Sunyi zaman mintuna Talatin kana Subai ta kalli Hafsah tana Fadin"Muyi Harama ko..?12 ta wuce kada muyi Dare Bisa Hanya.."Tafada tana mikewa Lokaci Daya tana Gyara zaman Saleem Dake Hannunta,suma Duk sai suka mike suna Fadin"Ai kuwa Toh sakina mu zamu wuce.."Cewar Hafsah sai Lokacin Sakina ta ijiye wayarta tana Fadin"Tun yanzu..?

Hafsah tace"Muna Bisa Hanya ne..Zaria zamu koma.."Sakina tace'Ai nagode..Ku gaida gida Allah kiyaye Hanya mungode.."Subai ce tace"Toh in yaya Nazifin ya dawo sai agayamai mun zo..Allah kara lafiya.."Sakinar ta karba da Ameen Fuskarta ba Fara"a Sosai iyakarta Rakiyarsu bakin kofar Falonta ta koma Subai bata Samu Bakin mgana ba sai da suka Dauki Hanya kana ta kalli Hafsah Tana Fadin"Gaskiya matar nan ta Ya Nazifi bata da Kirki..Duk Fadin Rashin kirkinta dasu Zakiyyah ke Fadi ban yarda ba sai yau Dana ganta.."

Hafsah tayi Dariya tana Fadin"Wai ina Ruwanki da Rashin Kirkinta..? Matar nan kin Cika gulma.."Subai tace'"Allah ba Zencen gulma ba sai gaskiya Shiyasa ba"a son Dogon Buri,kinga da Lokacin da zai yi Aure yabi yadda Sunna ta koyar mai addini da Tarbiya Shi kuma sai yabi Mai kyan Diri da kuma Tarin Dukiya Shiysa Tunda yayi Aure yake ta kwarewa kamar kudin Guzuri.."Dariya ta kama Mariya da Hafsah suka kyakyalce da Dariya Jidda dai Tabe kawai Tayi Dayake ita ke gidan Gaba.

Mariya ce tace"Haka ake ta Gulma a anguwa ana Fadin Auran kudi yayi Gashi kuma ya Auro ma kansa wacce tafi karfinsa kwanaki Mama naji suna mganar da Ya Abdullahi Da suka samu matsala ya Taba marinta ta koma Gida Babanta ya Kira Baba wada yace wlh sai yamaka ya Nazifi a kotu Baba wada yace Abun bai kai nan ba,Ya Kira ya Abdullahi yace maza ya Raka Shi Ya Nazifin  suje suyi ban Hakuri wanda ya jawo Ruwa ya Dakesa Shi kadai da Mutumcinsa bazai bari Nazifi ya maidashi Mutumin banza ba.."

Salati Subai ta saka ta na mamaki kafin tayi mgana Hafsah tace"kwarai kuwa Kwanaki sunje kano..Shida Abban Amira ammh kusan Halin yayanku Wlh ko Tadin bai taba yi Dani ba.."Mariya tace"Tabdijam Wake jin Zence abakin Ya Abdullahi in banda Mama..? Ko nima Ranar bai san ina Ciki bane Ina ma Mama gyaran Daki Dana Fito muka Hada ido kinga Ruwan Harara..?Dariya suka sakamata Lokaci Daya Subai tace"Da farko Haushinsa nakeji ina mai Allah kara ammh yanzu ya koma Bani Tsausayi Wlh inda ina da Diya Budurwa sai na wanketa na bashu Naga yarda Shegiya zata kare sai taje ta Rungumi aikinta Ubanta kuma sai ya maye mata Gurbin Nazifin..'

Hafsah ta Rike baki Tana Fadin"Lalle lamarin Babba ne..Ai bata baci ba ga Muhsina sai ya Jirata in ta kara Girma muyi Tuwona maina.."Duka Subai ta Daka mata abaya Tana Dariya Mariya na Tayasu Jidda kuma daman bata Cika saka musu baki ba in suna mgana Inna Talatu kuma taji sanyin A.C mota Tuni Barci ya saceta,Mariya ce ke Tayasu Da Dariya Dayake ita akwai manyance,Bus stop suka ijiye Mariya ta Hau adaidaita ta koma Bayan sunyi Sallama nan suka Barta tana neman Abun hawa.

Suna Tafe suna Hira gwanin Sha"awa Suna gabda Shigowa Zaria Subai tace"Jidda wai yaushe ne,Bikin autar Goggo Habiba ne..? Jidda tace"Wlh na manta ammh fa an kusa kamar naji Mama suna mgana da ita datazo mata Barkan Anty Zannira Tace watan Gobe ne.."Hafsah tace"Kai Abun har yazo..kamar fa Shekara aka saka ko..?

Subai tace"Eh mana nima nayi mamaki..Komai aka sakama Lokaci sai yazo lalle kice Danja zatayi Diban baki.."Hafsah tace"Aifa..Allah dai ya kaimu.."Jiddaa tace"Kafin na Madina din wannan Asabar din Diyar mijinta na Aure fa Shiyasa ma Tace ma Mama bazata samu zuwa Kaduna ba Tadai Kira Anty Zanniran ta mata barka.."Hafsah tace"Allah sarki..yakamata kuma ama Goggo kara kowani Sha"ani Da ita da ya"yanta akeyi.."

Subai tace"Sai Ya Abdullahi ya wakilataki kije Qawata.."Hafsah tace"Wa..? Rufamin Asiri ina Lallaba yan kayana yanzu ma Baku san Abunda zan Tarar ba na Tsiya.."Ta fada tana Dariya Dayake ta basu labarin yadda ya Barta ta Taho Tunda Ranar da sukazo da Daddare Umman Sadiq ta Kirata tana Tambayanta ko ya Kirata yace tatafi sai tace gatama akaduna.

Basu iso Zaria ba sai Wajen Biyu na Rana Dayake basu yi Gudu ba Gidan Mama Tawagar Sunan ta yada Zango suka bama Mama sakonta ita kuma tayi ta Hamdalan Sun dawo lafiya daya suka baro masu wanka sukace Lafiyarsu kalau suna gaisheta Dama koda suka iso Mama tayi Danwakenta da yajinta da manja nan suka baje sukaci suka Koshi suka Dora da Ruwa kana aka Zauna zaman Hira Bayan sunyi Sallar azahar.

MASIFAFFAN NAMIJI..!Where stories live. Discover now