Thirty

4.9K 281 23
                                    


Kamar yadda last Don ya faɗa akan idan sukaje Airport zasu kira 9-1-1 haka kuwa akayi.
Ya siya burner phone ne wanda zaiyi amfani dashi, sun siya one-way flight ticket to Abuja. Hamza fuskarsa yayi jazur Last Don ya siyan masa tabarau saboda ya ɓoye.
Harara ya watsa masa san rai kafin ta karɓa. Yana bala'in jin haushin Last Don, wai yazo da Oga Daddy gidansu babu ko sanarwa.
Shi ya dauka amintansu yafi haka, ya ɗauki Last a matsayin elder brother he never had. Koda yake dama ance blood is thicker than water but interest is thicker than blood.
Interest ɗin last yayi kuɗine kuma babu ruwansa akan wanda zai ha'inta. Rubutu Last Don yayi a takarda saiya bama wani yaro haka kafin sukai Airport din Akan yayi waya tareda karanta abinda ke ciki.
Ko sanda yaron yayi wayan akayi tracing wayan zuwa inda yake. Yan sanda ne sukayi masa cha akwai, anan ya fara kuka akan cewa 20 dollars aka bashi akan yayi wayan.
Koda suka isa Brooklyn lokacin Hunaisa tayi kuka tayi likis kamar alayahu. Nan aka kwanceta tareda bata first aid.
Duk yanda akaso tayi magana ta kasa, babu abinda ba'a tambayeta ba amma bata ce komai ba. Har yanzu tana mamakin abinda ya faru da ita.
Wani security ne rikeda MacBook a hannunsa yana dubawa, zuwa tayi wajensa tana tangal tangal ta amsa.
Google ta shiga saita rubuta Gwaiba, anan sunar Baffa ya fito. Nan take aka gane abinda take nufi.
Shugabansu na CIA suka kira suka faɗa mata ga abinda ake ciki, cikin mintuna aka samo Personal line ɗin Baffa Yusuf.
Shikam Baffa yana barci saboda cikin dare ne kuma kusan 10hrs difference. Cikin barci yaji ana masa maganar Hunaisa.
Da sauri ya gyara zama sosai domin yaji me ake cewa, anan sukayi masa bayani sunga yarsa Hunaisa. Hamdalah ya somayi saboda duk sanda yaga Gwaggo Dija saita tuna masa cewa duk kudinsa amma an kasa gano Hunaisa.
Cewa yayi zai shiga jirgi yanzu yanzu, kiran Major Musa yayi akan abinda ya faru. Shima anan ya kafe zai bishi.
Mommy kam murna ta somayi, taso ta bisu amma babu hali. Sallah ta shiga yi raka'a bayan raka'a.
Major Musa cikin kankanin lokaci ya haɗa kayansa da International passport ɗinsa. Shi kuma Baffa ya kira pilot ɗinsa a waya akan yazo zasuyi tafiya.
Ranar gabadaya YGG basuyi barci ba, kowa nata zulumi. Gashi gobe za'a fara events gadan gadan.
Suna isa Washington DC suka wuce chan Head office din CIA aka kai Hunaisa. An bata abinci kuma ta canza kaya ta kimsta.
Anata mata tambaya amma batace komai ba, ko takardar sakinta bayan an kwanceta tayi wuf ta dauke ta saka a haɓan skirt ɗinta.
San datake ma Hamza bazai barta ta faɗa masu komai ba, tasan cewa ko ba'a kashe shiba zaici bakar wuya.
Anyi ma Baffa bayanin cewa har yanzu batace komai ba, "Thank you for retrieving her, but she's been through a lot and need to be with family and loved ones right now" Baffa yace.
Dole suka yarda akan su sallameta saboda ansan cewa sabon shugaban kasa watau Donald Trump yana respecting Baffa saboda gaskiyar sa.
Yanzu idan Baffa yayi masa magana zance zai taɓarɓare. Hunaisa tana ganin Daddynta ta fashe da kuka tareda fadi jikinsa. Shima kawai dan Soja ne yasa baiyi ba.
