Twenty-two

5K 257 8
                                    


  Sharhin shafin daya gabata daga Fatima aka Ummie Rilwan masoyiyar YGG

Hhhh..
Hunaisa kenan..
Soyayyan shi kam anyi angama Tunda kinada tausayi..
Kafin Ku koma 9ja komai ya kankama😂
Hege Hamza talented Kullun experience daɗa qaruwa yakeyi..
Anji tsaro kam! Amma Kada ka boye mata komai a kanka..
Daga baya zata iya ganin lefinka koda tafara sonka ne 👌


Kai!  Su lubie qanshin gari Har an shinshino TK baya Haihuwa..
Ohni fadima! 🤔
Ynz qanwar shedan zata chanja mata alqibla🙆🏾


Wayyo mermerh lbrn aikinki Sai tabarbarewa yake..
Doc kam Allah ya shirya..
Giya kam ai batayi ba..
Nuwairah kidaina kuka Daga Allah ya dauke maki wahala da Ciyon zucia a dawo maki gda a buge..
Ai nay maki murna Ynz kam Sai kuyi barambaram🙅🏿

Ga shi Ga Nawwarah..
Daidai qurji Daidai ruwansa 👌

****

   Jikin Nuwairah yayi likis tareda sanyi kamar la’asar, zuciyarta wani ɗaci ɗaci yake mata tareda bak’in kirin kamar gawayi, gashi yana mata zafi kamar garwashin wuta.
    Ji take kamar an soketa da mashi da aka ciro daga shagon mak’era yanzu yanzu. Haka ta ɗauki karar kafanta ta tafi.
     Koda Mallam Musa ya ganta yasan akwai matsala amma kuma yayi shiru baisan yayi mata katsalandan.
    Saka shades tayi a cikin mota tareda jingina kanta ta baya, tunanin mafita takeyi sai ta yanke shawara akan taje ta roke Nawwarah alfarma akan ta bar mata Deenie.
    Tasan halin Nawwarah soyayya baya gabanta, zuciyanta irin cold dinnan ne kamar kankarar da aka ciro daga North pole. Yanzu ta riga tasa kanta akan ta burge Baffa a Gwaiba Investment yasa bazata bari wani ɗa namiji ya ɓata mata lokaci ba.
     Tana tunanin haka sannu a hankali harta kai Gwaiba Manor, Mallam Musa ta bakin kofar shiga falo ya ajiye ta saiya wuce Parking lot a ajiye motar daga nan ya hau babur ɗinsa ya tafi gida.
     Kai tsaye downstairs inda ɗakin Nawwarah take ta shiga, Nawwarah tana office bata dawo ba haka ta jirata.
     Lokacin sallah yayi ta tashi ta shiga bayin Nawwarah tayi alwala tareda amfani da kayan sallarta. Tayi addu’a sosai tareda dogon lazimi.
     Tana addu’a tana sheshekar kuka saboda ita kadai tasan Meke mata ciwo. Bayan nan ta dauki karamin Quran a gefe ta karanta suratul Khaf. Daga nan ta soma jin daidai fiye da yanda ta dawo.
      Naɗe kayan sallar tayi sai tayi daidai akan gadon Nawwarah tana tunani, lokaci baya wuyan gudu har la’asar yayi.
      Anan ta tashi tayi, dayake idan ranta ya ɓaci bata iya cin abinci yasa bata nema ba.
     Shikuma Deenie yana isa gida ko takalmi bai cire ba yabi lafiyan gado, babu ma maganar sallah tunda kona safe baiyi ba balle ayi tunanin zaiyi sallar juma’a.
   Dama AC a kunne yake nan yaji dadin barcinsa har wajen 3:30pm la’asar. Bawai sallah ya tadashi ba a’a gaida iyayensa zaije kamar yadda ya kasance dole idan kana Kaduna.
      Tashi yayi ya shiga bathtub ya sakan ma kansa ruwan dumi, anan ya tsaya na wajen 15mins, maganar da Nuwairah takeyi yake dawo masa.
     Abin yana masa gizo, wai shi take kira baby. Shidai yasan yayi bushasha a gidan giya jiya amma baiyi buguwan da zaice baiji me take fadi dazu ba.
    Haushin kansa yayi sosai daya bari tayi deceiving ɗinsa, shi yanzu bazai iya tantance wani lokaci take pretending kamar Nawwarah ba, sam bai lura yanzu ta daina saka kwabɗa kwabɗan tabarau ba balle wani karfe a bakinta.
     He doesn’t like her enough to care, haushin kansa yayi kuma he felt so stupid. Ya akayi wanna kuchaka tayi deceiving ɗinsa.
    Abinda yake kara bashi haushi yanzu baifi yadda ya tafi bai tara mata gajiya ba, gaskiya wannan shi ne babban kuskuren daya tabka. Aida ya mata tsinannan duka na kwanciyar asibiti gobe bazata sake pranking wani ba.
    Daukar wayansa yayi yama Nawwarah Text, “Nagode sosai da abinda kika min, kinsa ina sake ma sis dinki fuska gashi yanzu har tana zuwa wajena a matsayin ki
     Daga nan saiya tura mata, ita kuma Pinky tana office tana duba wasu takardu, Boss ɗinta sun yaba da presentation ɗin Nuwairah ɗazu yasa sukace itama zatayi next week kuma sunaso kada ta basu kunya.
     Ita irin wannan unnecessary competition dinne bataso, ko bata faɗa ba tasan cewa bazata taɓa fin Nuwairah a komai ba. Ko bata faɗa ba Nuwairah ta kece mata wajen kyau da ilimi. Ita cuwa cuwa ne na make-up masu tsada da kuma gogewa.
Deep down tana burin ta zama kamar Nuwairah (Ikon Allah, ni kuma DIMPLΣS nace kana so ka zama wani shi kuma kai yake so ya zama. Mu rinka gode ma Allah)
Duk da presentation ɗin ba’a saka ranar yinsa ba amma gwara ta shirya, ko bata iya ba zataje ta rinka zabga turanci ko French ne ma zata haɗa dasu Dutch duk domin asha tayi wani abin arziki.
     Ta dawo daga masallaci a inda tayi sallah la’asar, tana cin Mentos tan duba papers sai taga sako ya shiga wayanta.
    Tana ganin sunan Deenie kafin ta karanta ta soma murmushi, amma kuma abinda ke ciki ya daure mata kai.
    Tasan cewa Nuwairah is desperate amma batasan cewa harda satan kamanninta ba, wannan ai identity theft ne kuma its punishable by law. Amma da kanta zata hukunta ta.
     Tattara takardunta tayi ta wuce waje, tana tafe ranta yana mata wani iri. Da ace dane da bata san Deenie zatayi encouraging ɗinsa akan ya cigaba da yaudaran Nuwairah amma ba yanzu ba.
    Deenie kadai ne ɗa namiji data keso kuma take buri yazama angonta kuma uban yaranta. Dole tayi mata iyaka dashi kafin tayi nisa.
