Twenty-seven

4.2K 282 38
                                    

Amaturahman yarinya ce wajen Mallam Halilu Imam tareda Halima wanda suke cema Yaya.
     Tanada shekaru 19 a duniya yanzu, an haifeta a kaduna a wani unguwa mai suna Barakallahu.
    Maihaifinta Malam Halilu wanda ake cema Liman manomin gona ne kuma shine Limamin layinsu.
      Ama tayi primary a NTI model school saita wuce Day Rigachikun inda tayi Art class. Toh bayan nan bata cigaba da karatu ba saboda babu wanda zai tallaba mata.
    Ko abinci k’arma k’arma sukeyi kafin su samu balle wani karatu.
      Ama ta kasance hazukar yarinyar, daga boko har islamiya. Saukarta uku ta fannin addini kuma ta haddace Alqur’ani mai girma.
     Kullum sanye take da Hijab har kasa da safa, handglooves, nikap. Dayake yar gidan Mallam ne babu wanda yake mamakin shiganta.
     Sun tashi cikin talauci sosai, da chan Yaya tana zuwa scholar cikin makwabta amma tunda kanin Ama mai suna Khalil ya girma shike fita shagon carpenta.
     Yanzu haka babu abinda bai iya ba daga buga net, buga hanger, gyaran gado dasu kujera dasu kuma roofing. Yanzu rayuwarsu yafi nada sosai saboda duk rintsi sai sun kai bakin salatinsu.
     Dayake Baban Nawaz yana zuwa masallacin Liman sallah idan yanata uguwarsu. To tanan shakuwa ya shiga tsakanin su, sanda Nawaz ya samu aiki tun lokacin yana Mail Man Baba ya faɗa ma Liman. Har sanda ya koma makaranta ya fara aiki gadan gadan a office.
    Tun Ama tana shekara 10 idan taje gidansu Nawaz yake burgetabatada babban yaya saita daukeshi a matsayin haka.
     Shikuma yakan bata alewa idan tana wajen kuma ya kawo ma Hassatu, dayake tun wajen yayee taje zaune a gidansu.
    Saida Ama takai wajen Js3 ta gane cewa abinda take ji a ranta gameda Nawaz soyayya ne. Toh tayi kokarin ta gaya masa amma yayi burus da ita.
    Sau da dama tana aika mashi wasika sai ya yaga kafin ya karanta, kuma idan sun haɗu a zaure saita soma masa magana. Da sauri yake barin wajen ko saurarenta baya yi.
       Daga nan saita soma kama kafa wajen Gwaggo, duk bayan kwana biyu tana zuwa tayi mata su scholar da gyaran ɗaki, Nawaz yana ankare da ita kuma yasan danshi takeyi.
    Yanzu burinta ya cika saboda an ɗaura masu aure. Kawayenta ko sallar Magrib basuyi ba suka tafi.
   Pha’eexah ce ta kunna turaren wuta mai kanshi yan Maiduguri, komai ya dauki kamshi sai sukayi mata fatan alheri suka tafi.
    Tashi tayi shiga bayi, wani abu ta gani kamar bindiga sagale a bango, tana daukowa ta danna saiga ruwa ya fito ta bakin. Tasan ba shower bane saboda gashi chan a wajen sama kuma sam batasan abin yin tsarki bane idan mutum ya gama kama ruwa. Haka ta ajiye taje wajen Sink ta daura alwala.
    Nawaz bai dawo ba sai bayan Isha, zulumi yakeyi kawai amma kuma bakin alkalami ya bushe.
   Ama matarsa ne kuma dole ya bata hakkinta daya dace da ita, tasan cewa idan tayi wani munafunci rufe fuska baxai taɓa cewa ta buɗe ba.
    Haka ta bar fuskanta wanda tayi kwalliya irin wanda ta iya tana jiransa a ɗakin da akayi mata jeranta.
   Dakinsa daya gyara yaje, saida yayi safa da marwa wajen sau 10 kafin ya cire hula da babban riga. Da sallama ya shiga ɗakinta.
   Kamar yanda kowane amarya keda kwarjini haka Ama tayi, gashi tayi haske dukda dama fara ce. Umurtan ta yayi akan tayi alwala suyi sallah.
      Raka’a biyu yajasu tareda jero masu addu’a, koda ya gama itama ta jero nata addu’an masu dumbin yawa.
     Daga nan yace taje falo ta dauko fruits dasu yoghurt tareda naman kaza wanda ya siya.
    Bata kai hakanan ba saita taje kitchen taɓare su sannan ta saka a kwano masu kyau.
   Murmushi tayi masa data kawo mashi, shima sai yayi wanda bai kai nata ba.
   Tare sukaci babu wanda yayi magana, itace daga baya tace, “Ya taro?”
   “Lafia lau, ya naki?”
   “Alhamdulillahi
      Bayan sun gama cin abinci ta kwashe kwanonin, koda ta dawo bata ganshi a ɗakin ba. Wani purple night gown ta saka mai riga da wando, tana cikin ɗaura dan kwali saiga Nawaz ya dawo sanye da jallabiya.
     Anan ya kashe masu wuta suka kwanta.