Anan suka kira Nigeria, Gwaggo Dija aka soma kira domin a sheda mata. Dama tun data samu labarin anga Hunaisa taketa zirya tsakanin bayi da ɗaki.
Bayan nan aka kira Mommyn ta, Hajia Zainab tana jin muryan Hunaisa ta fashe da kuka. A duniya ta riga ta cire ran sake jinsa.
Sun shiga jirgi zuwa Nigeria, wannan karon a Zaria suka sauka ta Aviation. Motaci sunata jiransu harda Mudassir.
Mamaki yakeyi wai Hunaisa ɗinsa aka gani, burinsu ya kusan cika yanzu saboda idan ba wani ikon Allah ba auren su yana kusa kusa.
A falon Gwaggo Dija aka zauna, gaba daya YGG an hallara. Dama gashi duk anzo bikin twins har mutanen Lagos.
Nawwarah ma taje saboda suna ɗan ɗasawa da Hunaisa. An sakata a gaba anaso aji komai.
Anan ta basu labarin yadda suka tafi da ita daga kofar gida, har zuwansu Mexico sannan America. Kuma ta faɗa masu cewa Hamza ya aureta da karfin tsiya yanzu data isheshi ya saketa.
Karya sosai ta shararo, bata nuna ko sau ɗaya taji daɗin zamanta dashi ba. Ko da aka Tambayeta sunarshi tace bata sani ba saboda basa magana.
Anan aka rinka Salati, Aikuwa yasha tsinuwa wajen Gwaggo Dija. Hunaisa bataji daɗin abin ba amma babu yadda zatayi.
Nan YGG suka soma biki gadan gadan, hankalin kowa a kwance yake basuda wani matsala sai wanda ba'a rasa ba.
Daga Lagos aka ɗauko masu make up, event planner da kuma Chefs da sauran masu abinci.
Katin aure kuwa na dinner wanda shine zaifi haɗuwa. 300 copies akayi printing daga Italy kuma duk wanda zai hallara an rubuta sunarsa akai.
Na ɗaurin aure kuwa Nawwarah ta tada bala'i baza'ayi a waje ɗaya dana Nuwairah ba. Dole kowa a buga masa nasa tunda ba miji ɗaya zasu aura ba.
Dan raba gardama Momee tace ayi daban, Shikam Baffa sanda ya samu labarin yayita bala'i tareda ma Momee faɗa akan abinda yasa ta yarda.
Momee tasan cewa bak'in ciki ke damun Nawwarah, kuma tayi mata maganar abin. Anan ta fashe da kuka wai sharri akayi mata.
Momee batasan dogon zance kawai tace koma menene yake damunta ta bari, dukda su yan biyu ne ba lallai bane destiny dinsu ya zamanta iri ɗaya.
Gashi Nawwarah sai yaɗawa takeyi wai Mijinta yafi YaShehu komai, a fara daga ilimi, kudi da addini musamman tunda ɗan malamai ne.
Gashi wai YaShehu common Economics ya karanta a NDA, shikam Deenie Doctor ne kuma yanada PhD a psychology. Uwa uba ba'a Naija yayi karatu ba, sannan lefensa da kansa yayi ba iyaye sukayi ba. Haka dai tayita surutu birjik marasa daɗin ji.
They are different individuals kuma mutane daban daban zasu aura. Anan Momee ta roketa dan Allah ta rage zafin data keyi saboda karta kunyatata a gaban kawayenta da sauran al'umma.
Toh fah tun daga nan aka samo dama damanta, ta ɗan sake jikinta kuma tana yawaita fara'a tareda gaida baki yadda ya kamata.
Bridal shower, Mother's Day, Kamu da kuma Dinner ne events ɗin da za'ayi. Dama saboda Momee socialite ne tana zuwa bikin matan gwamnoni yasa itama zata haɗa.
