Twenty-four

3.5K 267 32
                                    

Gwaiba Manor...

   Momee da kanta ta shiga kitchen domin ta haɗa dinner, ta soma kenan tareda taimakon Anty Madina saiga Nuwairah ta shigo, “sannu da aiki Momee” tace, ita kuma ta amsa da, “uhum
    “Momee me zan tayaki dashi?”
   “Na hutarshe kiMomee ta amsa a dikilce. “Kokuma Kije kiyi faɗa da yaruwanki tunda nan kikafi karfi
    “Please Momee kiyi hakuri ki yafe mana, wallahi aikin sheɗan ne”
    Momee bata amsata ba, aikinta ta cigaba saima Nuwairah data mayar da ita kamar madubi.
    Da taga zata ɗauki koda kwano ne sai tayi maza ta mika mata. Tuwon shinkafa tayi da miyan agushi wanda yasha kayan ciki, stock fish, busarshen kifi da ganda.
    Anty Madina ta yanka Ugwu sai Nuwairah ta buɗe ledar tuwon, duk yanda Momee ta basar da ita amma taki barin wajen.
     Haka suka gama tas, a lokacin har Anty Madina ta markaɗa abarba da kwakwa tareda saka masu kankara.
     Daga nan sai Nuwairah ta wuce dinning table tayi setting dinsa yadda ya dace, haka suka jera komai yayi kyan gani sai suka wuce domin sallah akan cewa dinner karfe takwas ne.
       Shikuma Baffa tunda ya fita sallar Magrib bai dawo ba sai da yayi Isha. Anan masallaci ya zauna yana tarban mutane.
     Masu matsala na kawowa, su CV ne, su matsalar kudine da kuma sauran su.
     Haka ya gama dasu har wajen takwas da mintuna ashirin.
        Sanda ya shigo harsun fara cin abinci, Nafisa da Nabila sun kusan gamawa.
      Shima zuwa yayi ya zauna a master chair wanda ke opp na Momee. Da sauri Nawwarah ta tashi ta rinka zuba mashi, kana ganin ta kasan neman fada takeyi.
      Bayan ya gama ci saiya mik’e tsaye, saida yayi tafiya har wajen staircase saiya juya, “Nawwarah da Nuwairah kuzo ku sameni a falona”
        Su biyun gabansu ya faɗi saboda maganar da suke jira ne za’ayi yanzu. A gurguje Nawwarah tasha Fruits salad ɗinta wanda ɗabi’anta ne. Ita kuma Nuwairah wanke hannu tayi saita nufa sama.
      Momee kam daukar Nabila tayi wanda tanata gyangyanɗi a kujera domin ta kaita ɗakin kwanciyar ta. Saida tayi mata addu’a sannan ta rufeta da bargo tareda kunna mata AC, daga nan ta rufe ɗakin ta wuce falon Baffa itama.
   Babban falo ne wanda ya amsa sunarsa, komai a cikinta fari ne tas sai su TV masu ruwan toka. A tsakiyar falon ta sama wani tabkeken chandelier ne a mak'ale.
     Kujerun ciki kana ganinsu kasan custom made ne, three seater ɗin vintage ne from the 70s, sai sauran daga Denmark aka k’era su.
      A bangon falon akwai wani painting ɗin tambarin arewa mai girman gaske, sai kuma wani painting ɗin De Vinci na ocean.
      Samsung TV ne mai 72’’ ke makele a bango, sannan akwai fire place daga bango mai amfani da remote. Suma karin kansu labulen ɗakin da remote ake rufewa ko buɗewa.
     A tsakiyar falon wani table ne round wanda wuta ke fita Blue flame daga ciki, koda suka shiga falon Baffa yana zaune akan Favorite couch ɗinsa watau vintage ɗin 70s.
     Magazine ɗin Fifth Chukker yake dubawa, a gaban da hotansa akeyi amfani an rubuta ‘meet the prominent and popular Yusuf Gwaiba’
      Ya buɗe ciki yana dubawa yadda akayi su tournament ɗinsu polo, koda su Nawwarah suka zo a kasa suka zauna.
    Momee itama kusada shi ta zauna tana duba email ɗinta ta laptop ɗinta na Mac book.