Gwaiba Manor...

    An shirya Passports ɗinsu Nuwairah, Nawwarah, Nafisa da Momee. Zasu fara zuwa Italy sai su wuce Dubai.
   Nuwairah kam har yanzu bata sake jikinta ba, kuka take kwana dashi kuma dashi take tashi. Ita harga Allah tana jin Deenie mijinta ne sai gashi kuma taga akasin haka.
     Rabon dataga YaShehu kusan shekara biyu kenan,shima zata shiga Gidan Gwaiba ne suka ci karon yayinda duka su biyu suna danna waya.
     “Ki gode ma Allah nina fara bugeki da Yanzu yanzu kinci duka” yace saiya wuce.. Toh abinda take tunawa kenan gameda shi. Yanzu wannan mugun zata aura.
     Kuka takeyi saboda tasan rayuwarta yazo karshe, tasan bazata taɓa jin dadin zama a gidan YaShehu. Kawai dai zatayi zaman hakuri tayi ma iyayenta biyayya ne.
      Kullum batada buri idan tana kallon India tayita mafarkin irin rayuwar da sukeyi da mazajensu itama tayi da nata ba. Amma tasan YaShehu wrong spouse da zaiyi wannan ne.
     Sun isa Italy sun soma siyayya babu kama hannun yaro, anan suka siya fabrics ɗin dasu ɗinka sannan akayi masu embroidery dasu stones da crystals, ɗinkin sai sunje Dubai inda personal tailor dinsu zaiyi.
      Sun shiga shagon Kenwood na kitchen utensils, fafur Nawwarah tace Baza’a siyan masu iri ɗaya da Nuwairah. Dukda taso company ɗin amma bakin rai bazai barta ta yarda ba.
   Momee itama tana san products ɗinsu kuma shine take amfani a Gwaiba Manor yasa ma ta shiga shagon, haka akayi ma Nuwairah ordering komai da ake amfani a kitchen.
   Ita kuma Nawwarah shagon Masterchef ta shiga aka siyan mata, China wares iri ɗaya aka siyan masu farare tas.
    Ansha faɗa babu kama hannun yaro, Momee mamakin yadda Nuwairah ke masifa takeyi, ita kam tunda bata samu Deenie ba ta dauki alwashin Nawwarah nace mata kule zata ce chas.
     Sun gurza bala’i kamar zasu ara baki, sunata zage kansu daga tas. Momee ta hanasu amma kamar ingiza su takeyi.
   Sun bama Momee kunya ba kaɗan ba, daɗin abin a wajen ba’a jin hausa data gama jin kunya. Nafisa kanwarsu ta sakasu a gaba sai kallo takeyi.
    A duniya tana jin haushin yadda suke faɗa kamar kaji ko masu ganin hanjin juna. Har cikin ranta bataso ta haifa yan biyu indai haka suke.
      Shikam Shehu Usman ya saka wayanshi a Flight mode, koda Abbansa ya kirashi a waya bai samu ba. Dukda suna gari ɗaya tunda shi Reps ne kuma mon-thur yana Abj sai weekends yana Zaria wajen mutanensa.
    Text ya tura mashi akan ya soma shiri yayi masa mata.
     Wajen 2:30am na dare ya kasa barci, saiya kunna wayarsa tareda cire flight, anan yaga sakon daya firgita shi.
    Da sauri ya sauko daga kan gado ya soma haɗa kayansa, gida zai tafi ya dakatar da maganar kafin ayi nisa. Kuma ko yar uban waye bazai aureta ba tunda baiyi niyya ba.
    Magensa Mai suna Peaches ta shigo, fara kal sai wani tag a wuyanta mai crystals da kuma sunarta akai.
    Ba irin magen da muka saba gani bane na gargajiya, wannan ya siya a England sanda yaje course kuma tun lokacin suna tare.
     Duqawa yayi yana shafata saboda zaiyi kewarta. Haka ya gama haɗa karamin akwati ya tafi. Yaransa mai masa wanki da guga zai cigaba da rainanta har ya dawo.
   Dama yanada spare keys dinsa, shiga motarsa yayi Range Rover Sport ya soma sharara gudu. Lokacin wajen 3:15am.
   Haka ya dauki hanyar Zaria cikin daren saboda shi baya barin abu ta kwana. Dayake dare ne kuma yana gudu kafin 5 ya isa kofar gidansu.
     Saida ya isa ya tuna gangancinsa akan dayaje gidansu na Abj, saidai kuma harda Gwaggo yakeso ya tsayar ma duk abinda ke damunta, federal warning zai bada akan kada a sake magana akan aurensa.
    Idan lokacin yayi da kansa zai masu magana, yana zaune aka kira sallar farko dana biyu. Bottle water dake cikin motarsa ya dauko ya soma alwala, karar gate yaji alamar mutum.
   Shikuma Alhaji Abubakar ya fito zashi masallaci, mutum ya gani kofar gidansa yana alwala. Bai kawo cewa Shehu bane saida yaga kamar motar Shehu a gefe.
    Suna haɗa ido suka gane juna, wata ɗaya kenan da ganin juna, shima saida Mamansa ta takura masa yaje wajenta a Abuja.
     Abba yasan Meya kawo shi, maganar auren ne zaice bayaso amma wannan karon bazai saurare shiba, dama kwanaki chan anso haɗashi da Husna amma ya noke.
     Abba yana zuwa ya sauke mashi mari, “Duk abinda kazo faɗi ka rike abunka bana san ji, wuce muje masallaci
     Shehu shiru yayi yabi sahun Abba, mamaki yake karara wacece wannan wanda yasha mari akanta. Babu haufi kila an ma Abba alkawarin gwamna ne yasa yake rawar kai akanta.
    Bai kawo cewa kila daya daga cikin cousin dinsa za’a haɗa ba, dama sanda aka haɗashi da Husna yace baya san auren zumunci.
     Bayan sun dawo daga sallah ya dauki kayansa ya wuce ɗakinsa, ita kuma Ummansa tana lazimi sanda Abba ya dawo.
    Bayan  ta idar suka gaisa saiya ce mata Shehu yazo, da sauri taje dakinsa, yana jin an shigo yasan Umma ce.
    Murmushi yayi saiya gaisheta, itama ta amsa mashi da fara’a.
   “Usman saukar yaushe?”
  “Yanzu na iso Umma
   “Zuwan nan naka da magana halan kaji labari ne?”
    “Eh”
   “Kayi hakuri babana, dan Allah kada ka tada hankalin ka”
    “Wacece yarinyar?”
  “Nuwairah gidan Baffa Yusuf”
   Bai amsa ba saboda shi baya bambanta tsakanin su, ko kallo basu isheshi ba. Yasan dai sunada suna wanda ba a fiye ji a gari ba.
    “Babana kayi hak’uri dan Allah, kaji
   “Toh babu komai, kona ki wannan za’a samo min wata gwara nayi na huta
   “Yauwa Allah yayi maka albarka, bari naje na samo maka abinci
    Daga nan ta fice, shi kawai tunani ɗaya yakeyi. Idan an yi auren tamkar ba’a yiba saboda kowa zaman kansa zai rinka yi.... Wannan kenan!
     
