ama ne ta shiga kitchen. Kare mashi kallo tayi saita yatsina fuska.
   “ungo Kije bakin bus stop ki siyo min masara na naira sittin sai kwakwan arba’in” Ama tace tareda mika ma Hassatu ɗari.
     Ko kallonta batayi ba ta cigaba da aikinta, saidai ranta yayi bala’in ɓaci kamar zai fashe.
  “Bansan wulakanci, Hassatu bada ke nake magana ba? Koko bakiji mai nace bane?”
    Harda taso ta kyale Ama amma wani zuciya ya raya mata cewa gwara ta taka mata birki, “Sarai na jiki zuwane bazani ba”
   Ashe a kunnen Gwaggo ta faɗa, ‘tas’ ta wanka mata mari. Sai tace, “Dama bakida kunya! Matar kawunki kike ma ɗibar albarka! To Kafin raina ya ɓaci dake gwara ki karɓa kudin, idan kin gama jefa ɗan waken saiki je koda birnin Sin ne ki siyo
    Ita kuma Ama Gwaggo zata bata hakuri saita jefa ma Hassatu kudin tayi tafiyanta. Murmushi kawai Gwaggo tayi ta mayar da abin kuruciya da kuma cikin dake jikinta.
   Tabbas ciki babu abinda baya saka mutum, kuma daga ciki har masifa. Kawai fatan Allah ya rabata Lafia dashi takeyi.
   Hawaye Hassatu takeyi, haka ta gama tareda sakawa a cooler, sannan ta yanka su albasa da tumatir da kuma dafaffen kwai.
   Hijab ɗinta Maroon wanda ke rataye akan kofa ta figa ta tafi bakin bus stop domin ta siya. Haka taje ta dawo batace ma kowa kala ba.
   Lokacin Ama tayi zaman dirshan tana cin abinci tareda latsa waya, WhatsApp ta shiga group din su jokes sai dariya takeyi.
  A gabanta Hassatu ta ajiye saita koma kitchen domin ta ɗaura nata abincin da kuma Baba, Ama bata cinye wanda ta zuba cikin plate ba.
   Turawa gefe tayi saita hau cin masara, lokacin da aka kira sallah saita mike tsaye taje tayi alwala.
  Koda ta dawo uwar daka ta koma ta kabbara sallah, bayan ta idar nanta kishingida ta soma barci. Hassatu ne tazo sallah itama taga falo kacha kacha. Babu yanda zatayi haka kwashe kafin Gwaggo ta hau sababi.
    Ama bata farka ba sai wajen la’asar, a lokacin Gwaggo ta shiga makwabta saboda yarinya karama yar shekara 2 ta faɗa rijiya amma an samu an cirota.
      Alwala Ama tayi sai tayi sallah, a lokacin zaman gidan ya isheta. Gashi kuma Remote ɗin falo yana hannun Hassatu.
     WhatsApp ta shiga ta cigaba da karanta ‘A dalilin Mene’ na Ummiejafar wanda aka tura na ranar sai kumaIna Zan Ganshi’ na Zarah Bukar.
    Wajen 4:30 pm tayita kiran Nawaz, bama kira bane flashing ta rinka zabga mashi kamar me. Tako bala’in iyawa saboda ko haske wayan baya nunawa saidai yaga Missed call.
   Babu shiri ya tattara komai ya bar wajen aiki, yau babu daman zuwan zaman banza kofar gidansu Mermer kamar yadda ya saba.
    Yana shiga ta maza ta zura Hijab wai su tafi, baiko kalle ta ba ya samu kujera ya zauna. Sannan yace ma Hassatu ta kawo mashi abinci.
   Tako sauke sanwan dare kenan na Tuwan Semolina da miyan kuɓewa danye. Yaci malmala biyu yasha ruwa, lokacin Gwaggo ta dawo.
    Sunyi gaisuwan mutunci sannan ta gode masa akan ziyarar da Ama ta kawo. Har take cewa ya rinka kawota akai akai.
  Shima yaso haka saboda zamanta a gidansu yafi zaman gidan Maman Eemaad, ita kam Hassatu ta ɗauki alwashi duk randa Amaturahman ta sake zuwa wai da sunar zata yini, toh daukan Jakarta zatayi itama ta tafi chan gidansu yini.... Wannan kenan!

