DUKKAN TSANANI page 53

1.3K 107 9
                                    

💋💋💋💋💋💋
*DUKKAN TSANANI*
💋💋💋💋💋💋
           *Na*
*Jeeddah Tijjani*
        *Adam*
*(Jeeddahtulkhair)*

*Follow me on Wattpad @Jeeddahtou*

*Happy birthday to you Yaya Hayat wishing you long life and prosperity 🍡🎂🧁*

              *53*

Kwance nake bisa gadona ina jujjuya wayata, ba komai nake jira ba sai shigowar text ko wayar izuddeen yau da tunaninsa na tashi, ƙara kallon wayar nayi tare da sakin murmushi ina tuna yanayin da nake samun kaina a duk lokacin da naji muryarsa.

A dai-dai lokacin ne Adda ta shigo dakina, ɗan dukan kafata tayi a hankali na waigo na kalleta tare da yin murmushi kaɗan.

"Sannu da shigowa Adda"
Ƙarasa mi'kewa nayi tare da xama kusa da ita.

"Yauwa Sa'adatu, da fatan kin tashi lafiya"

Amsa mata nayi da "lafiya lau"
Sake mayar da kallonta tayi gare ni.

"Yanxun nan Babanki ya kira Abban su ihsan, yace xai zo yanxu sai kiyi sauri ki shirya kada yazo ya jira ki"

A xabure na dubeta.
"Me kuma zai zo yace Adda?? Har ga Allah ban san zuwan Baba gidan nan, kin san dai ba...."

Dakatar da ni tayi
"Ki kwantar da hankalinki kuma ki kyautata xato, babu abinda xai faru insha Allah"

Haɗa kai nayi da gwiwa ina tunani, Allah yasa dai ba xuwa xai yi ya rusa maganar aurena da izuddeen ba.
Komawa nayi na kwanta tare da ajiye wayata a gefe guda, ringing ta hau yi ina dubawa naga number izuddeen din, Amma fargaba sai ta hana ni ɗagawa sbd ban san me xai faɗa min ba, sai da yayi min missed calls 5 ban ɗauka ba, haka ya hakura ya kyale ni.

Shigowar text din shi naji, a hankali na kai hannu na buɗe wayar.
*_A lokacin da kika yi nesa da ni, a wannan lokacin nake fahimtar yadda zafin soyayya yake, a wannan lokacin nake ƙara tabbatarwa da kaina, irin matsanancin son da nake yi miki. Kada ki guje ni masoyiyata, idan na rasa ki, babu shakka zan iya rasa rayuwata, ina sonki da fatan gimbiyata ta tashi lafiya, kixo ina kofar gida ina jiranki_*

Wata ajiyar zuciya na saki tare da lumshe idanuna, sake mayar da kallona nayi kan wayar ina ƙara karanta kalaman da ya rubuto min, izuddeen kwararre ne wajen iya magana da kulawa da zuciyar 'ya mace wannan yasa a kullum nake ƙara narkewa cikin kaunarsa.

A hankali na tashi na sanya hijabina na fita.
Yau ma tsaye na tarar da shi jikin motar shi, hannun shi rike da mukullayen shi yana karkadawa.

Cike da nutsuwa na tako har na karaso wajensa.
sauke ajiyar zuciya yayi wacce take nuna tsantsar farin cikin sake ganina.

"My bride" ya faɗa tare da sauke kyawawan idanunsa a kaina.

Saurin kawar da kaina nayi, yau haka kawai na tsinci kaina a tsananin jin kunyar shi, gaba ɗaya ko amsa maganar shi na kasa yi ballantana na samu damar gaida shi.

Cigaba yayi da kallona yana murmushi.
"Yau kuma yan kunya ne a kanki Sa'adatu naga ko gaishe ni kin kasa yi"

A hankali na d'aga bakina nace.
"Ina wuni"
Ban yi tunanin yaji ba sbd yadda nayi maganar a sanyaye kuma muryata ƙasa ƙasa.

Lumshe kyawawan idanuwan shi yayi yana faɗin
"Tabarakallah"
Tare da sauke kyakkyawan murmushi a kan fuskata.

Duk da kasancewar Sa'adatu bata da kyau na a zo a gani amma tana da baiwar dauke hankalin namiji. Muryata ta Musamman ce mai kashe jiki, sannan tana da matuƙar kyan diri, da wannan baiwar tata take sace zuciyar maxaje da yawa.

Sake mayar da kaina ƙasa nayi ina wasa da yatsuna, haka kawai yau ban son wannan kallon nashi gaba ɗaya yake kashe min gabobin jikina.

"Da fatan kaxo lafiya" na faɗa tare da cigaba da abinda nake yi.

