DUKKAN TSANANI page 57

1.4K 129 12
                                    

💋💋💋💋💋💋
*DUKKAN TSANANI*
💋💋💋💋💋💋
           *Na*
*Jeeddah Tijjani*
        *Adam*
*(Jeeddahtulkhair)*

*Follow me on Wattpad @jeeddahtou*

              *57*

Washe gari da safe bayan nayi wanka na kammala aikina, Innah ta kira ni a waya tace tana son ganina, ba don raina yaso ba haka na shirya na tafi gidan, tun lokacin da Baba yayi min korar kare gidan ya fice min a raina, ko kaɗan ban son abinda xai sa naje, nafi so ko ina da bukatar wani abu innata ta kawo min. musamman ma yanzu da su Innah Salamatu suka daɗa zafafa adawar su gare mu, bana so naje a faɗa min abinda xai hana ni bacci, haka dai na shiryar ba don na so ba na tafi, sai da na fara biyawa ta wajen Rukayya sbd ta raka ni.

Tun daga soro nake jiyo haniyar jama'ar gidan, wannan ya tabbatar min da cewa dukansu suna tattare a tsakar gida suna gulma.

Cikin siririyar muryar mu mara hayaniya ballantana hargowa muka yi sallama, saurin sunkuyar da kaina nayi sbd wani irin kallo suke bi na da shi kamar basu taɓa ganina ba, babu wanda ya iya amsa mana sallamar mu, sai kallon mamaki da suke min, ko kala na canja musu oho.

Innah Salamatu da su A'isha duk suna wajen, wani kallo A'isha da zaliha suka watsa min gami da yin gefe da kawunan su, a ladabce muka tsugunna har ƙasa muka gaida innah, kamar dole haka ta amsa, ragowar matan gidan kuwa babu wacce ta amsa min, har yanzu dai kallon sama da ƙasa suke yi min gami da tabe baki kamar zasu yi min magana sai kuma suka fasa.

Tsaki suka sakar mana gaba ɗayan su gami da buga mana harara, a wannan karon lamarin su bai bani haushi ba sai ma dariya da naji na ƙoƙarin fito min, juya bayan mu kenan naji A'isha na magana.
"Innah wannan fa don taga xata auri mai kuɗi ne shi yasa ta fara jiji da kai, da bamu san asalin mutum bane sai yayi mana girman kai, Allah yasa dai mun san daga gidan ƙasa mutum ya fito kuma da gero aka raine shi"

Juyowa nayi kawai na kalleta tare da sakin siririn murmushi, wannan murmushin da nayi ba ƙaramin 'kona musu rai yayi ba.

Nan fa suka fara habaici har da xagi ta inda suke shiga ba ta nan suke fita ba.

Sake kallon innarta tayi.
"Nima fa innah nayi wani sabon saurayi mai kuɗi mai ilimi kuma sananne ne a cikin unguwar nan, yace a sati biyu xai fito ya aure ni, akwatuna hamsin ma yace xai min, ba irin na wannan yar matsiyatan ba"
Ta karasa maganar tare da galla min harara.

Da sauri ta dubeta tare da rungumeta
"Alhamdulillah Allah ya share min hawayena shi yasa nake sonki A'isha kina da kishi sosai, gara dai ki kankaro mana mutuncin mu, ko don waɗanda basu gaji arxiki ba su daina yi mana kallon yan iska"

Ta ƙarasa maganar tare da mi'kewa tana daɗa janyota jikinta.

Kallon kallo kawai muke yi da Rukayya mamakin wannan muguwar dabi'ar tasu muke yi, a cikin maganganun da suke yi xaka fuskanci akwai tsantsar hassada da baƙin ciki, don haka bamu saurare su ba, shirun da muka yi ma ƙara musu wani baƙin cikin ya yi.

Kai tsaye dakin Innah muka shiga, cike da farin ciki ta tarbe mu, taji daɗin ganina a dakinta don tun lokacin da aka fitar da ni zuwa gidan malam jibo bata sake ganina a dakin ba, wajen zama muka samu tare da gaisawa da ita.

Gefen cinyarta na samu na kwanta.
"Oh!! Yaushe rabona da dakin nan har na manta, ta ƙarfin tsiya dai sai da aka so raba ni da ke Innah"

A kunyace ta ture kaina
"Ke dai ban san lokacin da xaki girma ba Sa'adatu ba ki da burin da ya wuce ki haye min cinya kamar wata yarinyar goye"

'Bata fuska nayi
"Haba innata yaushe rabon da na hau cinyar ki, a lalace fa na kusa Shekara, ko bakya farin ciki da ganina ne na tashi na tafi wajen Addata, dama na fuskanci ta fi ji da ni"

DUKKAN TSANANI Where stories live. Discover now