    Ranta a jagule ta tafi motarta, tana sharara gudu kamar zata tashi sama amma tana ganin baya mata sauri balle Maraban Jos da wajen Kaduna.
    Dama a 120 take gudu tuni takai 180,aiko bata wuce NDC Anguwar kaji ba ta kusan ture wani mai garuwa da amalenkensa zai tsallaka titi.
    Harda bazata tsaya ba sai kawai ta fasa, fito da bandir ɗin 200 tayi watau 20k ta watsa ta Window sannan ta wuce abinta bata ko kalleshi ba.
    Cikin ikon Allah bata samu daman kashe kowa ba harta isa gida, batako rufe kofan mota ba a ta fice.
      Upstairs ta wuce ɗakin Nuwairah amma bata ganta ba, cizan yatsa tayi saboda ba haka taso ba.
    Tana murɗa kofan ɗakinta sai taga Nuwairah zaune akan gado tana kallon agogon bango. Haba da sauri ta shiga ta haska mata mari sannan ta fizgo gashin kanta ta rike da karfi.
      Ita kuma Nuwairah mamakin yanda har yanzu Nawwarah bata dawo ba takeyi, gashi har kusan hudu da rabi. Kawai sai taji an wanke ta da mari sannan an murɗa mata gashi.
      “kome zakiyi min Nawwarah bazan ji haushi ba, nasan cewa na cancanta a mareni ne
   “Mts” Nawwarah taja tsaki saita tureta. Sannan ta soma magana sama sama.
    “Barina gaya maki wani abu, fita a harkan Deenie saboda ba sanki yakeyi ba. Koma me kike tunanin ya shiga tsakanin ku was scripted by me saboda ninace yayi leading ɗinki
      “eh naji, kuma na yafe maki but yanzu ni sanshi nakeyi kuma inaso ki taimaka min akan na sameshi
   “Halan bakaji mai na faɗa bane? Nace maki acting yakeyi wajen ki, bakinsan wasa bane halan???... Koda yau ba 1st April bane amma April fool yayi maki, kuma kinsan ko makaho bazai kalle ni ya kyale ba, oya fice min a daki ko kice dan iskan duka”
    “Nawwarah a duniya meye na taɓa maki da kika tsane ni haka?”
   “Nidai nace ki fita koh! Unless kinaso na tara maki gajiya
     “ki amsa ni, Wat did i ever do to you dayasa kikayi resenting ɗina haka? Bazan iya tuna abinda nayi maki ba amma you’ve made it your mission ki shiga tsakani na da kwanciyar hankali. Koda yaushe kina kokarin ki musguna min
     Cire takalmi Nawwarah keyi sanda Nuwairah ke magana amma saita lura cewa bazata fita ba. Zuwa tayi taci kwallarta ta soma fincikarta.
    Ita kuma Nuwairah saita rinka tirjewa, haka suka rinka kokawa, anan suka shake juna tamau idanunsu ya firfito sosai sai nishi sukeyi saboda sun damka juna yanda ya dace. Suna haka har sanda Nuwairah ta fizge kanta daga rik’on.
    Kuka Nuwairah keyi sosai saboda tashin hankali, anan ta soma magana cikin kukaKiyi min rai dan Allah, bazan iya rayuwa ba tareda Deenie ba”
  Sai Nawwarah tayi dariyar mugunta mai sautiGaskiya you’re delusional! Kina tunanin koda bana san Deenie zan bari ya soki ne balle he is my life gaba ɗaya yanzu. Dole a baki dose of reality saboda kina bukatar shi”
     Ita kuma Nuwairah murmushi tayi kaɗan tareda lashe bakinta daya bushe kamar busarshen fura, Saboda yanzu na biyu da aka kirata ‘Delusional’ kenan. Amma su suka sani, ita tanaji cikin ranta Deenie shine soulmate ɗinta. Kuma saita mallake shi ta kowane hanya. Ita yanzu tayi nisa a duniyar soyayyar sa kuma batajin kira. Gyara tsayuwan ta tayi ta soma magana fuskanta babu wasa a ciki.
     “Gaskiya Nawwarah kiyi hakuri, ni yar uwanki ne. Yan biyu muke, kaman mu ɗaya  yasa zaki hakura ki barmin shi. Amfanin yan uwantaka kenan
    Yanka mata wani wawan mari Nawwarah tayi na ganin taurari, cikin masifa ta nuna mata ɗan yatsa, “Karki kuskura ki kara faɗin haka, any resemblance to you is what I hate most about myself. Kuma daga yau this means war nida ke, no retreat no surrender tsakani na dake! Wallahi tallahi sai kinyi dana sanin fitowa a gidan gwaiba. Mutuwa zai zame maki abu mafi sauki saboda zaki gwammace ki mutu da sani na a duniyaitama daga nan ta fashe da kuka.
    Ashe Momee tayi kusan 3 mins tsaye a wajen baki a sake tana kallon su, dama tazo wucewa ne taji hayaniya kuma dayake kofa a buɗe yasa basu ji zuwanta ba.
     “Halan akanku aka fara haihuwar Yan biyu?” sukaji muryan Momee.
    “Daku nakeyi? Halan nice mace ta farko data fara haihuwar Yan biyu. Kun mance nima twins ce halan? Amma ban taɓa yin haka da sister ɗina ba. Wai ace ɗan uwanka kake firta ma kalamai masu zafi haka. Haba niko makiyi na bazan furta masa haka ba!” sai Momee ta fashe da kuka itama.
     “Dan Allah Momee kiyi hakuri wallahi bazamu sake ba”Nuwairah tace tana matsawa dab da Momee. Hannu Momee ta ɗaga mata alamar ta tsaya a wajen.
    “Bazan Hakura ba, nace nak’i nayi hakuri. Wallahi kin bani mamaki. Inasha you’re the reasonable one a cikin ku amma shi ne kika bani kunya
     “Dan Allah Momee kiyi hakuri ba laifin Nawwarah bane, idan zakiyi faɗa ni zakiyi mawa... Amma kada kiyi mata faɗa Please”
     “Ki fita a idona Nuwairah, baki isa ki shigan min faɗa ba. Idan Momee tana min faɗa babu ruwankiNawwarah tace a hasalce.
    “Wato bazaku bari ba ko! Ai bani na fara haihuwa ba. Bari kuji abinda zanyi, zan cika bathtub da ruwa ne sai na nitsar daku saikun mutu shikenan idan hukuma sunzo sai su kamani. Kuma I’m really disappointed”
     Daga nan ta fita daga ɗakin tareda buga kofa da karfin gaske wanda saika runste ido saboda kara. Itama Nuwairah ta kwashe handbag ɗinta tana jan majina ta fita.
    Nawwarah kuwa zaman dirshan tayi a wajen ta soma kuka, watau kowa yana tunanin cewa Nuwairah tafi hankali. Toh ko akan maganar nan bazata taɓa barin mata Deenie ba.
     Bayan 2 weeks.....