     Husna kam bayan ta kashe arna da Goje Scofield, burinta kawai yanzu ace tanada ciki, koda ta isa gida wanka tayi.
    Daga nan ta fito falo, zama sukayi suna taɓa hira da Hajja Zee. Wayanta yayi ruri a lokacin, sunar Lubie taga ya fito.
Nan ta tashi ta shiga ɗaki domin su zanta.
    “Dama yanzu nakeso na kiraki?”
    “Toh gani bani labari nasha, injin dai komai ya kankama?”
    “Sosai ma kuwa, da farko ina dari dari amma sai kawai na cire kunya
    Dariya Lubna ta bushe dashi, “Kai Kawata bakida dama, ai yanzu kwantar da hankalinki. Idan bayan kwana biyu kikaga bakida ciki dole ku koma ku sake, yanzu for the main time zakice ma TK ba’a gama dubawa a Lab ba”
    “Dama mana, sai kace wawiya. Yanzu zan samu fada sosai da cikin nan kuma na tsula tsiya na san rai”
   “Dama abinda nake neman maki kenan, yancinki!! Haba mufa lagosians ne babu gwagwar mayar da bamu gani ba”
    “Ai kam tunda ba yawan gini nazo ɗirgawa Kaduna ba, dole na samu rabona wlhHusna tace tana dariya. Gashi ta harde kafa ɗaya kan ɗaya tana wani karkada su.
   “Dama mana tunda babu irin ginin da babu a Lagos, yanzu haka ki kwantar da hankalinki tunda dama zuwa Jibi idan bakonki na wata bai zoba sai ki gane komai ya kankama. Nima zan kira Goje na gode masa
    “Toh shikenan Lubie Nagode sosai da duka taimakon da kike min, bari zan kira ki anjima naji muryan TK ya dawo”
    Daga nan suka kashe...... Wannan kenan!





#YGG


     fans ɗin YGG naga duka sakon ku, kowa yace ina son Nawwarah da Deenie, im sorry that I led you on but favourite character ɗina Itace Nuwairah sai Kuma Shehu Usman from the future.... Lol




DIMPLΣS CE
   
     

'Yan Gidan Gwaiba (Completed) Where stories live. Discover now