Twenty-three

4.4K 266 11
                                    

     Sharhin shafin daya gabata daga Naima Abbas Hamid babban masoyiyar YGG

Assalamu alaikum

Allah sarki yan gidan gwaiba suna ganin iftila’i


Asmaul husna Allah yasa wannan muguwar lubie din karta kaiki ta baro

Nuwairah Allah ya musanya miki da mafi alkhairi ita kuma Nawwarah taje can ta karata tata jarabar kenan ta tsanar yar uwarta

Hunaisa Allah yayi miki zabi mafi alkhairi

Kai kuma Deenie kaje gaka ga Nawwarah nan

Ke kuma gwagwgwo Allah yasa bakiyi zaben tumun dare ba

Kema Mermer Allah ya futar dake ko ba komai kya koyi daraja dan adam

Nawaz Allah yasa biyayyarka ta zame maka alkhairi


A karshe nake maki fatan alkhairi DIMPLES Allah yasa kifi haka.  


#ANA TARE


*******

Bayan sati uku....


Brooklyn, NY

    A karo na farko tun zuwan Hunaisa gidan tayi masu breakfast. Bawai shi ya sakata ba a’a ra’ayinta ne tun jiya da daddare ta daukin ma kanta wannan alkawarin.
     Karar agogon dake gefen gadonta ya tadata sallar asuba. Da farkon zuwanta Hamza kullum saiya zo duba ko ta tashi kuma yana yaba ganin idanta biyu a wannan lokacin.
    Yanzu dai abu ɗaya ne ya kwanta mata a rai game da Hamza, yanada san sallah kuma dama burinta a duniya kenan.
    Duk mugun halin mutum idan yana sallah yana zuwan mashi da sauki kuma a kyautata sa masa rai akan denewa. Koba komai alwala yana kara karfin imani.
     Bayan tayi sallah tareda yan addu’a saita wuce kitchen kai tsaye. Dube dube ta somayi cikin shelves domin taga menene akwai a gidan da zaka iya sarrafawa.
   Anan taga flour, kwai, cheese, madara, butter, syrup, fruits dadai sauran su. Dayake taje catering school wanda ake bridal package za’a koya maka sarrafa abinci kala kala.
    Anan ta markada strawberries da ayaba a blender saita zuba cikin wani farin kwano ɗan madaidaici. Toh a ciki ta haɗa su flour, sugar, kwai, madara da butter inda tayi Banana/Strawberry pancakes.
     Sai kuma ta kunna Nespresso machine inda ta haɗa masu Latte Coffee kamar yadda ta lura abinda Hamza kesha kenan kullum daga star bucks.
     Shikuma ranar ma yayi makaran sallar safiya sai wajen shida da rabi yayi kasancewar wajen uku da rabi ya kwanta.
     Ragowar pizza na jiya yakeso yayi masu micro waving, ya fito daga wanka kenan yana goge jikinsa da towel sai ya rinka shakar kamshin abinci.
     Bai taɓa tunanin cewa daga gidansu kamshin yake ba, shi ya riga ya cire a ransa cewa zata taɓa masa girki. Ya dauko sweatpants da riga ya saka sai kuma ya daura hooded blue jacket.
    Tura kofar ɗakinsa yaji anyi yasa ya juya da sauri, Hunaisa ne tsaye fuska babu yabo babu fallasa.
    “Ina kwana” tace a sanyaye
   Da murnar sa ya amsa, “lafiya lau, kin tashi lafiya?”
   “Alhamdulillahi, dama breakfast na haɗa mana yanzu”
   Zare ido yayi tareda haɗiye miyau mai zafi. Gabansa ya soma harbawa, wai Hunaisa ce tayi wani abu domin shi. Tuni ya mance da ita ya shiga duniyar tunani.
   Bubuga kofa tayi saiya dawo, anan ya murmusa sai yace, “Muje”
