DUKKAN TSANANI page 30

1.6K 133 7
                                    

💋💋💋💋💋💋
*DUKKAN TSANANI*
💋💋💋💋💋💋
            *Na*
*Jeeddah Tijjani*
         *Adam*
*(Jeeddahtulkhair)*

*Follow me on Wattpad @jeeddahtou*

*Masu karatu sai kun yi hakuri da ni, baxan rika samun damar typing kullum ba sbd ina xuwa makaranta, na gode da yadda ku ke nuna kaunarku ga wannan littafi*

             *30*

Sun yi tsayuwar sama da minti talatin suna tattaunawar sirri, amma babu mai iya jin abinda suke faɗa, sai da suka gama suka shigo dakin da Sa'adatu take, ko sallama basu yi ba suka samu wajen xama suka zauna suna fuskantar likitan, Malam Jibo ne ya fara yin magana "Yanxu dai ina ganin sulhu ya kamata a yi likita bai kamata a ce matata ta samu matsala kuma an barta a nan wajen ba, ina ganin hakan babu maganin da xai yi sai dai ma ya ƙara mata wata cutar, duba da asibiti matattara ce ta shaidanu, kuma ciwon Sa'adatu ba na Asibiti bane maganin gida za a yi mata, don a ganina tana fama da shaidanun da suke hanata jin maganar mijinta, tunda mun gano hakan, to a bani sallama mu tafi gida tunda ina da taimakon da nake bayarwa, kaga ya kamata a bani ita mu tafi kasancewar matar nan mallakina ce, ko musulunci ya yarda na kafa mata doka ta bi, ga kuma mahaifinta ya bani damar yin dukkan abinda naso a kanta kaga kuwa babu Maganar ta sake xama a nan"

Cikin nutsuwa likatan ya dube shi gami da sakin wani ɗan siririn murmushi "Dadina da kai dawo da hannun agogo baya Malam, yanzu fa aka gama maganar cewa baxa a sallame ta ba har sai ta warke, me yasa kake son tada mana da hankali, idan har da gaske kake kana son matarka ya kamata ka kula da duk wani abu da xai taɓa lafiyarta, dan Allah ku gaggauta fita daga nan sbd bana so ta farka taji hayaniya jikinta ya sake dawowa sabo, tana buƙatar hutu sosai"

Mijin Adda saratu ne ya dubi likitan "ka ma daina haɗa su da Allah tunda sun nuna basa jin kunyar yin abin kunya, mu ma mun shirya yaƙi da su, xamu yi iya bakin kokari wajen ganin basu samu nasara a kanmu ba" nuna malam Jibo da Baban Sa'adatu yayi "ku fita ku bar Wajen nan na riga da na fada muku yanxu Sa'adatu ba taku ba ce har sai ta warke xata dawo hannunku, idan kuma ba haka ba yanxu ku ga hukuma a nan"

Wani kallo malam jibo ya bi shi da shi, xai buɗe baki yayi magana Baban Sa'adatu ya tari numfashinsa "kada ka fara cewa komai idan ka duba xaka ga mutanen nan ba da alheri suke nufin mu ba, tunda kaga muna sa'insa da su akwai abinda suke shirin kulla mana tashi mu tafi, idan sun san wata ai basu san wata ba"

fita suka yi suka bar asibitin zuciyar su cike da baƙin ciki, suna tafe suna tattauna yadda zasu kwato Sa'adatu daga asibitin.

Sai washe gari Sa'adatu ta farfaɗo a hankali ta fara buɗe idanunta tana ambaton Allah, shafa fuskarta Adda saratu tayi tare da yi mata sannu, a hankali ta bude baki tana mata magana "yaushe kika xo Adda saratu, dama ina ta kewarki malam ya hana naje na ganki" murmushi tayi "Da bai bari kinxo wajena ba ai gashi ni naxo ko?"
Yunkurin tashi daga kwanciyar da tayi ta fara yi amma sai ta kasa, a hankali Adda saratu ta dagota tare da jinginata a jikin gadon, a hankali ta sake buɗe ido "Nan kuma ina muka xo Adda"?
Cike da kulawa ta bata amsa "Asibiti aka kawo ki"
Zaro ido tayi tare da gyara zaman da tayi "Asibiti kuma Adda ya aka yi malam ya bari aka kawo ni amma nayi mamaki sosai"
Rausayar da kai tayi"ai dole kiyi mamaki idan kinga tagagarin da muka yi kafin ma ya bar ni na shiga gidanki xaki yi mamaki, ke dai labari sai kin warke kawai"

Suna cikin hirar likitan ya shigo hannunshi riƙe da magunguna, guri ya samu ya xauna yana duban Sa'adatu "lallai jiki yayi kyau matar malam Allah ya ƙara lafiya"

"A hankali ta amsa da "ameen"
Mayar da kallonsa yayi xuwa ga Adda saratu "Hajiya akwai maganganun da nake so mu yi da ke, Hakan yana da matuƙar muhimmanci ga rayuwar yarinyar nan, idan babu damuwa ki same Ni a waje"
Cike da nutsuwa ta dube shi tare da cewa, "to ba matsala"
Tashi tayi ta bi bayansa. Waje suka samu suka tsaya, kallonta yayi tare da neman izinin fara magana, cike da kulawa tace masa
"Ina saurarenka"
"Kiyi hakuri da tambayar da xan miki yanxu, abin ne ya d'aure min kai ina bukatar na san amsar tambayar da xan miki"

DUKKAN TSANANI Where stories live. Discover now