Amsa min yayi da "lafiya lau"
Gyara tsayuwa yayi
"My bride sallama naxo mu yi"

Da sauri na d'ago tare da ware idanuna
"Sallama kuma, wace irin sallama?"
babu abinda ya fado xuciyata sai abinda Adda ta faɗa min daxu, game da xuwan Baba, ko dai tunanina ne ya tabbata.

Katse min tunani yayi da maganar shi.
"Ya naga kamar kin firgita amaryata"

Girgiza kaina nayi alamar ba komai.

Ɗan tamke fuska yayi yana gyara kwantaccen gashin fuskar sa.

"Zan je Lagos ne akwai wani aiki na gaggawa da zan yi, shi ne na xo faɗa miki amma baxan dade ba kwana uku kacal xan yi, kin san baxan iya yin nisa da ke ba"

Sauke ajiyar zuciya nayi, tare da kallonsa idanuna sun yi rau-rau kamar xasu kawo hawaye, xan yi masa magana sai kuma na kasa, sbd mayataccen kallon da yake bi na da shi wanda yake min barazanar faduwa, ya fahimci a tsarge nake amma ya kasa daina bi na da kallo.

Cikin sanyin Murya ya dube ni.

"Menene ya bata miki rai my wife, har yake kokarin saka min ke kuka?"

A shagwabe nace
"Baka faɗa min xaka yi tafiya ba sai yanzu"

Kwantar da murya yayi, cikin wani salo yace.
"Nafi so sai naxo na faɗa miki, sbd ko ranki ya ɓaci na rarrashe ki, kin san ni nafi can-canta na rarrashi matata a kan kowa, ko kaɗan ban san ganin damuwa a saman fuskarki, kiyi hakuri baxan dade ba xan dawo gare ki, amma idan baki amince da tafiyar ba sai na hakura na dawo mu xauna tare"

A hankali na d'ago
"Na amince Allah ya dawo da kai lafiya"

Amsa min yayi da "Ameen"
Buɗe mota yayi ya dakko leda ya miko min.
"Ga wannan naki ne amma kada ki bude sai kin je gida"

Karba nayi tare da godiya har sai da yaga shiga ta gida Sannan yaja motar shi ya tafi.

Komawa ta gida kenan ko kayan da aka bani ban buɗe ba, naji sallamar Baba, jikina na rawa na shiga dakin Adda na fada mata yaxo.

Tabarma na bawa ihsan taje ta shimfida masa tare da faɗa masa cewa ina xuwa.

Fargaba ce ta cika xuciyata sbd ban san abinda ya kawo shi ba, alkhairi ne ko akasin haka?.

Sai da na gabatar da addu'o'ina sannan na fita zuwa gare shi.

Mamakin yadda ya canja min lokaci ɗaya nake yi, kamar ba shi ne baban da yaƙi jinana ba a da, ya kore ni daga gidan sa, ya yanke duk wata alaƙa ta ɗa da mahaifi tsakanina da shi.

Sannu da xuwa nake masa cikin sakin fuska yace
"Yauwa Sa'adatu yar albarka sannunki, ya gida ya Addar taki?"

Kaina a sunkuye na amsa.
"Da suna lafiya Baba ya innah da yan uwana"

"Duk suna lafiya Sa'adatu"

Gyara xama yayi tare da gyaran murya.
"Abinda yasa na kira ki, kuma na tako da kaina wajen ki, naxo ne na tambaye ki game da yaron da ya zo gurina a kan maganar aurenki, na san kin san da maganar shi kuma ya faɗa min yana xuwa hira ko?"

A hankali na girgixa kai alamar "eh"

Cigaba yayi da magana "Alhamdulillah haka nake son ji, iyayensa sun xo sun yi min magana a kan xasu kawo kayan auren ki, shi ne naxo na tambaye ki idan kin amince bana so naxo nayi abinda xai kawo miki matsala a rayuwar ki, amma ni a ɓangarena na amince ki aure shi sbd yaron mutumin kirki ne kuma iyayensa mutane ne na gari"

Shiru nayi ban iya bashi amsa ba, sai dai ya lura da ina son izuddeen.
Cigaba yayi da magana.
"Na fahimci komai Sa'adatu tashi kije xan ce kin amince Allah ya sanya alkhairi Allah ya bada xaman lafiya"

Kaina a ƙasa har na shige cikin gida sbd kunyar shi da nake ji.

Dakin Adda na shiga na bata labarin yadda muka yi, ita kanta tayi mamakin yadda ya canja dare ɗaya kayan da aka bani na nuna mata, fito da shi ta shiga yi, kayan kwalliya ne kala-kala da kayan saka, ba ƙaramin kuɗi izuddeen ya kashe min ba. Godiya tayi masa tare da ajiye kayan a wajenta.

*Jeeddahtulkhair😘*

DUKKAN TSANANI Where stories live. Discover now