   *****
  Nuwairah tana aiki a Gwaiba Investment wanda ke Abuja branch a Maitama, dayake Gwaiba sunada Conglomerates a ko’ina yasa duk garin da kake zaka samu wajen aiki.
      An bata CEO a wajen kuma yadda ta nuna gaskiya da adalci yasa kowa ke santa, da wajen karfe hudu take tashi taje domin ta ɗaura ma YaShehu abinci.
   Working days breakfast and dinner kawai yake ci a gida, kuma weekend yaci sau uku. Ko sau ɗaya bata taɓa wuce lokacin daya ce.
    Kamar yadda ya bukata bata tadashi daga barci, bata shiga ɗakin daya haneta ta shiga. Duk wani abu tana kokarin kiyayewa.
Kuma shima yana respecting ɗinta sosai, baya musguna mata kuma suna jin daɗin zaman su tare thou wani abu na zamanta kewan aure bai shiga tsakanin suba.
   Saidai kuma Peaches magensa tana firgita ta, kwata-kwata she is not a fan of maguna. Tsoron ta takeji sosai yasa idan tana zaune dole akwai zabori gefenta. Tana wuce arm length away zata zabga mata.
   Gashi magen tana bala’in san Nuwairah, duk inda taje saita bita. Koda YaShehu ya lura cewa basa shiri saiya ɗauke magen yakai ɗakinsa na kasa watau Private room ɗinsa.
    Ita kullum tunani kala kala takeyi akan meke cikin ɗakin dayake so ya shiga shi kadai.
    Tana dawowa daga aiki saita biya Jabi Lake Mall domin tayi shopping. Ta siya su groceries sosai ta cika boot saita nufa hanyar gidansu wanda ke Audu Ogbeh Street a Jabi ɗin.
   Har mai gadi ya buɗe mata gate saita tuna tanaso taje Saloon. Anan tayi reverse ta juya saboda wash and set za’ayi mata babu yawa.
    Wani Saloon tagani karami wajen Jabi garage saita tsaya wajen. ‘chiamaka Saloon’ aka rubuta a sama.
   Suna ganin Hajia da gwala gwalai suka rinka washe hakora, anan aka bata VIP seat dukda bambanci shi akwai dunlop sauran kuma farin kujeru ne.
   Anty Chiamaka ta ajiye dubu hamsin yan dubu dubu a drawer, wuf Nuwairah ta sace. Dama tun zamanta ta dauka Tama mance ta wani yi sata tana nan tana replying emails ɗinta har aka gama mata. 3500 sukace kudin gyaran gashi don sunga tanada kumban susa.
    Itama tasan baikai haka ba amma ta basu haka, kuma dama tanada wajen dubu dari a Jakarta kuma ba cikin wallet suke ba yasa bata tuna kudin Anty Amaka ba.
   Ta fita Anty Amaka sai murna takeyi, taje drawer zata ajiye kudi sai kudi yace daukeni tunda ke kika ajiye ni.
   Lokacin Nuwairah ta danna key ɗin mota tun daga nesa tajishi ya buɗe, harta murɗa murfin mota zata shiga sai Amaka taci kwallarta ta biya.
   “Where you wan carry my money go?” taji muryan Amaka. ‘Rasgabanta yayi mummunar faɗuwa. idonta ya raina fata ya cika da ruwa.
    Nan ta soma ɓarin leɓe, kuma tabbas ba kazafi akayi mata ba. Kudin Anty Amaka yana cikin Jakarta.
  “What are you talking about?” tace Kamar bata gane ba.
   “woss!  If i give you back hand u go remember say my money dey with you, arm robber dressed like HajiaAmaka tace tareda ɗaga hannu kamar zata mare Nuwairah.
    Sukam mutane nan sukayi cha aka taru, wasu kawai basu san kan zance ba suka zo suka fara dukan Nuwairah, ta baki ta hanci.
    Sai kuma wasu suka kare mata suna tambaya aji kan zance, gardama ya kacame tsakanin masu kare mata da masu son su duketa.
    Kuka takeyi sosai saboda idan akaga kudin cikin Jakarta gasu yan warri ne wajen suka taru, ba Abuja ba koma ina ne zasu iya saka mata taya su konata kurmus.
    Shikuma magensa babu Lafia, ya biya wajen Vertinary Doctor ta wajen Jabi Garage zai siyan ma Peaches magani.
   Sai yaga ana hayaniya mutane sun taru makil, ita kam Anty Amaka sai shela take an mata sata anaso a noke, tuni ta fara so ta mayar da abin religious crisis. Gashi ta fasa kwalbar giya tanaso ta luma ma Nuwairah an hanata.
