DUKKAN TSANANI page 24

1.4K 110 2
                                    

💋💋💋💋💋💋
*DUKKAN TSANANI*
💋💋💋💋💋💋
            *Na*
*Jeeddah Tijjani*
         *Adam*
*(Jeeddahtulkhair)*

*Follow me on Wattpad @jeeddahtou*

              *24*

Yau kusan satina biyu a gidan malam Jibo har na fara canjawa daga kamannina na Sa'adatu xuwa wani sunan daban, saboda tsabar wahalar da nake girba na girki da aiyukan gida, kusan girkin mutum talatin nake yi a duk ranar girkina, sannan kuma babu mai taya ni ko iza wuta duk da cewa gidan akwai yan matan da xasu iya taimaka min da wani abun, gani ba gwanar iya tuka tuwo ba haka dai na daure na koya, wata rana yayi kyau wani kokacin kuma ba yabo ba fallasa, ko xan mutu da aiki babu mai taimaka min sai dai idan na gama a xo ci karshe ma yaran gidan su yi min rashin kunya haka nake kyale su ba tare da na tanka musu ba, abinda yasa bana damuwa da abinda suke min sbd nasan insha Allah xamana ba mai tabbata bane a gida.
Taimako ɗaya Allah yayi min duk tsayin satukan da na shafe a gidan malam Jibo, Allah bai bashi damar cimma burinsa na sanina a 'ya mace ba, sai dai mu sha kokawa ya gaji ya kyale ni.

Da yake yau ba a dakina yake ba shi yasa bani damar samun isasshen bacci, don matuƙar yana dakina ba ni da kwanciyar hankalin kwantawa nayi bacci kamar kowa, sbd fargabar kada ya min illa ina bacci, tun bayan da nayi sallar asuba ban farka ba sai wajen sha biyu don ko karyawa ban yi ba, tashi nayi a hankali na nufi banɗaki ina isa wajen naji wani wari na tasowa a daddafe na kwara ruwa na ɗan wanke shi sbd baxan iya amfani da shi a haka.
Zan shiga kenan naji ana min magana waiwayar da xan yi naga uwar gidan Malam Jibo ce a tsaye tana ƙare min kallo, nima kallonta nayi tare da sauraren jin abinda xai fito daga bakinta, sai da ta gama ƙare min kallo tsaf sannan tayi magana.
"Na fuskanci tunda kika shigo gidan nan kike mana gani-gani kin wi fitowa cikinmu ki sake tamkar wacce kike ƙyamar mu da yayanmu, yanxu kin xo shiga banɗaki kin hau toshe hanci kamar waɗanda xamu shafa miki cuta, alhalin mun san gidanku mun san tarihinki gaba ɗaya ke ba yar kowan kowa bace, kamar yadda labari ya tabbatar mana mannawa mijinmu aka yi, idan kinga baxa ki iya hakuri da yadda muke ba, xaki iya tafiya dama mu ba a son ranmu aka dakko mana ragowar karuwanci aka kawo mana gida ba"
Kallonta nayi zuciyata cike da mamakin jin waɗannan kalaman daga gareta, har nayi niyyar mayar mata da martani sai kuma na fasa, sbd bai kamata karya tayi min haushi ba ni kuma rama, kuma ko ba komai akwai banbanci mai yawa tsakanina da ita, wannan yasa na kyaleta na cigaba da abinda nake yi.

Daya daga cikin matan nasa ce ta taso tana mata magana.
"Haba maman biyu wannan abinda kika yi bai kamata ba, kuma zubar da kima ne da mutunci,  kuma ko yanxu kin xubar da girmanki a idonta wanda hakan bai dace da ke ba, tunda yarinyar nan ta shigo gidan nan bata yiwa kowa abinda xata bata masa rai ba kullum kokarin kyautata mana take yi, kuma tsakani da Allah ko mu idan xamu shiga banɗakin nan sai mun wanke sbd mutane ne daban daban suke shigarsa laifi ne don mutum ya tsaftace wajen da xai biya bukatarsa, gaskiya bai kamata ba kuma hakan da kika yi xai bawa yaran mu damar rainata, ko me tayi a baya bai kamata ki goranta mata ba tunda dai Allah ta yiwa ba ke ba kuma idan yaga dama dai yafe mata" jikinta ne yayi sanyi da jin kalaman yar uwar tata na lura duk kunya sai da ta kamata, shiga banɗakin nayi na kyale su tana ci-gaba da yi mata faɗa ni kuwa ko kadan abin bai bata min rai ba sbd na san ban aikata abinda ake zargina da shi ba.