  Babu abinda ya kara shiga tsakanin twins, ita Nuwairah idan taga Nawwarah kamar yadda ta saba cewa ‘Hi sis’ ko ‘Hello twinnybata fasa cewa ba.
    Kuma as expected Nawwarah bata amsawa, ita kuma Momee ta daina sake masu fuska gaba ɗaya. Daga gaisuwa sai gaisuwa.
    Ko wacce a cikinsu taje tasha kuka ma ishi amma Momee ko gizau. Idan ta gaji saita tafi Gym tayi exercise, ko ta tafi Garden tayi zamanta.
    Nawwarah abin yafi bak'anta mata rai saboda akan ‘worthless gal’ kamar yadda take kiran sis ɗinta Momee bata sake mata fuska.
   Shikuma Baffa bayan presentation ya wuce Italy a private jet ɗinsa ko gida baije ba yasa baima san da faɗan ba.
     Momee Allah Allah takeyi ya dawo saboda yayi maganin su yadda ya dace, ko zanesu yayi bazata hana ba.
    Basu kadai bane yaranta balle su saka mata hawan jini. Bata san abinda ya haɗasu faɗa ba amma bari Baffa ya dawo kuma ya ɗauki tsartsauran mataki akansu.
     Shikuma Deenie ya barma Dr Amrah komai akan Nuwairah, yanzu ita take ɗaukan sessions ɗinta.
     Kawai dai rashin ganin Deenie ne amma Dr Amrah tafi kwarewa sosai kuma taji ɗadin session da ita. Matar yar kimanin shekara 37 is very professional tasan makaman aikinta.
   Tanada PhD a psychology kuma tasan tambayoyin daya kamata tayi ba kamar Deenie ba wanda ke cewaMeyasa take satagatsal babu sakayawa.
   