An masu lalle duk a Four Seasons Settle Spa dasu gyaran gashi.
Ita Hunaisa har yanzu tana shock, bataje bikin ba tana gida. YaMudassir kam yana tareda ita sai mata tambaya yakeyi. Bata amsashi sai kuka, shi yasha Missing ɗinsa tayi yasa take kuka.
Ita tunanin inda zata sake ganin Hamza takeyi, tanaso tayi masa tambaya akan dalilin yaudaratan dayayi.
Haka Mudassir ya gama zamansa ya tafi, cewa yayi zasuyi waya anjima. Daga masa kai ita kam tayi.
A wajen Bridal shower Pinky ta saka bak'in leggings da pink custom made pink riga Wanda aka rubuta 'Mrs Deenie' ita kuma Nuwairah 'Mrs Shehu'
Sun saka fararen Tiara da sash masu kyan gaske, sai kuma gogayen Hills masu spikes.
Husna ma taje sai salo takeyi, a cake din Nawwarah anyi Carving Lingerie watau Bra and Pant akai in pink color.
Kawayenta 'yan Désolé sai shewa sukeyi sunata koɗata. Ita kuma sai basarwa takeyi kamar tayi abin arziki.
Ita Nuwairah kayan make-up ne nata, shima ya kayatu sosai kalar black and white.
Nawwarah sai rawa take nunawa salo daban daban kamar tana ba'a da wata. Haka ta ishesu ita mijinta kaza ita mijinta kaza.
Yakura cousin dinsu tace dalla ta rufe masu baki, ta wani damesu akan Deenie.
"maza kala kala ne kuma suna suka tara, akwai Face me i face you, akwai 2 bedroom flats, Bungalow, Mansion, Manor etc but Deenie 5 star hotel ne kuma ya kece tsara"
"Ke kika sani" Husna tace.
Tayita salo daban daban yadda zata rinka tarban sa idan ya dawo kuma tace ba zata sake zama akan couch ba saidai cinyarsa.
"Yuck!" Mufeeda tace saita tabe baki.
A wajen mother's day kuma a Kaduna Golf Club akayi, ankon peach and honey brown color of lace ne. Hall yayi bala'in armashi gashi mutane sai tururuwa sukeyi kamar ambaliya.
Balle yadda mutane suka san cewa 300 guests ne zasu dinner na ranar Thursday yasa suka hallara wannan kafin suyi 2-0
Su kuma amare sun saka Lilac gown mai bala'in jan kasa sai sukasa purple head da kuma purple clocth mai yanayin Bow.
Ita kuma Momee ta saka Purple lace wanda akayi ɗinkin Iro and Buba. Abu yayi armashi fiye da yanda ake zato.
Ana cikin Hall sai akace Amare da Momee su fita filin rawa, anan aka saka masu wakar 'Sweet mother i no go forget you for this suffer wey u suffer for me'
Rangaji sukeyi gabadaya suna hawaye, sun tabbatar cewa daga yanzu idan bata kama ba bazasu sake zama waje ɗaya su uku ba.
Nan Momee ta rungume twins ɗinta sunata kuka, kowa a hall ɗin yaji abin. Daga nan aka saka masu wakar 'My baby my mother, I love you forever'
Sun sha liki sosai sai DJ ya saka wakar Dolly Parton na 'Jolene' nanfa iyaye mata suka motsa jiki a filin rawar an tuna su 60s and 70s. Sai kuma a saka nasu Kool and the Gang.
Anan kowa kema Hajia Hussaina murna da fatan alheri zata aurar da yaranta guda biyu a maran nan da ake scarcity of husband.
Biki yayi armashi sosai anci ansha sosai ga kuma souvenirs birjik. Su Nuwairah basuyi pre-wedding pics ba, su Nawwarah ne sukayi.
Sunyi da kayan Polo, Basket ball, coperate wears, native wears da abaya.
Wajen kamu kuma a Murtala Muhammad Square Multi purpose hall sukayi. Atampha Gwaiba wax suka saka riga da zani sai sukayi mayafi da atamphan.