   Anan ta juya ta tafi, shikuma saida ya tsaya tayi nisa kaɗan,  dribblingbya soma yi kamar kwallon kafa yana wajen saiya naushi iska tareda faɗin “Yeah Yeah Yeah” saiya ɗaga kwalansa ya canza tafiya irin na basawa.
    Murna yakeyi sosai saboda an masa girki, shifa baiki ba koda ruwan zafi ne aka bashi. Yana zuwa wajen dinning ya sake shan mamaki, pancakes ya gani an jera guda haɗu a farin China wares, sai aka saka syrup tareda daura grapes da kuma strawberry akai.
   Zama yayi akan kujera yanayi yana kallonta ta gefen ido kamar yaga fatalwa saboda ba Hunaisa daya sani ba kenan. Itama tasan tayi mashi bazata sai tayi guntun murmushi irin ya yarda da ita babu komai.
    Bata tafi ba illa ɗauko kwanan nata abincin ta ajiye ta soma ci, tanayi tana kurban Coffee ɗinta wanda ta tsugaga mashi madara da sugar. 
     Kasa hakuri yayi saida yayi magana, “bakida lafiya ne?”
    “I’m fine” ta amsa batako kalleshi ba.
   “me kike so nayi maki?” 
    Da sauri ta ɗaga idanta ta kalleshi, “kasan me nake so... Gidanmu zaka mayar dani”
   “Yi hak’uri ba abinda nake nufi ba kenan” yace a sanyaye.
     “Kawai naji yin girki ne”
   Murmushi yayi saiya soma ci, tun bayan rasuwar iyayensa bai samo nishadi kamar yanzu ba.
   Ya gamaci tas saiya soma lashe kwano, yi tayi kamar batasan da zaman shi a wajen ba, saiya kuma ya kura mata ido yanata kallonta. Daga masa gira tayi alamar ta karo masa ne. Da sauri ya girgiza kansa akan ta bashi.
    Dariya tayi dama neman yada kai takeyi da pancake ɗin, anan ya karɓa ya bige tas.
   Tashi yayi yana mika tareda salati, yanda yakeyi da ita wani zai dauka sun saba. Wayansa ne ya soma ruri alamar kira.
   Ita kuma saita kwashe kwanoni ta soma wankesu da gel ɗin wanke wanke.
    ɗakinsa ya koma domin Oga Daddy ne ya kirasa.
    “Daddy ina wuni”
   “Lafiya lau Boy, ya karatu?”
    “Alhamdulillahi”
     “Yauwa Boy kana Jina koh?”
   “Eh Daddy”
      “Mun riga mun gama shirye shirye akan operation ɗin danake maka magana, yanzu kai kawai muke jira ka gama karatu sai muyi komai, Last Don ya riga ya samo mana duk wani information da zai taimaka mana”
     “Okay Daddy ai saura sati uku na gama”
   “Yauwa yayi kyau, please ka mayar da hankalinka wajen karatu. Dukda nasan babu abinda zai shagalar dakai but inaso ka sake natsuwa da kyau. Wannan operation ɗin babu wanda ya taɓa yinsa a Nigeria kuma idan muka ci sa’a zamu samu kuɗi sosai”
   “Okay Daddy zamuyi waya anjima yanzu makaranta zani”
    “Allah ya bada sa’a” daga nan suka kashe. Zama a bakin gado yayi yana tunani, dama bayan sun gama operation da Daddy yanaso ya ɗauki fansa akan iyayensa ne amma kuma yanzu ga Hunaisa.
    Baisan wanne ne yafi soba? Hunaisa ko Fansa? Komai dayake faruwa da mutum yana linking zuwa wani abu a gabane, da ace iyayensa basu mutu ba bazai dawo zariya da zama ba.
    Kuma idan bai dawo ba bazai haɗu da Hunaisa ba, koda yake Allah ya riga ya kaddara haduwar su kuma dole ne su haɗu.
   Amma kuma yasani babu tantama idan Hunaisa tasan abinda yakeyi zata guje shi, yanzu kawai zaiyi kokarin ya rinka boye mata komai ne har su gama wannan kwara dayan daga nan sai yace ma Oga Daddy shi ya daina kwata-kwata.... Wannan kenan!