    Ita kuma Asma’ul Husna datayi ma TK maganar ya kamata suje asibiti, ranshi ya ɓaci sosai saboda ya riga ya cire rai akan samun haihuwa.
    Anan yayi mata tas kuma yace kada ta sake tada mashi da maganar bayaso, shi saida ya gaya ma Iyayenta kuma suka aminta da hakan kafin akayi auren.
   Ana ta soma kuka ta kira Lubie a waya, tayima ma Lubie tas saboda itace ta kawo mata shawarar.
    Lubie batace komai ba saida ta bari tagama masifa tas sannan tace ta share hawayen ta, ai dama tasan za’ayi haka.
     Dole yaja mata aji, yanzu ta bari bayan kwana biyu saita sake tada mashi zancen.
     Aikuwa haka akayi, bayan kwana biyu wajen dare zasu kwanta saita soma kuka tana sheshekar. Daya tambayeta saita ce masa akwai wani sabon asibiti a Barnawa wanda mutane ke zuwa kuma cikin Ikon Allah ana dacewa.
     Anan tace masa bata damuba aje da Hajja Zee su duka aga asalin matsalar. Shi yace mata ta daina kuka bari yayi shawara da Hajja.
     Koda yayima Hajja magana tace a sauka Lafia, shekararta arba’in kuma ta hakura da yara.
    A haka suka tafi asibiti inda akace wai yanada Varicoceles kuma idan Husna tanaso za’a yi mata Intrauterine Insemination inda za’a dauko sperm daga jikinsa ayi mata inserting ɗinshi.
   Kokuma gabadaya za’a ɗauko kwai daga jikinta da kuma TK sai ayi amfani da machine a raineshi.
    Shidai TK bai gamsu da bokan bature ɗinnan ba sai yace masu zasu dawo.
  