Nura M Inuwa yazo da kanshi, sanda amare zasu shiga Hall saiya soma wakarsa na 'Yar Amana' bayan nan kuma sun zauna sai aka saka wakar jeran kumbu na amare.
Maman Husna itace ta kama Nuwairah tunda mijinta ne babba a family sai kuma Anty Aisha yar uwan Deenie tayi ma Nawwarah.
Kawayen Pinky saida aka basu dubu dari kafin suka yarda aka Kamata. Sukuma na Nuwairah sukace basaso saboda abin arziki sukazo.
Anan aka fesa masu turare sai aka tsoma hannayensu da kafa cikin ruwan lalle tareda gogewa da wuri kafin ya ɓata na jikinsu.
An kira Boda da Ado Gwanja shima yayi wakarsa na kujerar tsakar gida.
Haba nan hall ya rude akayita babbaka rawa, Pinky sarkin rawa tayi sosai kamar ba amarya ba. Saida Anty Hassana watau sister ɗin Momee ta harare ta. Anan ta fara rangaji tana jin haushi.
Ita Nuwairah murmushi takeyi tunda dama jikinta babu engine oil ko daya yasa babu rawar data iya. Haka shima akayi events cikin arziki.
Ranar Alhamis za'ayi dinner party, Baffa ne yace babu wanda zai masa bidi'a a gida bayan daurin aure yasa komai za'ayi kafin Friday.
Kuma a ranar ne Deenie zaiyi Bachelors Party ɗinsa. Shehu shidai friends ɗinsa sunce sai anyi crossing of the sword Kafin a shiga hall ɗin.
Babu yanda zaiyi dole aka rinka practice, dayake yanada good human relationship, abokansa sunzo wajen su 15 ga kuma sauran wanda sukayi secondary da primary.
Office Boss dinsa Brigadier General S Z Kazaure ya amsa RSVP yace zashi dinner. Sannan ga kuma abokan Dad dinsa masu kumban susa.
Shi kawai yanzu he has an open mind akan auren, kwata-kwata baisan meyake soba. Kawai yana jira agama shagali ne yayi sorting komi.
Husna ta gayyace Hajja Zee da TK domin tuni sukayi anko saboda yanda Husna ta ishesu da cewa sunada gagarumin biki.
Wajen karfe takwas na dare ne lokacin dinner kuma za'ayi a Fifth Chukker Polo Club dake Maraban Jos.
Su Twins da friends ɗinsu tun wajen ukun rana suka tafi saboda su fara su make up da sauran su.
Kowa ta sauka a narkeken Master Room da kawayenta, Mostly wanda suke tareda Nuwairah Cousins ne wanda tadan girma Kokuma suka girmeta.
Husna kam tana tareda Pinky yar karya. An fara masu kwalliya amma saida sukayi alwala tukun saboda Sallah.
Itama Momee da sauran Yan uwa an kai masu nasu mai kwalliyar.
White bridal gown suka saka iri ɗaya, ko make up iri ɗaya Momee tace ayi masu.
Nawwarah bata soba ita tafisan tayi harsh make-up ɗinta na fama na smoky eyes da red bold lips.

7:45pm
Security ne aka baza birjik a cikin garin Kaduna, manya manya masu faɗi aji a Nigeria da sauran duniya baki ɗaya sun sauka a airport zasu Dinner of a lifetime.
Convoy set by set suke wucewa kan titi, kowa ya kure a daka zashi bikin YGG. Kuma rules ɗin IV saika wuce 15yrs saboda haka babu yara.
Maza sun saka Farin kaya da blue hula, mata kuma Lace ne pink sai lining ɗin ciki da blue tareda blue kallabi ko gwargwaro.
Tunda anyi anko babu damar karyan kaya, a wajen jeweries dasu takalma aka nuna bambanci.
Daga su peep-toe, wedge, pointy Jimmy Choos, Gucci, Marc Jacobs, Michael Kors da sauran designers masu faɗi aji a fashion industry.