     Babu wanda yace ma twins komai har wajen minti ashirin. Su kuma duk zaman ya ishesu sai sukur sukur sukeyi, saida Baffa yaga dama ya ajiye magazine a gefe yayi gyaran murya.
    “Nuwairah” ya kirata
    “Na’am Baffa”
    “Nawwarah”
   “Na’am Baffa”
     “Naji irin zaman da kukeyi, watau yanzu irin tarbiyan da kuke nunawa kenan, ka rasa abokin gabanka sai dan uwanka”
   “Ai wallahi gabana faɗi yayi danaji yadda suke watsa ma kansu kalamai” Momee ta chapke
   “Yanzu saiku gayamin abinda ya jawo maku wannan ɗiban albarkan?”
     Anan sukayi shiru babu wanda yace komai, bakajin komai sai sanyin AC dake tashi.
     “badaku akeyi ba?”Momee tace.
    Anan sukayi sake yin shiru, kowa kanta a kasa. Baffa ne yace ma Nawwarah tayi magana koya kwaɗeta.
   Anan ta zayyana mashi cewa Nuwairah ce take zuwa wajen saurayinta a matsayin ta. Anan Baffa ya rinka salati tareda Momee, sun mayar da hankalin su kan Nuwairah daketa kuka.
     tambayan Nuwairah itama akayi, saita faɗa batasan cewa yasan Nawwarah ba. Duk zatonta ita yake so amma ta lura wata sa’in tana mashi gizo da Nawwarah saidai bata dauka komai sai randa ta mashi tambaya yace ai ba ita yakeso ba Nawwarah ne.
      “Yanzu ke Nuwairah kin sanshi ne?” Momee ta tambaya, girgiza kanta tayi alamar eh tana kuka.
    “Nawwarah fa?”
    “Eh Momee ina sanshi”
   “Zancen banza zancen wofi, banda rashin hankali kun taɓa ganin inda yan biyu suka so mutum ɗaya?” Momee tace
    “Wannan wani irin rashin hankali ne? Idan an hanaku mutuwa sai ku suma. Toh Wlh bazan lamunta ba dole na ɗauki tsartsauran raayi a kanku” Baffa yace
     Shi Baffa bayasan auren haɗi da akeyi, ya fison yaransa su kawo mazaje da kansu. Ko yanzu haka yaran gwamnoni da manyan attajirai sunata masa maganar ko za’ayi haɗin dasu.
    “Kawai a haɗa ɗaya daga cikin su da Shehu Usman yaron Yaya Abubakar, kasan shima yaki aure ga kuma zafin kai sai yayi maganin rashin kunyarsu” Momee tace
    “Toh shikenan haka za’ayi kuwa, daya daga cikin ku zai aure Jalaluddeen ɗaya kuma zai aura Shehu Usman. Shi kuma Jalaluddeen zan masa magana na bashi yarinta ɗaya idan yanada hankali zaibi duk zaɓin dana bashi”
     “Toh saiku tashi ku tafi” Momee tace, haka suka tashi suna jan kafa, kowa burinta baifi a bata Deenie ba saboda sunsan halin YaShehu. 
    Soja ne yana aiki a Abuja kuma bashida wasa kwata-kwata, shine ma discipline master a cikin family, yanzu yanzu saiya sakaka tsallen kwaɗo dasu pumping.
    Sanda suke yara idan sunje Gidan Gwaiba yana cin ubansu ba kaɗan ba, domin babu wanda baisha zana ba a wajensa.
    Shifa hayaniya ne bayaso, ko kayi barin abu a waje. Idan ka cika surutu bazaku taɓa shiri ba saboda zaita jibgan banza.... Wannan kenan!

     FCT Abuja..

       Sanye yake da desert camouflage na sojoji. Kafarsa kwabɗeɗan takalmansu ne akai. Sai kuma bak’in tabarau a fuskanshi.
   Yana zaune cikin KFC yana cin abinci, latsa wayarsa yakeyi a lokaci ɗaya. Ya gama shan roban coke na farko ya buɗe na biyun har yakai rabi.
     Wasu matasa ne su uku suka shigo chachacha suke zuba surutu, tattara takardunsa yayi da wayansa tareda mukullin mota ya fice.
     A duniya baya san hayaniya, yasa ma ya shiga aikin soja, kuna magana ya daka ku. Ko sanda yake NDA idan yana tafiya ko abinci kake ci zaka tsaya saboda idan yaji karar cokali ranar naka ya kare....Wannan kenan!




#YGG




DIMPLΣS ce
     

'Yan Gidan Gwaiba (Completed) Where stories live. Discover now