   Gwaiba Manor....

      Koda Baffa ya dawo Momee ta zayyana masa abinda ya faru, kuma anan ne tace masa dama tun asali Nawwarah ta raina Nuwairah. Shima anan ya sauke ma Momee ruwan masifa saboda bata faɗa mashi meke faruwa a cikin gidansa ba.
   Kamar yadda ya saba idan ya dawo yana zuwan masu da wani kayan yayee su designers kala kala wanda masu neman fada wajensa ke bashi, musamman ma da suka san yanada yara yan biyu kuma har sun girma sun fara masa aiki.
   Dama Yan biyu sunada shiga rai balle mata, haka wasu designers suka rinka ɗinka masu riguna da jaka amma labarin da Baffa yaji yasa ya hanasu.
     Shima kamar yadda Momee ta share su haka yayi masu, bayan sun gaisa saiya ɗaura girar sama dana kasa babu yan wasa da dariyar daya saba masu.
      Haka suke cin zaman su kowa ya kama harkan gabansa, kuma ɗan Lunch da Momee ke siya a office ta kirasu suci ta daina.
    Idan kuma ana présentation Momee ta rinka auna masu tambayoyi kenan ta rikita su, kuma koda wasa suka ce mata Momee a office zata juya a hasalce tace, ‘Yes Ma zakuce ba Momee ba”
        Su suna tunanin dawowan Baffa zasu ji dama dama amma ashe ba anan gizo ke sak’a ba saboda duk kanwan ja ce.
   Gashi bai kawo masu maganar ba balle su bashi hak’uri, zaman gidan ya bala’in isarsu. Ji sukeyi kamar suna gidan yari.
     Gwanda Nawwarah takan kira Deenie yazo suje strawberry gardens su shakata. Morar soyayya sukayi babu kama hannun yaro.
    Suna kashe ma juna kuɗi yadda ya dace, ita dama Nawwarah akwai san bubuɗawa. Hakan nan zata shiga Online tayi masa shopping kamar su agogo ko takalmi kokuma belt duk masu ɗankarin tsada.
   Shima ba tayar baya ba wajen kyauta saboda saiya aika mata su turaruka seti seti kuma last week haka ya aika mata wani akwati pink na customise. A saman an rubuta ‘Pinky’ kuma ciki yanada kusurwa daban daban nasu agogo, kayan kwalliya, zobe, yan kunne, yan hanci, vandana, Tiara kuma komai pink ne.
     Ita kam Nuwairah sau ɗaya ta ganshi tun bayan daya hamɓareta a ciki. Shima taje Deenie Clinics ne wajen Dr Amrah ranar Laraba kamar yadda aka mayar mata session ɗinta.
   Ta fito kenan sai gashi zashi office ɗinsa, kallon kallo sukayi na wajen seconds talatin. Murmushi ta soma masa saboda har yanzu sanshi yana nan daram a zuciyarta, shine first love ɗinta kuma bata tunanin zatayi saurin mantawa dashi.
      Watsa mata harara yayi saiya doka tsaki sannan ya tafi, runtse ido tayi saboda taji ɗacin abun, Itadai tana kyautata zaton shine mijinta saboda tana jinsa a cikin ranta, jijiyanta, k'albinta da duk ilahirin halittan ta.
     Haka ta koma Office tunda dama daga nan ta fito, tana isa sai taga Nawaz a Parking lot yayi tagumi.
    Zuwa tayi wajen ta tsaya, anan ne ma taga idonsa yayi ja dab da hawaye, “boss lafiya na ganka haka”
     Dagowa yayi ya kalleta, “auren dole za’ayi min da girmana Fisabillilahi, kuma abin haushi shine inada wanda nake so”
   Anan Nuwairah ta ɗan ji daɗi saboda ba ita kadai ke wahala da soyayya ba, jingina tayi sosai a motar Nawaz tace, “Toh meya hanaka auren wanda kake so?”
   “Wallahi yanzu haka idan na dauki waya zan kirata sai kiga na shagala, ko kofar gidansu naje haka zan gama tsayuwata amma bana iya katabus”
      Abin ya bama Nuwairah dariya, sai kace an haɗa abu da aljanu. Tunda Nuwairah bawai tasan yana san Mermer bane, saiya tambayeta yaushe rabon data ganta.
   Anan tace tun wajen bikin Husna,  rabon dasuyi ido hudu.
     “Haba tana kawarki shine bakije dubata ba” yace, mamakin kalman Nawaz tayi saboda Mermer bawai kawarta bane haka. Tanada girman kai da raini sosai gatada da takama a matsayinta na yar sarauta.
     Amma tunda yayi magana bari taje ta dubata kafin ta wuce gida anan tabar Nawaz taje cikin Office.
   