    “Make una allow me teach dis arm robber lesson, today i must comot dat hand where dey steal anyhow, Shey dey no give you home training”
   “ u sef madam Amaka how u take know say na she thief am” wani yace
   “who go steal am? Na me go thief my money, i count 50 thousand flat for her front oo, Abeg make una allow me show her say i be correct area babe”
   “Okay Anty Amaka calm down make  we ask her”
  “Warri no dey carry last, my body don already hot... Make una allow me end her parade sharp sharp” ta faɗa tana lankwasa baki.
     Tsaki yayi saiya fito daga shagon Doctor ɗin ya wuce wajen hayaniyar, motar Nuwairah ya fara hanga, haushi sosai yaji wai harda ita a masu kallon fada.
  Yana isa wajen ya daka masu tsawa yace suyi mashi shiru Kokuma ya ingiza keyarsu zuwa guard room.
   Kawai saiya hanga Nuwairah tana kuka, da hanzari ya karasa inda take.
    “Meya faru?” bata amsa ba illa barkewa da kuma sabon kuka.
   “Oga na she thief my money” Amaka tace.
  Mamaki yayi sosai, sai Amaka ta labarta mashi komai daya faru harda tsadan datayi amma bata damu ba saboda tayi mata sata.
   Zagin Amaka yayi sosai saboda batasan wa ta yima kazafi ba, YGG ce zata daukar mata wani dubu hamsin.
   Kowa ma yana jin abin ya karyata Amaka, Shehu ya amsa account number ɗinta yayi mata transfer na 70k.
    Tana ganin alert tayita godiya, ta bala’in jin dadin 20k data samu kari, dama haya zata biya Kokuma ta koma chan kauyen su na Warri da zama.
     Kiran wani Boy ɗinsa na ofis yayi saiya bar key din motarsa wajen Vertinary Doctor, sai suka shiga motar Nuwairah which da kansa ya tuka.
    Idan akwai abinda yafi kunya yau taji shi, ballema yau YaShehu yaga asalin halinta. Zulumi takeyi saboda har tana tunanin ta fara samun nasara cikin zuciyar sa.
   Amma yanzu komai ya rushe, babu wanda zai so ya zauna da ɓarawo. Tana ganin kila ma sakinta zaiyi.
    Bai hanata kuka ba dukda bayasan hayaniya, amma ko shine akayi masa cin mutunci haka ranshi zai ɓaci.
     Gashi duk yanda yaso yayi denying yasan cewa akwai burbushin santa a cikin ransa.... Wannan kenan!

****
     Nawwarah a hankali ta gane Deenie gogaggen ɗan duniya ne. Da farko idan lokacin sallah yayi saiya wuce ɗaki kamar zaiyi acan amma kwanciyar sa yakeyi ya hau Instagram ko YouTube.
   Idan ta shigo ɗakin saiya maza yacekinga harna idar na kwanta inata hutawa koh
   Da farko bata saka wani abu cikin ranta ba, sai daga baya ta lura karya yakeyi. Musamman idan bawai tace ayi sallah ba bai taɓa furtawa da bakinsa akan suyi.
   Kuma idan tace yaje Masjid ya rinka sanya kenan da nuku nuku har a idar Kokuma yayi zamansa a bakin gate wajen dakalin mai gadi.
   Sai a lokacin ta lura da cewa sanda yake zuwa taɗi wajenta kafin suyi aure zance daya jiɓanci sallah bai taɓa haɗasu ba.
    Bata taɓa kawo abin cikin ranta ba tunda mahaifinsa malami ne, gashi babban wansu har tafsir yanayi da watan Ramadan.
    Dannewa tayi a ranta ta bashi uzuri tunda dama mutum tara yake bai kai goma ba. Ashe banan gizo ke saka ba, Kullum idan ya dawo zai rambaɗa turare kuma nan take zai wuce bayi yayi wanka da ruwan sanyi saboda yayi lowering blood temperature dinsa tunda giya ta saka komai yayi high, sai kuma kada taji tsamin giya.
      Haka zata jirashi saboda yaje suci abinci, dama breakfast and dinner Kawai suke ci tare kasancewar tana zuwa aiki kuma shima haka.
