"Ina jinki," Alamin ya faɗa ba tare da ya kalleta ba, gabaki daya hankalinsa yana kan Jasmine da ta dauko yankan pancake ta kawo masa daidai bakinsa. Ajiyar zuciya Nadia ta saki tare da sunkuyar da Kanta  kasa dan sam bazata iya cigaba da kallonsu a haka ba. "Daman so nake na biku Germany idan zaku tafi ni ma na dubo jikin Abba,"

Sai a lokacin Alamin ya juyo ya kalleta yace "That's fine, gobe zamu tafi sai ki shirya around 3pm zamu tashi."

Kakalo murmushi tayi tace "Alright, nagode," sannan ta mike da sauri tace "Na tafi," cikin hanzari ta fita daga suite din saboda kar kukan da take dannewa ya subuce mata a gaban Jasmine.

Tana fita Jasmine ta kalli Alamin suka hada ido sai suka tuntsure da dariya a tare, sunfi minti daya suna dariya da sun kalli juna sai dariyar ta sake kubuce masu, da kyar Jasmine ta tsayar da da dariya ta tace "She really loves you M,"

"What makes you say that?" Alamin ya tambayeta yana kokarin tsayar da tasa dariyar.

Murmushi kawai Jasmine tayi tace "Nothing," sannan ta mike daga kan cinyarasa.

"Ina zaki?" Yayi saurin tambayar ta.

"To get ready for the day," ta bashi amsa tare da yin hanyar kafar benen da ke cikin suite din su. Murmushi kawai ya bita da shi har ta bace masa da gani.

Jasmine tana fitowa daga bandaki ta tarar da Alamin a zaune akan kujera sanye da sababin kaya da alama bayan ta shiga Wanka shima wankan yayi a daya dakin. Ganin bai dago kasa daga kan wayar da ke hannunsa ba yasa Jasmine ta bata rai, takowa ta tayi har inda yake ta leka cikin wayar tasa taga hotunanta yake kalla, wayanda ma bata san sanda ya dauke su ba dan, har da wanda tana bacci ya dauke shi "Oh My God, yaushe ka dauki wannan hoton?" ta tambayeshi tana kokarin karbar wayar da ke hannunsa, amma kafin ta kai ga karba ya kasha wayarsa ya dago yana kallonta "Yesterday, lokacin da kikai bacci?"

Turbune fuska Jasmine tayi tace "Gaskiya ni dai ka bani na goge hoton nan banyi kyau ba, ka rasa sanda zaka yi min hoto sai ina bacci."

Mikewa Alamin yayi yana dariya yace "I don't think so love, beside ni hoton yayi min kyau, you look cute when you sleep."

Bata rai Jasmine tayi ta buga kafar ta a kasa kamar wata karamar yarinya ta chuno baki tace "To bani na sake ganin hoton,"

Dariya Alamin ya fara yi ya daga hannunsa sama tare da wayar a ciki yace "No matter how cute you look Love, bazan baki ba, ina son hoton."
Daga gira daya Jasmine tayi "Really?" ta tambaya tana kallon idanunsa, murmushi tayi ganin ya zuba mata idanu yana kallonta irin ko me za ta yi ba zai bata ba. A hankali tace "That sounds like a challenge," 

Shiru yayi bai bata amsa ba, hakan yasa tayi murmushin ta masa kusa da shi. Dan yatsanta daya tasa akan fuskarsa tana ja a hankali kamar mai tafiyar tsusa har izuwa wuyansa, sannan ta saki sauran yatsunta ta janyo shi a hankali yadda zai yi daidai da tsayinta. Bakinta takai dai dai kunnensa ta sumbata a hankali sannan ta fara magana muryarta a sanyaye tamkar mai rairai waka cike da yanga ta fara cewa "I...I.... Lo...vee...Love.."  tare da daukan lokaci kafin ta karasa da "PIZZA," cikin sauri ta janye jikinta daga nasa tana dariya.

Wani irin kallo Alamin yayi mata yana murmushi, hannunsa ya kalla yaga babu wayar a ciki, bai san lokacin da ta karba ba dan gabaki daya hankalinsa baya jikinsa lokacin da take masa magana.

"Mema kake cewa dazu?" Jasmine ta tambaye shi tare da daga wayarsa da take hannunta tana girgizata.

Bude baki yayi zai yi magana sai kuma dariya ta kubuce masa ya sunkuyar da kansa, yana dagowa yayo kanta da gudu. Dan karamin ihu Jasmine tayi kafin ta taka a guje.

Jasmine Baturiyya ceМесто, где живут истории. Откройте их для себя