    Barakallahu.....

      Ama Yan Mata sai hada hadan biki akeyi, kudinta na sadaki suka wuce kasuwan Central aka siya su kayan kitchen, an siya tukunya mai guda shida na 12k, sai suka siya cooler guda biyu yan dubu uku uku.
     Sannan aka siya setin cokula na dubu hudu da ɗari biyar. Sai suka siya kwanan tangaran yan dubu uku guda daya saina dubu biyu guda biyu.
     A haka suka gutsurtsura kudin kan ka sani sun cika baro guda da kaya, Ama ta raina kayan amma batada yanda zatayi tunda bata bawa kowa ajiyar kudi ba.
    Suna isa saiga kanwar Yaya mai suna Atine tazo daga kauyensu na Ikara. Anan ta kwance kullin zaninta inda ta fitoda dubu saba’in gudun mawa daga dangi kap.
   Murna Yaya tayi saboda tasan sunyi ɗankarin kokari. Da kudin za’a siya zanin gado, labule da sauran kayan amfani.
   Shikuma Liman siyarda gonarsa yayi na chan jeji saboda ayima Ama gadon yayee tareda gara. Dubu ɗari da ashirin ya bama kafinta yayi mata gado, kujera, durowa da kuma karamin tabur a falo.
    Sai kuma aka siyan mata katifa, buhun semovita sai man gyada 10 litres. Dama a masallaci wani attajiri ya bashi buhu biyu na shinkafa.
     Dayake basuda wadatar kudi yasa bikin karma karma za’ayi a lallaba a cida iyali.
     Ita kuma Gwaggo ta bama Shatu Maman Hassatu kudi akan taje Kano ta siyan masu lefen zamani.
     Akwati hudu da kit kalar toka aka siya mai leda, sai aka zuba atampha yan leda dasu materials da leshi yan madaidaita.
     A takaice tayi mata seti ashirin da bakwai. Komai yaji kowa ya yaba da abinda Shatu ta siya. Dama ita sana’ar ta kenan. Siye da sayarwa.
     Aminan Gwaggo guda biyu da Shatu, da kuma Ikilima yar Nawaz da Hassatu aka kai lefen.
   Ita kam Yaya baki kamar gonar auduga, tara makwabta tayi suna shige da fice, kowa sai san barka yakeyi Ama tayi goshi.
   Itama Ama daga ɗaki tanata murna wai ita ce ke cikin daular nan, koda su Pha’eexah suka zo kallo tayita masu gani gani levels don change tunda ta kece masu zarra..... Wannan kenan!

      Jaɓi Road......