     Wajen dinner nan zata dage tayi masa varieties balle tayi Food and nutrition a secondary school so Kaudi.com, koda wasa mai aiki bata tayata girki. Saidai tayi wanke wanke bayan ta gama. Ta riga tasan how to win a Man’s heart is through his stomach.
     Idan sukaje kan dining kamar abin arziki zai zauna, yana buɗe coolers yaga any form of Carbohydrates zai fasa cin abincin. Fruits kawai zai sha ko salad da kuma pepper soup. Sannan baya mance shan Black coffee.
   Idan tayi magana zaice bashida appetite yasa yakeso yayi boosting nashi, chan anjima cikin dare zai tashi yaci.
     Shikuma duk yana preventing wani irritation da cikin sa zai samu kafin yaci abinda bai dace ba ya narka amai a gabanta ta ɗago halinsa.
   Shi ya riga ya yarda barasa itace kadai zai iya taimaka masa wajen cigaban rayuwa, baya tunani da kyau idan bai kyankyama ba. Yasa a rana saiya sha wajen kwalabe ashirin, idan kuma yana jin garin zai sha wajen hamsin.
    Gashi yanzu Nawwarah tanada shigan ciki na wata biyu, baya bata wuya yasa babu wanda ya sani sai ita kadai.
    Tanaso tayi masa surprise ne ta faɗa masa, Mai aiki ta gyaran gidan ta sake mopping ko’ina. Daga nan sai Nawwarah da kanta ta saka turaren wuta a duka burners na kowane kusurwa na gidan.
    Tunda ta lura yana san Salad sai tayi masa mai uban yawa wanda tayi decorating ɗinsa in an oval form da Heinz salad cream tareda baked beans and eggs Sai kuma hanta.
   Sai kuma grilled cat fish a gefe, ita kuma Lingerie ta saka mai over all. Fuskanta shake da smoky eyes sai ta saka Hills tana jiransa a 3 seater, ita duk zumudi take ta sanar dashi cewa zasu haifa yaro rabi da rabi na jikinsu.
   Wani zuciya yace mata waya sani ko twins ne ko triplet, nan wani farin ciki ya sake lulluɓe ta.
   Yau wani wansa yayi mashi zuwan bazata a ofis yasa bai samu daman shan Barasa ba da kyau, abin yayi bala’in bashi haushi saboda yau har Asr da Magrib cikin jam’i yayi.
   Haka ya dawo gida kafin yaje ya daɗe Nawwarah ta lura, shi abinda yasa yake wani ɓoye mata baifi irin sanda yake mata kafin ta sani ta gujeshi. Yasan dai ta san baya sallah saboda ta daina masa magana akai.
   Shima yanzu ya samu sauki, dama MTV base sunfi sako sabbin waka karfe 6-7 kuma yana kallonsa hankali kwance.
     Shifa baya ganin aibun abinda yakeyi, saboda baya bin mata, baya sata, baya shan kwaya, baya cha-cha kuma ko karan sigari baya zuka. Kawai Barasa ne sai kuma rashin sallah, haba ai yayi kokari!
    Wani karamin zuciya ne ya tuna masa cewa ko Azumi saiya gadama yakeyi, mostly azumin dayake yi kamar na Yahudawa.
    Salin alin zai dauka ana sallar azahar zai wuce restaurant ya girba abinci yayi gyatsa. Kawai yanzu abinda zaice ma Nawwarah anyi diagnosing ɗinsa da Chronic Ulcer yasa bazai iya azumi ba idan ramadan ya gabato.
  Daga nan xaici 3 square meal Watau breakfast, lunch and dinner hankali kwance. Murmushi sosai yayi saboda idea din yakai mashi karo, ‘Kai Deenie bakada dama’ yace yana kanne ido tareda zaro harshe ya lashe bakinsa.
     Koda ya shiga falo yayi arba da Nawwarah, wani farin ciki ya mamaye masa zuciya. Janyota jikinsa yayi yana ajiyar zuciya, ‘Ko babu giya idan kanada kyakyawan mace ai ka more’
     “Baby sannu da zuwa, yau inada surprise maka”
  “Kafin nan ki kawo min abinci naci”
  “Ga salad ɗinka kan dining”
   “A’a abinci nakeso” shi abinda yasa yake neman abinci baifi yau bai sha giya ba baiga dalilin kwanar yunwa ba.
    Da murna ta jashi har Dining ta zuba mashi purple fried rice data girka. Anan yaci sosai kuma taji dadi.