Kana shiga Hall ɗin zakaga anyi decorating ɗinsa da sky blue and egg shell crystals, Throne chairs na amare mai double guda biyu zaka hanga fari sol daga chan kurya.
Sannan wedding aisle din anyi decorating gefensa da pink and blue crystal Wanda aka sagalosu daga ceiling. Ga kuma flowers su Lili, Hydrangeas, roses da Dalia a cikin hall ɗin wanda ya kara armashi.
Ta wajen kujerun amare akwai narkeken dance floor. Kuma anyi roofing kujerun amaren da crystals farare masu wuta.
Cakes guda biyu akayi masu hawa shida farare tas, a wajen hawa na ukun zuwa na hudu anyi Carving rose wanda rabinsa daga sama sai sauran daga kasa, gashi kuma wajen na kasan an zagaye da feathers masu kyau. Sannan anyi topping da crystals wanda ya kara k'ayata shi.
Mutane sai zuwa sukeyi, duk abinka da kushe abu saika yaba da wajen, an zazzauna an fara taɓa su lemu da suke kan table wanda shima table'n fari ne sai wani candle da akwai ruwa a cikin k'ok'on.
Su Anty Bilkisu saida aka tasa Mermer a gaba tayi mata kwalliya saboda tasan zataji kunya da irin make up ɗinta.
Mermer tace taje ta samo nata kayan kwalliyar amma ba nata ba, haka taje ta siya saboda ta riga ta kwallafa rai sai taje bikin manya.
Kasuwa taje ta siya Lace ɗinta pink na dubu saba'in, saboda a card ɗin an rubuta dress code.
Mermer tayi mata kwalliya tareda ɗaura mata gwagwaro. Haba tana ganin yanda ta haska saita soma fito da baki, burinta baifi taje tayi ma matan Manya shishigi ba.
Femi Otodola, Mike Adenuga, Sabon CEO ɗin MTN Mr Shuter shima ya hallara tunda Baffa yanada hannun jari a wajen.
Gwamnoni wajen 18 sukaje wanda basu samu damar zuwaba sun aika deputy dinsu.
Taron masu shi kake gani kowane k'usa bayaso a barshi a baya.
Baffa mamakin irin zuwan da akayi yayi, kuma duk wanda yaje saiya je ya gaida shi.
Dayake suites ɗin akwai ɗan tafiya tsakani da Hall ɗin, Deenie yafara isa da Range Rover fari tas, nan Nawwarah ta fara ɗaga kafaɗa mijinta ya iso.
Shikam Deenie sai yanzu ya lura Nuwairah tafi kyau gashi tafi sirinta. Ita kuma ta fara daina sanshi, Infact haushin sa taji dataga yanayin abokansa kamar wanda suka K'wale.
Nan George Okoro, AhamdZol, Steve reinz, Maigaskiya suka soma masu hotuna. Dama an riga anyi ma amare personal
Ba'ayi 5 mins saiga kidan sojoji yana tashi. Hilux ne a gaba cike da sojoji sai convoy ɗin motoci goma a baya sun nufa inda suke.
Nan su Stevereinz suka kyale su Nawwarah suka fara Video covering convoy ɗin.
A tsakiya wani Bentley ne baki wanda Abban Shehu ya bashi yayi amfani lokacin bikinsu, sanye yake da farin shadda ɗinkin babban riga tareda farin hula da takalmi.
Da kansa ya fita yaje inda Nuwairah ke tsaye, salute ya fara mata saiya ce, "Hi! Shall we?" daga nan ya mika mata hannu.
"Of course" tace tana murmushi sannan ta mika masa hannu suka tafi, masu hoto ne suka ruga a guje "Sir please let's take you one shot"
Kallonsu yayi da smug face yace, "no" saiya buɗe ma Nuwairah ta shiga ciki shima ya shiga.