         Wajen karfe hudu da rabi Mallam Musa ya ajiye Nuwairah gaban gidansu Mermer. Katafaren gida ne kuma ya cancanci jin kan da Mermer keyi.
   Fitowa tayi taje bakin gate saita kwankwasa, Ado ne ya leka tareda gaidata.
   Anan tace tanaso taga masu gidan, shi duk zaton sa wajen Bilkisu zata yasa bai wani damu ba.
    Buɗe mata karamin gate yayi saita shiga ciki, tana shiga falon tayi sallama.
   Bilkisu ce ke zaune akan Three seater, sanye take da riga farar T-shirts saita saka irin Bend down select skirt ɗinda ba’a yayensu.
   Girarta as expected tayi layi ɗaya da bakin gazar kuma bakinta yasha lining shima. Kaza tasa aka gasa mata saita tasa a gaba tanata ci. Bakajin karar komai sai k’ururus ɗin kashi datake tauna.
    “Ina wuni?” Nuwairah ta gaidata.
    “Meye? Wa kike nema?”
  Abin yabama Nuwairah mamaki saita dake, “Wajen Mermer nazo”
   Harara ta watsa mata saita ce, “Ke Mamalo ana neman ki”
   Ita kuma Mermer mamaki takeyi saboda batasan da zuwan kowa ba, wanke hannunta tayi daga kullun kamu datake tacewa.
     Tana isa falo ta sandare, idan dai idanta ba gizo yayi mata ba amma ɗaya daga cikin Yan biyu ne a tsaye cikin falonsu.
   Itama Nuwairah mutuwar tsaye tayi, da Ace Mermer bata nuna ta santa ba bazata ce wanda ke tsaye itace Mermer ba.
    “ijin dai kin gama tace min kullu na koh?” Bilkisu tace saita lankwasa baki.
      “Yanzu zan gama”
    “Muje na tayaki” Nuwairah tace.
   Da sauri Bilkisu ta mike tsaye ta shiga gaban Nuwairah kamar zata hankadota, “Wallahi bazaki shigan min kitchen ba, sallan kiyi min barbaɗe” ta faɗa tana jijiga.
    “aiba kowa bane irinki” Nuwairah ta amsa saboda kana ganin yanayin gidan kasan an shiga an fita.
     “Malama karki zo gidana kiyi min rashin kunya, yanzu yanzu zan la’anta maki rayuwa”
    “Yi hak’uri Bilkisu bai kai nan ba” Mermer tace.
    Ita kuma Nuwairah zatayi magana Mermer ta toshe mata baki saita ja mata hannu zuwa ɗakinta, daga nan saita koma kitchen ta gama aikinta tsab.
    Koda ta dawo taga Nuwairah zaune akan gado, murmushi sukayi ma juna sai Mermer tace, “Sorry ban ganeki ba”
    “Mene?” ta tambaya a razane.
   “Na sanki mana, ina nufin Nuwairah ko Pinky?”
    “Nuwairah ce”
   “Allah sarki, kinga abinda nake ciki koh? Duniya ya canza min farad ɗaya” saita soma kuka. Janyo ta Nuwairah tayi ta soma buga mata baya.
    “Shhh, ba laifin ki bane. Kowa da nasa jarabtan, in sha Allah zaki fita daga wannan kangi”
     “Wata rana idan Bilkisu tana min abu ina ganin alhakin mutane ke bina, ni karin kaina nasan banida mutunci... Kawai rokon gafarar Allah nakeyi”
    “Karki damu komai zai wuce maki, kuma kiyi hakuri banzo dubaki da wuri ba... Wallahi ɗazu mukayi maganar ki Nawaz”
   Da sauri ta ɗago, kallon Nuwairah tayi saboda an sosa mata inda yake mata kaikayi. “da gaske Nawaz yayi magana ta?”
   “Eh menene? Innalillahi kece wanda yake cewa yana so koh?”
   Runtse ido Mermer tayi tareda gefe dakai, Nuwairah ce ta cigaba da magana. “Sati mai zuwa bikinsa fah, za’ayi masa auren dole”
    “Allah ya sanya alheri” tace saboda koba auren dole zaiyi ba ai yayi kokari da ita. Balle yanda Bilkisu ke gurzanta yanzu tasan bazata bari tayi aure ba.
    Tasan wannan labarin data samu zai hanata barci na kwana bila adadin, saidai kaiwa Allah komai zatayi saboda shine gatanta.
     Magrib aka kira yasa Nuwairah ta tafi, daga nan tayi alkawarin zuwa dubata akai akai. Tambayanta tayi mezata zo mata dashi, a sanyaye tace mata Always take so. Shiru Nuwairah tayi, gaskiya Mermer na cikin yanayi amma akwai ranar k'in dillanci watau ranar da babban rigar mai gari ta ɓace.
      tana cikin mota sun nufa hanyar gida sai taga dan kunne wari ɗaya a Jakarta, babu tantama daga zuwa gidansu Mermer yanzu ta sace.... Wannan kenan!
     
