DUKKAN TSANANI page 37

1.4K 125 12
                                    

💋💋💋💋💋💋
*DUKKAN TSANANI*
💋💋💋💋💋💋
            *Na*
*Jeeddah Tijjani*
        *Adam*
*(Jeeddahtulkhair)*

*Follow me on Wattpad @jeeddahtou*

              *37*

Cike da nutsuwa nake taku a hankali kaina a ƙasa har na isa kofar gidan su Rukayya, da sallama na shiga cikin gidan, tun daga uwar daki ta jiyo muryata  da gudu ta taso muka rungume juna muna murna, hannun mu riƙe da na junanmu muka shiga dakin tare da samun guri mu zauna.

Ina umma na tambayeta, faɗa min tayi tana banɗaki tana wanka,
Sannu da xuwa tayi min tare da jawo min flask din abinci gami da cewa.

"Ga abinci ki ci Amaryar malam don na san kin yi kewar girkin umma"
Murmushi nayi "Ai kuwa dai kamar kin sani"
Plate ta janyo ta fara xuba min abincin, kallonta nayi ina murmushi "kada ki zuba abincin nan Rukayya wlh a koshe nake sai da na ci abinci na fito"
Tsayawa tayi da zuba abincin tana hararata "Tunda malam ya shagwaba ki ai dole kice baxa ki ci irin girkin mu ba, lallai Sa'adatu amarci yayi daɗi, to ko bakya so sai kin ci abincin nan"
Cigaba da xuba abincin tayi, sai da ta haɗa komai sannan ta turo min shi gabana.

Cike da kulawa ta dube ni "Sannu da zuwa Amaryar malam kin yi kyau sosai kin canja, kin fi komai a kan xuwan da nayi kwanaki, yaushe rabon da na ganki aminiyata, yau dai wato yaga dama ya bar ki xaki yi zumunci"

Ɗan murmushi nayi wanda sai da hakorana suka bayyana " Hmm ashe fa baki san wainar da ake soyawa ba ko?"

Kallo ta bi ni da shi "Kamar yaya, yi min bayani kawata"
Rausayar da kai nayi "mun rabu da Malam Jibo fa nayi zaton ma kin ji labari don duk xancen ya baxa gari"

"Ban ji ba wlh, ai kin san baxan ji ba tunda bana shiga harkar yan unguwar nan sbd munafuncinsu"

Nayi tsammanin xan ga ɓacin rai a fuskarta sbd aurena ya mutu sai naga ta daka tsalle tana murna " Alhamdulillah Allah ya taimake ki kin yar da kwallon mangwaro kin huta da kuda, wannan masifaffen aure ina ranarsa, ai da naga kin yi kyau kin canja na xaci kyallin amarci ne, ashe kyallin yan matanci ne"

Dariya muka sa gaba dayan mu, a dai-dai lokacin ummansu ta shigo, tun daga nesa take ta buɗe ido, da alama tana son tabbatar da gaskiyar abinda idanunta ke nuna mata ne, da ƙarfi tayi magana tare da ajiye abin wankan da ke hannunta.
"Wa nake gani haka kamar Sa'adatu?"

Murmushi nayi "nice umma ba idonki bane"
Da sauri ta karaso "Sannu da xuwa amarya yau an tuna da mu kenan"

Rukayyah ce tayi saurin cewa "ki daina cewa amarya umma Sa'adatu sun rabu da Malam Jibo Allah ya taimake mu"

Dafe kirji tayi tana salati "Oh amma ban ji daɗi ba mutuwar aure ba tada daɗi ko kadan Allah yasa haka ne yafi alkhairi"

Amsawa muka yi da ameen.
Sai a lokacin nake labartawa Rukayya sanadin rabuwata da shi da irin azabobin da na sha bayan ziyarar da ta kai min, ba ƙaramin farin cikin rabuwa da shi tayi ba, sbd dama tana cikin mutanen da gaba ɗaya basa son tarayyata  da shi.

Tambaya na jefa mata.
"wai kuwa ina izuddeen ne?"
Shiru tayi min tare da tafiya dogon tunani sannan ta dago ta dube ni
"Tun bayan rabuwar ku da shi sau biyu kawai muka taɓa yin waya, sai a wajen abokinsa nake jin labarin cewa ya samu aikin custom yanzu haka yana can yana training"

Ji nayi gaba ɗaya jikina ya mutu, tabbas abinda Adda saratu ta faɗa min na cewa izuddeen yayi min nisa gaskiya ne,  ban iya cewa komai ba sbd halin da na tsinci kaina.

A hankali ta dago da kaina tana dubana "ya naga kamar kin damu Sa'adatu? Na san dole xaki ji ba daɗi na rashin izuddeen, sbd shi ne mutum na farko da ya fara koya miki SO, amma hakan kada ya sanyaya gwiwarki idan har izuddeen rabonki ne xai dawo gare ki, fatana dai ki cigaba da addu'a sai kiga komai ya zo da sauki"

Sauke ajiyar zuciya nayi tare da cewa"Haka ne insha Allah xan cigaba da yi"

Nayi zaman sama da awa biyar a gidan muna ta hirar yaushe gamo da kuma labarin izuddeen, ban tafi ba har sai da nayi magariba, har gida Rukayya ta raka ni.

*********

Malam Jibo ne zaune ya haɗa kai da gwiwa ya rasa me yake masa daɗi a ransa, tun bayan rabuwar su da Sa'adatu bai sake jin wani abu mai suna farin ciki ba, ko abinci ya daina ci kullum tunaninsa ya zai yi ya dawo da ita gidansa, burinsa yana cika zai ɗauke ta ya mayar da ita kauyensu ta cigaba da rayuwa a can.

Ɗaya daga cikin ƴaƴansa ya kira tare da umartarsa ya kira masa ɗaya daga cikin almajiransa, da sauri yaron ya fita ya sanar da shi ya shigo.

Da Sallama ya shiga shagon da malam Jibo ke xaune, tsugunnawa yayi tare da gaida malam din.
Sakin labulen shagon malam Jibo yayi Sannan ya dawo ya xauna yana mai fuskantar sa "wani aiki nake so ka taya ni"
A ladabce ya amsa da "to malam"
Wata farar takarda ya xaro tare da mika masa.
"Ina so kayi min sirrin da Sa'adatu Amaryar da na aura kwanaki, xata dawo wajena da kafafunta, kayi iya bakin kokarinka wajen ganin ka mallake min ita ta dawo gidan nan ko tana so ko bata so, nima ina nan xan bada himma wajen yin wani, na raba aikin ne sbd abin namu yayi sauri"

Tashi kaje, daga yanxu nake so ka fara aiki, nan da jibi kuma nake son ganin sakamako.

Jikin sa na rawa ya tashi yana fita malam Jibo ya bushe da wata dariya yana mai cewa "Da kafarki xaki zo kina neman gafara Sa'adatu indai ni ne na isheki riga da wando har da yar ciki"

Comment nd share

*Jeeddahtulkhair😘*

DUKKAN TSANANI Where stories live. Discover now