Kowa a wajen abin ya burgeshi, har Deenie amma banda Nawwarah. Tsaki tayi ta shiga mota masifa yana cinta.
"Idan suna tunanin cewa zasu rigani shiga Hall ɗin ne Toh Wallh sunyi karya"
Shikam YaShehu bai sake cewa komai ba, dama yayi ne domin kada ya bata kunya saboda tun daga nesa yaga ta tsaya frustrated.
Suna isa Hall ɗin sai friends din Shehu all kitted in military attire da swords zasuyi crossing.
Nawwarah ce ta fara masifa ita ba zatabi karkashin wuka ba kamar tsafi. Saidai Nura M Inuwa yayi wakarsa na Tambarin Ango da Amarya yayin dake shiga.
Haka kuwa akayi, ita ta fara shiga ciki, ana wakar nan gata tasha ado sannan Deenie da Entourage ɗinsa da kuma nata suna biye dasu. Sun sha tafi kuma sunyi armashi
Sun zaune kenan sai kida ya canza, dama DJ Xclusive aka gayyata da kuma Basket Mouth a matsayin MC. Nan ya fara cewa, "Oya Make una all stand up bcs soldiers wan do deir own, our amerya(Amarya) and Ango wan waka in a grand style"
Kidansu na sojoji aka fara Sawa, sannan sojoji suka shiga Hall ɗin. shi kuma Jabir abokinsa ne zaiyi commanding parade ɗin. Sukan suna cikin mota basu fito ba.
'Attention by number code one, code two' sai suka rinka yi.
'Parade in quick match, division in two columns by the centre, quick match, left wheel'
Anan suka rinka yi, saisu Shehu suka fito, nan Jabir ya bada Parade command akan su ɗaga wuka da sauran su.
Nan hall ya rikice anata ihu ana fito kowa abin ya burgeshi. A hankali Nuwairah take takawa da angonta a gefe. Husna taji haushin data bi Nawwarah da yanzu sune wannan.
Chan cikin ran Nawwarah taji haushin gangancin datayi da yanzu itama za'ayi mata.
An zauna sai Baban Husna ya buɗe taro da Addu'a, sai Baffa ya tashi ya bada opening remarks tareda gode ma kowa daya hallara.
Umaima ta bada biography ɗin Nawwarah sai Anisa ta bada na Nuwairah. Jabir ya bada na Shehu sai Tunde ya bada na Deenie.
An fara saka waka amare da angwaye suka fito. Saiga theatre smoke and fog ya fara fitowa ta ko'ina musamman kasa, Su Nawwarah da Deenie sai rawa sukeyi, balle dama Deenie rainon club ne, tare idan mutum ɗaya ya dauki azonto dayan ma zaiyi, sunayi suna crip walking
Anata tafi, ita Nuwairah rangaji tayi shima angonta haka. Sai kawai Dj Xclusive ya saka 'Kolewerk' ashe Shehu yana san wakar.
Tun kafin ya fara rawa guys dinsa suka shiga filin rawa a guje, gashi dama sojaji da rawa.
Ya fara rawa kenan sai aka kai wajen lyrics ɗin, "Paskalavista, can I be friends with your sister
Don't get it twisted I'm a mister
I'm a young man also a barrister
Paskalavista, can I be friends with your sister" sai yaje gaban Nawwarah yanayi tareda nuna Nuwairah. Aiko ta shaka sosai saboda ta rinka balla masa harara.
Aiko sai aka fara wani baiti, "Shu shuperu
Warri Warri do
Someone cannot play with you
Is dat how you used to do"
Nan Hall aka soma dariya saboda duk anga abinda ya faru. Ko Momee saida ta dara.
Sai aka saka wakar 'IF' anan Shehu ya soma bi, "my money my body na your own oo" tsaki kam Nawwarah tayi a ranta, 'jibeshi babu tarbiya kamar rainan club'
Falz ne da kansa ya fito, wakarsa na 'Soft work' yayi. Nan sojaji suka rinka rawa balle ma Jabir ya gurza sosai. Deenie ma haka dasu abokansa su Chike da Tunde sai triplet Abdulhafiz, AbdulRazaq, Abdulbasiq.