      GRA, Lugard Roundabout.....
   Koda TK yayima Hajja Zee maganar haihuwa tace su sauka lafiya, ita bataga amfanin ace da tsufanta tana yawon maternity clinics.
    Kuma tasan kuruciya ke damun Husna, nanda shekara 2 zuwa 3 zata daina. Ita mayar da kanta  akan kasuwancin data keyi saboda yanzu ana damawa da ita a kaduna.
   Kowa yasanta Hajja Zee matar TK. Gata mutumiyar arziki mai daɗin sha’ani.
   Ita Husna tun bayan sun dawo daga asibiti TK ya basar da ita. Bai sake tada zancen ba, jira takeyi suyi magana amma abu ya ci tura.
     Haka har hakurinta ya gaza tayi masa magana, “Nifa ban yarda dasu ba” yace.
    “Bafa abin wuya bane, kawai kwan dake cikin jikinka zasu dauko su saka min, nifa zan raina cikin na haifa abina”
   “Toh shikenan bari mu gwada mu gani”
     Ranar da sukaje aka ɗauki sample daga jikinsa, an kai lab ayi analysing sai bayan kwana biyu inda Husna Zataje a saka mata.
     Dama shi yace bazai rakata ba, yanada business saboda za’a sauke masa tankin mai. Ita bata damu ba saboda yayi mai wuyan ya bada kwan.
    Lubie ce tazo suka tafi asibiti, anan Doctor ke mata bayanin anyi contaminating kwan a cikin lab saboda haka bazai kyankyasu ba.
   Gashi kwai ɗaya TK yakeda, kuma Doctor yace magunguna daya sha a baya ne ya samo masa kwan da kyar saidai bazai iya fita daga cikin jikinsa ba yasa aka ciro.
    Husna Sharara ma Dr mari tayi kuma ta haushi da faɗa, hakuri ya rinka basu akan zai kira Alhaji da kansa. Yaji ya dauka duk matakin da zasu yi masa.
      Da sauri Lubie ta dakatar dashi akan kada ya kuskura ya gayama TK idan ba haka ba da kanta zata saka a kulle shi.
    Janye hannun Husna tayi suka tafi, a mota take faɗa mata sabon Plan.
    “Tunda dai yanzu an gano Alhaji yanada kwai, sai a samo wani wanda zai maki ciki ba tareda sanin TK ba”
       “Ban gane ba Lubie? Da aurena kike so nayi iskanci?
    “Nifa bance haka ba, rana ɗaya zaki bashi kanki musamman idan ovaries ɗinki a buɗe yake”
     “Kina ganin haka zai yiwu kuwa?”
   “ Sosaima, barmin wuka da nama, zankaɗeɗan namiji zan samo maki mai curly hair ya baki tsiron sa, tunda kinada kyau Baza’a gane ba”
    Anan dai tareda daɗin baki kanwar shedan tayi mata famfo tareda karkato da hankalin Husna zuwa abinda takeso, daga bisani har shewa suka somayi da Husna ta lura da gadon da zata  ware dasu duk randa TK ya kwanta dama.
     Basu tsaya ko ina ba sai Kanti Plus sukayo siyayya saboda Husna zata Gwaiba Manor domin gaisheda Momee...... Wannan kenan!






#YGG




DIMPLΣS ce

'Yan Gidan Gwaiba (Completed) Où les histoires vivent. Découvrez maintenant