Barakallahu....
      Ama tanajin abinda Gwaggo tace akan auren Nawaz tayita murna. Koba komai zata kece ma yan unguwansu tsara zatayi fresh zata shiga gari.
   Shikam Nawaz kamar an aika mashi da sakon mutuwa, ya tsane wannan haɗin da za’ayi mashi. Saidai kuma yasan idan bai yarda ba zai gamu da fushin Gwaggo kuma abinda bayaso kenan tunda iyaye ba abin wasa bane.
    Gwaggo kam sai shige da fice takeyi za’a kawo mata surikar arziki, a ranar da za’a gaisuwan Ama. Saida ta saka Baba yasa kayan dayaci  babban sallah daya gabata wanda akayi ɗinkin hannu.
    Ita kawai tanaso ta burge su Ama sosai yanda za’a basu babu gargada. Sunje gidansu Ama an masu tarban mutunci.
    Dama Babanta shine limamin wani masallaci ɗan madaidaici dake cikin layinsu.
    Sun kaɗa masu jolly juice da panke sai kuma faten tsaki garau garau. Anan aka bada kudin gaisuwa dubu goma sai sadaki dubu hamsin.
    Da farko Liman k’in karɓa yayi saboda yana ganin kamar ya siyarda Ama ne. Shifa bai taɓa cin karo da kuɗin haka ba a tare saidai a baki ko gutsur gutsur.
    Ko kuɗin masallaci dubu arba’in da biyar aka tara bara lokacin azumi.
     Baba yace masa babu komai ai ana tare kawai ya karɓa. Anan yayi godiya saboda Ama tayi goshi.
    Ba karamin mai kuɗi suke kallon Nawaz ba kuma yanzu za’a kara bazawa makwabta.
    Sai aka saka biki nanda wata ɗaya tunda ango yanada sana’ar sa. Ita kam Ama ta zuba garau garau ɗin fatenta a wani faranti mai lamba sai wabta takeyi.
   Liman ne ya shigo ya soma gaya ma Yaya abinda aka kawo, nan take Yaya tayi shewa saida ya kwabeta akan tana shewa gidan Liman. Anan ta saka hannu a baki tana dariya.
    Dama tasan Ama goshin arziki gareta gashi kuma ta kusa fidda su a talauci tunda ɗan Gwaiba zata aura.
     Yanzu tasan yan unguwa zasu fara mata bakin ciki tunda zata fisu kumban susa. Kawai su bita a hankali domin ba kowane kwashi karab zata gayyata ba.

   Ita Mermer kam babu labari sabo, tana cikin jarabtan rayuwa. Tsanani yana kaima Anty Bilkisu karo saboda tana cin karenta babu babbaka.
   Koda mutanen mai martaba suka zo duba Daddy saboda ya kusan wata hudu baije fada ba.
    Anan tayi masu wankin babban bargo na rashin mutunci kuma ta gargadesu akan kada kowa ya sake zuwan mata gida.
    Dama Mai martaba yaji labarin cewa an mashi asiri yasa ya tura mutane akan suji gaskiyar lamarin.
   To wulakancin datayi ya tabbatar mashi da komai.
Anan ya samo manyan malamai suka rinka yin masa addu’a ko Allah zai fishe shi.