Yan mata ma sunyi sosai balle da sukaga sojaji, nan aka rinka ballin naira da dollars.
Wanda suke lik'e bandir suke kwance wa a filin kuma su karar.
Ko Husna tayi rawa tayi lik'e, Anty Bilkisu ma haka sosai take juya jikinta kamar tana cultural dance.
Bayan nan aka yanka cake, 'LOVE' sukayi spelling suka yanka. Deenie saida ya rinka wasa da cake ɗin kafin ya bama Nawwarah har saida ta kulu. Ita kuma harda rinsinawa saboda ta k'ayata abin.
Shiko Shehu salutu yayi ma Nuwairah saiya bata, itama ta yanka ta bashi.
An cigaba da raye raye inda masu k'oroso sukayi rawa da masu siddabaru suka rinka hura wuta ta bakinsu.
Lokacin item 7 yayi watau cin abinci, waiters birjik suka rinka shiga. Zaka faɗa abinda kake so sai a kawo maka.
Akwai Arabian cuisine, French cuisine, African cuisine Duk wanda kake so.
Kowa yaci ya ture wasu kuma ana cin abinci rawa sukayi basu ciba.
Daga nan aka fara bada gift, zaka mike tsaye idan zaka bada abu.
"Na bama amare kyautar mota" FCT Minister yace. "Na bama amare dubu dari dari" Matar gwamnar Kaduna.
Haka a suka rinkayi anayi ana masu tafi. Itama Anty Bilkisu tace ta bada dubu ashirin ashirin. Sister ɗin Deenie ta rufe taro da addu'a saboda dare ya tsala.
Snapchat yayi kuka ranar saboda yanda kowa keso ya nuna ya je, haka akayita hoto su George Okoro sai kashe masu Shehu yakeyi da Nuwairah.
Wajen 12am Shehu yaja hannun bride ɗinsa saboda su tafi, haka sojoji suka rinka binsu a baya suna ihu, "Na you be the guy, see babe abeg" kunya take ji sai turgudewa takeyi. Da badin tana rike da Shehu ba data fadi.
Su Nawwarah sai watsa shoki dasu dab sukeyi, basu suka bar Hall ɗinba sai 1:30am
Deenie yana ajiyeta suka wuce club 'Ibiza' domin bachelor's party.
A mota suka canza zuwa kananan kaya. Yau kwanar Club zasuyi.
Suna shiga kida ya canza manya sun iso, VIP table aka basu. Su Vodka ne masu dankarin tsada aka jera akan table. Sai kuma su Triplet suka fito da hodar ibliss domin su shaka.
Deenie baya shaka saidai yana shan kwayoyi da chan sanda suke USA tunda anan suka haɗu su duka. Yau kam yasha kuma wanda kwaya ɗaya 30k ne kuma akalla mutum zai sha biyar.
Nan suka soma shan Shots, anayi ana ihu. A kalla Deenie yasha Shots hamsin.
Nan kansa ya ɗauki Charging sosai, yayi niyyar tashi aka rike mashi jiki, "One more, one more, one more" aka rinka ihu. Haka ya kwace shot ɗaya ya shanye.
Sai Dj yace "Let's give it up for the man of the hour, our latest groom Deenie" an soma tafi raf raf raf waka yana tashi sai Deenie ya mike yana tambele tareda daga masu hannu.
Yan mata ne masu gashin kanti suka zagaye shi sai rawa sukeyi a jikinsa, anan ya fige guda biyu ya wuce guest rooms din wajen.
Bashi ya farka sai 11pm. Yanmata ya gani a jikinsa suna barci tareda munshari. Kana ganinsu kasan anyi masha'a a wajen..... Wannan kenan!!


#YGG


DIMPLΣS ce

'Yan Gidan Gwaiba (Completed) Where stories live. Discover now