DUKKAN TSANANI page 56

1.4K 124 8
                                    

💋💋💋💋💋💋
*DUKKAN TSANANI*
💋💋💋💋💋💋
            *Na*
*Jeeddah Tijjani*
         *Adam*
*(Jeeddahtulkhair)*

*Follow me on Wattpad @jeeddahtou*

            
              *56*

Zaune nake bisa kujera ina wanke kwanunkan da muka bata, yau ni kadai ce a gidan duk kaɗaici ya dame ni ya'yan Adda duk sun tafi islamiyya, sauri nake na ƙarasa abinda nake yi na tafi wajen Rukayya, mu yi hirar mu ta xumunci, farin ciki ne lullube da zuciyata sbd na san izuddeen ya kusa zama mallakina har abada, sallamar da Adda tayi ne ya dawo da ni daga duniyar tunanin da na tafi.

Tun kafin ta karaso take min murmushi "Amarya kin yi goshi, kinga abin arxikin da aka zubo miki kuwa? Abin dai sai wanda ya gani, kaya kamar ba da kuɗi yake siyan su ba, gaskiya yaron nan yana sonki da yawa"

Ta faɗa tare da karaso wa kusa da ni gami da cire mayafin da ke jikinta gefena ta samu ta xauna.
Cikin jin kunya nayi mata sannu da xuwa, ban nemi jin abubuwa da aka zuba min ba, sbd na san ina yin magana Adda xata ce ba ni da kunya, shi yasa na mayar da hankalina wajen aikina.

Sake yi min magana tayi.
"Baki ce komai ba Sa'adatu, ko alkunya kike min?"

A hankali nace
"To me xan ce Adda!?"
Murmushi tayi
"Yau dai kin ga damar yin shiru ne amma da sai kin tambayi komai da komai, tunda kin ji kunyata bari na faɗa miki, akwatu ashirin da hudu ya kawo miki, kuma kowacce cike take da kaya, har da sarkar gwal ya saka"

Da sauri na dafe kirjina.
"Ashirin da hudu kuma Adda? Gaskiya kayan sun min yawa ya xan yi da su"

Murmushi tayi
"Arziki da wadata ne yasa ya kawo miki, da ai bai miki ba da ba shi da shi, amma yanxu tunda yayi miki ai ba laifi bane sai ki godewa Allah, tare da fatan Allah ya baki ikon yi masa biyayya, domin izuddeen ɗan halak ne ya haifu, kinga kuwa ya cancanci kiyi masa komai matuƙar bai saɓa dokar Allah ba"

Kaina a ƙasa na amsa mata da "haka ne Adda"

Tashi tayi xata shiga daki.
"Yaushe xaki je gidan naku kiga kayan arzikin da aka yi miki"

Manyan idanuwana na xaro
"Haba dai Adda so kike innah salamatu ta saka ni a bakin duniya"

Siririyar dariya ta saki
"Kamar kuwa kin san yanxu a cikin jin haushin ki suke, kamar ke kika bawa kanki, sun manta Allah ne ke yin komai, kuma wannan hassadar baxa tasa su yi gaba ba, sai dai su yi baya"

Tana gama maganar ta shige dakinta.
Dama na san dole su ji baƙin cikin alkhairin da ya same ni, ni kaina ban yi xaton samun hakan ba ina kuma ga su, da suka ji abin babu zato ba tsammani dole su shiga damuwa.

Ƙarar da wayata tayi ne yasa ni saurin kai hannu wajenta, bakuwar number na gani da har baxan ɗauka ba sbd bana son d'aga number da ban sani ba, tashi nayi na shiga daki tare da kara wayar a kunnena cikin siririyar muryata nayi sallama.

Amsa min aka yi da
"Wa alaikumussalam"

Na so na gane Muryar mai maganar amma sbd an makale murya sai na kasa fahimtar mai maganar, kafin nace komai an sake yin magana.

"Malam Jibo ke magana, Sa'adatu ce ko?"
Ya karasa maganar tare da sakin siririyar dariya.

Bata fuska nayi gami da turo baki kamar mai maganar yana kallona na san ba kowa bane illa izuddeen.

"Babyna yau kuma kaine ka koma malam Jibo? Tabdi ashe kuwa zan fasa auren nan sbd baxan auri kaxamin ango ba"

Da sauri ya zare idanunshi tare da saita wayar a kunnun shi
"Sorry Babyna baxan sake ba, a yafe min"
Ya faɗa tare da tsugunnawa a ƙasa kamar tana ganin shi.

DUKKAN TSANANI Where stories live. Discover now