    Anan ta koma kan cinyar sa tana masa magana kasa kasa, “Baby mun kusan samun yaran mu na kanmu”
    Nan take ya kware ya tuntsire abinda ke cikin bakinsa, zare ido yayi yana kokarin yayi magana amma ya kasa.
  Saida ya kurba ruwa sannan yace, “Bangane ba”
  Kyas tayi da idonta sannan tace, “Ciki gareni, 2 months”
   “Why” yace a hasalce. Sai kuma ya saisaita kansa. “Sannu” ya sake maimaita wa.
  Ikon Allah ta tsaya kallo, “Meke damunka halan? Jibe yanda kake zuba zance out of context, meya kawo ‘why’ Kokuma ‘sannu’ cikin maganar da mukeyi.
     Mikewa tsaye yayi, bazai iya absorbing wannan bad news ɗin ba shi kadai babu abokan rayuwarsa watau Barasa, gwara yaje club chan inda zaiji sanyi.
    “Bari naje ofis na dawo, nayi mantuwa a chan. Idanna daɗe karki damu kawai kiyi kwanciyar ki”
   “Ka bari gobe mana, haba ai dare yayi kuma wannan shiga hakki ne”
Baiko kalle taba ya ɗauki key ɗin motarsa dake kan centre table ya wuce abinsa, anan ta soma gumi tareda fashewa da kuka.
  Ko bai faɗa ba tasan cewa cikin ne bayaso yasa ya wani daburce, amma ko zai mutu ne saidai fa yayi tunda ciki da ubansa kuma zama daram dam dam.
      Shikuma Deenie Naf Club yaje tunda yafi kusa dasu, anan yaje wajen Bar ya hakince, bottle after bottle yayita sha. Su Gulder, star, Sminoff, Guinness etc crate crate.
      Sannan ya siyan ma kowa a cikin wajen kwalba biyu biyu wai a taya shi bak’in ciki matarsa tanada cikin wata biyu, wasu na mashi jaje wasu kuma nace masa yara rahama ne baisan alherin da zasu taho mashi dashi ba.
   Nan yace koma menene bayaso su rike abinsu, wani daga cikin mashaya shima yayi ma Deenie jaje daga nan yace ai nashi mai sauki ne, jiya budurwasa tace masa tanada ciki.
   Nan take ya nakada mata duka wanda cikin ya zube a wajen, saboda take cikin yake tayi. Shima Deenie yayi tunanin haka amma saiya tuna Nawwarah Yar Gidan Gwaiba ce.
   Ita kuma taci kuka ta koshi, bata koma daki ba tana jiran Deenie, wajen tsakar dare taji karar gate. Tana kallon agogo taga 2:45am.
   Wani sabon hawaye ya gangaro mata, dayake ta kashe wutan falo yasa baisan da ita ba.
    Yana shiga ciki sai labule ya kama mashi jiki, nan ya zage damtse ya rinka dambe dashi. Ita kuma abin mamaki take gani, kallonsa takeyi cikin silhouette.
    Tashi tayi taje ta kunna wuta, anan ta maida hankalinta kan fuskanshi babu wasa a tareda ita. Tana kallon shi tana kallon labule.
  Shine ya soma murmushi yana magana cikin maye, “wallahi labulen ya raina min wayo ne, dan wulakanci nazo wucewa shine ya wani shafani”
   Dakewa tayi saboda bataga abin dariya ba, karasa tayi inda yake tsaye saboda duk ya cukwikwiya labule a hannunsa. Tana kokarin tayashi cirewa ashe turaren jikinta yana takura mashi.
   Nan ya soma amai babu tsayawa. “Innalillahi wa inna ilayhi rajiun” tace a fili. Shikenan abinda take gudu ya faru da ita, Her worst nightmare has finally come to past saboda babu tantama Deenie mashayin giya ne.... Wannan kenan!

*****
   Hunaisa ta gama idda, yanzu ya tabbatu zata iya auren wani. Mudassir ya sake kawo sabon sadaki na aurensu.
   Family murna akeyi sosai musamman Mommy, ita kam Hunaisa kamar zata kashe kanta dan bakin ciki.
   Kwata-kwata bata san YaMudassir yanzu, gashi kuma tana fama da PTSD watau Post-Traumatic Stress Disorder.
   Har Yanzu bata cewa kala banda bin mutane da ido, wasu sunce kila idan akayi auren zata murmure tunda masoyinta Mudassir zata aura.
