Hafsah chan take wuni Asibitin,Da Rana kuma Asibi ta koma Gida ta Huta Da Daddare kuma Hafsah ta koma Gida ita kuma Tazo ta kwana da Hadizan,Kwananta Hudu a Asibitin aka sallameta ta koma Gida Har kuma Tsawon wannan kwanakin Hafsah ko Sau Daya bata Kira Abdullahi ba Shima bai Kirata ba,Saboda ta Dau Fushi Dashi Sosai,Shima sai ya Kyaleta kawai Yana ganin taso ta bata ma kanta ne rai ne kawai.

Washegari Sai ga su Mama da Inna Abu,sun zo wuni sukayi sai Bayan La'asar suka Tafi Bayan Mama tayo mata Yaji Inna Abu kuma tazo mata da Kubewa da Kuka,Sai Zogale Bushasshiya,Sai Sakon Abdullahi Turamen Atamfa Biyu da Rigunan yara Biyu sai Sabulan wanka da klin wanda Kudin ya bama Mama ita kuma tayi Siyayyah ta kawoma Hadizan Anty Hadiza nata Godiya Matuka da alherinsu Da zasu Tafi ta Hadasu da Direba Tace ya kaisu har Zaria.

Hafsah tasha Mamakin ganin Sakon Abdullahi,wato Shima Fushi yake da ita kenan, Kuma da gasken yake Baiyi Niyyar bata komai ba Aranar sai Ranar da yayi Niyya kenan Tana jin Anty Hadizan na Fadama Mijinta Sakon Mijin Hafsah ne,bata nuna mata ba Tana Tunanin kila ta san da Sakon alhalin ita bata san komai ba kuma bata Fadama kowa Abunda ya Faru Tsakaninsu ba sai kawai tayi Fuska Ta Nuna ma Anty Hadizan tasan komai saboda karta gane akwai matsala Ita Hadizan ma Bata da Lura ne ammh yaci ace ta Fahimci ko Waya basu yi.

Ana Gobe suna Iyalin Gidan Baba Mustapha ne,suka zo Ranar suna kuma sai ga Subai"atu da Jidda,Mariya kuma bata samu Zuwa ba sun Fara pratical a Asibiti,sai Umman Saddiq Datazo kwananta Daya a zaria suka Wuto Tare,Kwana sukayi sai washegari suka Koma,Anyi suna Lafiya an tashi lafiya an ci an sha mai kyau Raguna Uku aka yanka da katon Sa Yara sunci Sunan Abdulwaseen da Abdulaseem,Hakika Dangin Mijin Hafsah sun ma Hafsah kara Sosai sunzo kuma sun aiko da Abun arziiki,Umman Sadiq da Turamanta Biyu harda kudi 5k Shiyasa da zasu tafi,Itama ta Hada musu komai na Suna,Ta aika ma Mama Turmin zani da Inna Abu sai Umman Sadiq wacce Ta karba Dakyar,Ita kuma Hafsah sai bayan Suna da kwana Biyu ta Dawo chan ta bar Inna Asibi Sai Anty Hadiza tayi Sati Biyu kana Zata Dawo.

Koda La"asar tayi Tana Cikin Gidanta,Agajiye ta Dawo Shiyasa bata Fara ma wani aiki ba,Ammi ta Kira tace mata ta Dawo daman Ammi ke ta matsa mata ya kamata ta Dawo Gidan Mijinta,Dayake Abdullahi jiya yaje Shida Nazifi suka mata Barka ita da Daddy sun Dade sai da sukaci abinci kana suka musu sallama suka tafi,Bata iya Tsinana komai ba sai Bayan da Ta iddar da sallar Mangariba Kana ta Shiga Kitchen ta Sulala Taliya Dama Tazo da miya Daga kano,Tana gamawa ta Shiga wanka Bayan ta Fito ta saka Wasu Riga da sikat yan kanti ta yane kanta da Vail din gyale,Tana gama Shiryawa Ana Kiran Sallar Isha"i sai kawai ta Shinfida sallaya ta Tada salla Tana idarwa Ta Dauko wayarta ta Fito Falo ta Zauna ta Kira Auwal tace In ya tashi Daga Shago ya biyo ta Gidanta zata bashi sako yace mata yau ma bai je shago ba Yana Hanya ne zai Dawo daga makaranta ya tsaya yin wani abu ne yasa yakai Dare.

Kafin Auwal yazo tatashi ta Zuba Abincin Cikin wasu kololinta masu kyau Umman Sadiq ta sama Abinci Tunda tana nan bata Tafi ba tana Jiran Bikin Autan Goggo Habiba da za"ayi nan da kwana goma,Dayake  batazo da yara ba,Ko Zahra gida ta barta saboda makaranta,tazo da Nama da yawa Shima ta Diban ma Umman Sadiq din da Mama sai Atamfofi Guda Biyu Cikin wanda Anty Hadiza ta bata Bayan kuma Dinkunan da tayi musu Na Fitar suna Kala uku Dataso ta hada harda wanda Zata karama Umman Sadiq sai kuma Tabari sai Umman tazo ta bata.

Ba Dadewa sai ga Auwal yazo nan yaci abincin Shima Suna Hira sai wajen goma Saura yamata Sallama ta bashi Sakon Turaman kuma tace ya bama Mariya Daya Jidda Daya,Sauran kuma tace yakaima Mama,Ta hadamai da 1k tace yayi kudin Mota ya Rike Sauran Dayake ko Kudin da Daddy ya bata bata taba baGashi kuma Anty Hadizan ta kara mata 10k da zata Dawo.

Auwal yana Zuwa Gidan Mama yaga Ya Abdullahi achan ganinsa da kaya Niki Niki yasa Mama ke Tambayansa Daga Ina yace Daga Gidan Ya Abdullahi,nan ya mikama Mama da Umman Sadiq sakon Anty Hafsah,sai Sakon su Mariya Tsalle suka kama da Murna,Ya Abdullahi na gefe yayi kamar bai ji su ba,Mama ta karba Tana gani tana ta Godiya Umman Sadiq ma Tana ta Tayasu Godiya Mama ta Bude baki tace"Kai Wlh Hafsah da iyayenta Mutanen kwarai ne...Kinga da zamu Taho Abunda ta bamu Nama Dayawa kuma gawani Hafsah ta karo mana Bayan Danyen da Ammi ta aiko mana Jiya.."

MASIFAFFAN NAMIJI..!Where stories live. Discover now