Brooklyn, NY
      Sanye take da wani palazzo jumpsuit ɗin Nina Ricci, saita saka ankle black boots ɗin René Lacoste, daukar wani purple dogon three-quarter jacket tayi mai spikes da stones ta haɗa dashi sannan ta yana kanta da bak’in gyale.
      Fuskanta babu kwalliya kuma kyanta yana nan. Ita ko a haka taga tayi make-up sosai.
    Kwarjininta yana nan mai cika ido, tana fitowa falo taga Hamza ya tsaya jiranta shima yayi kwalliya.
    T-shirts ne mai kalar toka wanda akwai tambarin Apple akai, saiya saka crazy jens da kuma sneakers. Ya kuma ɗaura hular baseball akansa.
    Ko bata faɗa ba tasan yayi kyau, shima kallonta yakeyi yana yabawa.
    “Muje koh!” tace da guntun murmushi a bakinta.
    Tashi yayi ya ɗauki mukullin motarsa. Shine yace su rinka fita shakatawa idan bashida class saboda shakuwa ya soma bunkasa tsakanin su.
   Itadai kamar rakuma da akala ne, batada na cewa duk abinda yake so zatayi. Akwai aureshi akanta kuma tasan illar bijire mashi.
     Itafa babu karatun auren da bata sani ba kasancewar Mommy kullum saka mata tafsir ɗin zamanta kewar gidan miji takeyi.
      Suna shiga cikin gari saiya kaita fashion show ɗin Naeem Khan. Dukda batasan waye shiba amma yadda taga ya biya 1000 dollars wajen siyan ticket ta gane ba karamin waje bane.
    Ga kuma manya manyan mutane kamarsu Rihanna, Beyonce, Janelle Monae, T. I, Emma Stone, The Weeknd da dai sauran wanda suka sharara a TV.
    Anan ne ta gane waje babba Hamza ya kaita saita sake respecting ɗinsa.
   An zazzauna dukda a layin karshe suke saboda gaba gaba sai manya yan wane da wane, bata damu ba because shiga ma wajen aiki ne.
   An kashe wuta Taylor Swift ta soma waka saiga models sun fara fita kan runway cikin kaya masu kyan gaske.
   Shi karin kansa runway ɗin abin kallo ne saboda Swimming pool ne a tsakiya sai aka saka dogon katako inda ya rasta waje biyu na zuwa dana fita. Sannan kuma ga fireworks suna tashi daga gefe. Sai kuma cikin ruwan akwai wasu kananan faranti na alfarma mai dauke da karamin candle.
       Kendall Jenner ne ta fara fitowa cikin wani X-ray Material na dinkin short gown. tana kuma makele da wani leather jaka sai takalma flats masu igiya. Ga kuma tabarau mai yanayin kiss a idonta 
    Tana tafe cikin kwarewa a matsayinta na model har taje ta dawo, daga nan sai Gigi Hadid ta fito itama.
    Hunaisa bata taɓa ganin kawataccen waje haka ba, haka suka gama kallo shi ne kowa ya shiga shopping. Shidai Hamza wani gyale ya siyan mata na 200 dollars sai suka tafi.
    Daga nan sai suka wuce Central Park garden sukayi ordering burger Wajen masu siyarwa. Sunci sunyi nat saiyace saura waje ɗaya kuma zasu kafin suje gida.
   Ita a lokacin tayi likis ta gaji amma haka ta jure ta tafi, Shahararren Empire state building ya kaita chan hawa na karshe a inda zaka iya hangen Newyork baki ɗaya.
    Shifa duk kashe kudin nan dayake yi baifi dan ya burge Hunaisa ba, kuma Yadai lura fuskanta babu yabo babu fallasa. Amma expression ɗin datayi da suke sama ta karshe ya nuna mashi cewa wanka ya biya kudin sabulu.... Wannan kenan!






#YGG







DIMPLΣS ce

'Yan Gidan Gwaiba (Completed) Where stories live. Discover now