    Yanda kuma take kuka kullum ansha wahalar data sha gidan Hamza yasa abin ke sata kuka idan ta tuna.
     Tun tana ɗirga kwanaki ko Hamza zai nemeta amma shiru, yau 109 days rabonta da ganinsa.
    Gashi an saka bakinta cikin wannan mako, ‘Dan Allah Hamza come back to me please, Wallahi bazan iya zama ba tareda kaiba’ ta faɗa cikin ranta saita fashe da kuka.
     Shikuma Hamza kamar yadda yayi alkawari fuska biyu yake masu Oga Daddy da Last Don. Basu san cewa yasan komai ba, ya sake jikinsa sosai kamar da kuma sun ji daɗin haka.
    A yaune zasuyi gagarumin satan da suketa shiri, kowa ya saka camouflage na sojoji. Sannan sun saka Mask ga kuma AK47 a hannu su.
       Hamza ya riga yayi hacking security ɗin Kaduna state, musamman Na Gwaiba Group wanda ke Maraban Jos.
  Anan ne akace Baffa yanada wani Safe ɗin kudi, kuma laptop ɗinsa yana ciki wanda tanan zaka iya transfer ɗin billions ɗinsa daga Swiss.
     Suna cikin armoured tanker kamar ba ɓarayi ba. Hamza yayi hacking alarm ɗin wajen suke controlling ɗin komai.
     “Fito mana muje ayi komai dakai” Last Don yace ma Hamza.
   “Banni wajen nan, bazan iya jigilar computers ba. Kawai ka saka wannan flash ɗin cikin system ɗinsa na iya accessing daga nan”
    “Last Don bar mata mazan dinnan muje mu fito” Oga Daddy yace yana dariya saboda wannan karon yace dashi za’a.
   Sun harbe na harbewa a cikin security kuma sun kulle na kullewa. Sauran Boys suna Downstairs suna wani zare ido sai Oga Daddy da last Don suka hau elevator zuwa ofis ɗin Baffa.
     Wani karfe suka manna a bango sai sukayi baya, abin baiyi 5 secs ba saiya tashi da kofar.
    Nan suka sha hannun suka shige, sun sha wahala kafin suka gane inda Laptop ɗin yake.
     Kamar yanda Hamza ya bukata haka suka saka flash cikin sai Hamza ya soma kokarin hacking.
    Da kyar ya gano password saboda ya kusan 30mins ana abu ɗaya.
     Gashi password ɗin da uban tsawo wajen 25 Characters.
     Ya shiga ya fara transfer ɗin kudin, suma su Last Don suna ganin abinda yakeyi. Haba nan suka soma rawar Shakiti Bobo.
     Suna yi suna makale kafada ɗaya suna zaro harshe, sai kawai Hamza yaji siren ɗin yan sanda.
    Nan ya ruga da gudu ya fantsama daji, gashi garin gudu Laptop ya faɗi ya fashe. Su Kuma suna chan suna rawa sai sukaga abu ya makale a 73%.
    “This is the kaduna State police Operation Yaki, you are surrounded.. I repeat you are surrounded and out numbered. Surrender yourself and your weapons”
     Abinda sukaji kenan ta speaker ana faɗi, nan ido ya raina fata. Shikam Hamza sai gurza gudu yake cikin daji babu kakkautawa kafin a chapke shi.
     Oga Daddy kam yace he is not going down without a fight, babu wanda zai nuna masa bariki saboda mamansa da babansa a gidan Magajiya watau club ɗin da suka haɗu sukayi aure. No retreat no surrender kake gani.
     Aiko nan ya buɗe ma sojoji da yan sanda wuta, suma suka mayar da martani. ‘Barin bindiga akayi sosai kuma an kashe yaran Oga Daddy da dama.
  Da last Don yaga babu kanta yayi surrender, Oga Daddy yana masa magana amma bai kulashi.
   Dole shima ya dauki na damu ya ajiye bindiga a kasa, “Nayi surrender please karku kasheni” yace yana kuka.
     Nan Police sukazo da gudu suka dauka bindigar dake gefen su sannan suka kwada masu bindiga a kai, sai suka saka masu handcuffs tareda ingiza keyarsu zuwa Jail....... Wannan kenan!











YGG






DIMPLΣS ce

'Yan Gidan Gwaiba (Completed) Where stories live. Discover now