*ATAƘAICE*

Anyi miki Jesica da angonta Jahal,inda bikin yatara mutane sosai lokacin cikin Jawahir wata bakwai yayinda Juliet take laulayin ciki komi taci sai ra amayar inda Jadida  ko da tasamu ciki saida Jawad ya zubar acewar shi bai tashi haihuwa ba balle yatsufa.

Juliet ko tattali da tattalawa  take samu kamar ƙwai cikin cokali,ji ake yi da ita kamar gold,wata irin kulawa ake bata sabida laulayin da take komi taci sai ta amayar ,hakan yasa Hajiya Kaka tasa ya dawo da ita family house a ɓangaran ta ya ajeta.

Ummie duk da batason Juliet yanda taga tana wahala akan ciki ba ƙaramin tausayinta taji ya shigeta ba,ba abarta a baya wajan kulawa da ita ba  itama.

Jahda ko kamar ta kashe Juliet haka takeji,inta shigo side ɗin Hajiya Jasmin ,bazata taɓa fitowa ba sai ta tabbatar ta wuce.

Awani ɓangare kuma tana jin daɗi komi banza kota window tana hango masoyinta taji sanyi,don ita har yanzun bata haƙura ba sam bata cire rai da samun Jaheer ba a matsayin mijin auran taba ,kullum sai tayi mafarkin ta aure shi.

Bayan wanta tara da ƴan kwanaki,safiyar lahadi inda ta tashi da mugun matsanan cin vowing mara da baya,tun tana cijewa harta fara birgima .

Hajiya Jasmin ta tafi side ɗin Hajiya Mama.

Kamar antsikare ta ta tashi ta dawo tundaga waje take jiya ihun Jahda da sauri ta shiga taga har  tayi mugun gala baita.

Da sauri taje ɓan garan Ummie ta kirata tazo suka temaka mata zuwa asbiti.

Ummie da badon tasan zafin haihuwa ba,kuma sabida Allah da bazata iya temakon Jahda ba.

Saida aka shiga da ita labour room kafin ta kira Dadyn yara da Hajiya Mama ta shaida musu.

Bata jima tana naƙuda ba ta haifo ɗanta ƙato amma baizo da raiba,sai bayan an gyarata akafito musu da yaro lokacin Hajiya  Mamah da Alhaji Jalal,da Juliet da yanzun ta samu ƙwarin jikinta.

*********
Tundaga Monguno suke tafiya suna hira suna Allah-Allah su iso gida su wakanar da aikin da boka yabasu aiki take kamar yankan wuƙa,sunzo dai-dai gadan rigachikum wata motor tirela tahau kansu.

Take Allah ya ɗau ransu,kawunan  su duk yafita  ,ƙafa da hannu duk suncire,mutuwar wulaƙanci.

Take mutane suka fara ɗauka suna ɗaurawa a social network ana cigiyar dangin su.

Daga baya ne aka samu wayar ɗaya amotor kiran number da aka rubuta my son aka kira.

Jahoor da mamaki yau Ammie shi ke kiran shi,ta dena fushin kenan,saura kaɗan ta tsinke ya ɗaga da sallama.

Jin muryan namiji sai da gaban shi ya faɗi.

"Ina mai wayar?.
Ya tambaya a taƙaice.

Mai wayar Allah yai musu cikawa ta hanyar hatsarin motor anan rigachikum,amma bamusan daga insa suka fito ba,yanzun haka suna general hospital kawo,in kuna da dangan taka da ita kuzo".

Innalillahi wainna ilaihi rajun kawai Jahoor ke maimaitawa inda Jawahir tai saurin tashi daga kwancen da tayi kancniyar shi ga ƙaton ciki ta yamutsa face tace,"Honey lafiya".

"AmmieAmmieAmmie na ".

Akiɗime yake magana.

"Miyasami Ammie?.

Ta faɗa cike da tashin hankali itama.

"Ammie ta rasu".

Hankalin ta tashe ta buga wani uban ƙara ta miƙe daga jikin sa.

Jikin shi na rawa ya nemi number Abie yasanar mai,yanemi number Jaheer ya sanar mai,kan ace mi labari ya ishe ko ina.

Nan danan akaje asbiti akai cike-cike aka anshe gawar su.

 A GIDANMU SUKE Labari ne akan Soyayyar arniya da Kuma musulmi Όπου ζουν οι ιστορίες. Ανακάλυψε τώρα