A tsantsame nayi wankan duk ina jin kyankyami, kasancewar masan gidan a cike yake fal da kashi gashi ko murfi basu saka masa ba, ga iyayen kyakyasai da suka mamaye shi abin dai sai wanda ya gani, don kawai bana son kazanta ne amma da baxan iya wanka a wannan banɗakin ba ko don kada na kwashi wata cutar.
Ina gamawa na shiga daki na saka kayana har da hijab kamar dai mai shirin zuwa unguwa, fitowa nayi tsakar gida na shimfida sallayata na zauna kasancewar garin ana ɗan zafi.
Daga soro na jiyo murya kamar ta ya salim, tsayar da hankalina nayi don sauraren muryar mai maganar, a karo na biyu kuwa naji ya ambaci sunana da sauri na tashi na nufi soron
Ina ganin shi wasu hawaye masu xafi suka riƙa xubo min sai naga kamar innata na gani sbd ya salim yana cikin mutanen da suka gwada min so, sai na rasa kukan me nake yi kukan murna ne ko na baƙin cikin halin da nake ciki.

Hankalin shi a tashe ya dube ni "ki daina kuka sa'ar mata kada kisa hankalina ya tashi ziyara na kawo miki domin kiyi farin ciki ba na xama silar sanyaki a damuwa ba, sai da nayi kukana sosai duk lallabanin da yayi bai sa nayi shiru ba sai da nayi mai isata sannan na hakura.
Cikin gida na shiga na dakko masa tabarma kasancewar Malam Jibo baya bari namiji ya shigar masa gida duk kankantarsa, wannan yasa na dakko masa tabarma na shinfida masa.
Waje ya samu zauna muna fuskantar junanmu, tambayar farko da ya fara min shi ne babu abinda yake damuna kuma babu abinda malam Jibo yake min wanda yake kuntata min.?

Nan da nan naji idanuna xasu kawo hawaye amma sai nayi ƙoƙarin shanyewa sbd bana son na d'aga masa hankali girgixa kai nayi alamar babu komai.
Tsare ni yayi da ido yana sake tambayata "ki fada min gaskiya sa'ar mata wane ne zai kalle ki yace babu abinda yake damunki, ko makaho idan ya dube ki zai fahimci akwai damuwa a tattare da ke, dubi fa yadda kika yi baƙi kika rame, sati biyu kacal da aurenki amma duk yanayinki ya canja, kin xama kalar tausayi"

Share guntun hawayen da ke shirin fito min nayi "babu abinda yake damuna sai kewarka kai da innah, sai kuma aikin da nake yawan yi wanda ya fi karfina shi yasa kaga na rame"
A xubure ya dube ni "aikin me kike yi da har yake shirin yi miki illa haka?"

Rausayar da kaina nayi "aikin girki ne na kusan mutum talatin shi yasa kaga na rame"

Kallon tausayawa yake bi na da shi "kiyi hakuri Sa'adatu komai mai wucewa ne wata rana xaki ji dadi har ki bada labarin irin wannan halin da kika shiga"
Sake jefo min tambaya yayi "amma kina samun abinda kike so kina ci ko? dan na sanki sari ba gwanar cin abinci bace kin fi son kiyi ta xama da yunwa, wai ke kada kiyi kiba"
Har sai da ya bani yar dariya.
A takaice na bashi amsa da "bana iya ci" kallon mamaki yake bi na da shi

"bakya iya ci kuma to sbd me, kinga irin halin naki ko"

Kaina a sunkuye nace "Abincin da aka dafa da daddare shi ake ci safe da rana sai wani daren ake sake yin sabon girki shi yasa bana iya ci"

Na lura da ya salim kamar kuka yake son yi amma ya daure, a hankali ya fara min magana "Allah sarki sa'ar mata Allah yana tare da ke kuma zai kawo miki mafita"

Hannu yasa a aljihu ya miko min "karbi wannan duk lokacin da aka yi abinda bakya so ki siya abinci ki ci wannan zaman baxai yiwu a haka ba, sbd Allah ne kaɗai yasan ranar fitar ki daga gidan nan tunda aure rai ne da shi, sai lokacin da Allah ya ƙare shi xai mutu, ki cigaba da hakuri da kuma jajircewa da ibada da addu'a nima xan taya ki"
Gabana ne ya fadi jin yana kiran Allah ne ya san ranar fitata daga gidan Malam Jibo, sai da na ɗan yi nazarin maganar na wasu lokaci sannan naga gaskiya ya faɗa min.
Cike da ladabi nasa hannu na karbi kuɗin tare da cewa "na gode ya salim Allah saka da alkhairi Allah ya bude maka hanyoyin samu, amma fa kaima ba kudi ne da kai ba me yasa ka bani kuɗi masu yawa haka, kada ka karar da yan canjin naka"

Cike da kulawa yake min magana
"duk abinda nayi miki wajibina ne kuma ban yi asara ba Sa'adatu fatana dai Allah ya kawo miki ƙarshen wannan matsalar da kike ciki, insha Allah kuma sai kin ji dadi a rayuwarki, kuma ki kwantar da hankalinki da yardar Allah kin kusa fita daga wannan kurkukun da aka kawo ki"

Wannan kalmar da ya faɗa karaf ta shiga kunnen malam jibo ashe ya dawo ma basu sani ba sai kawai ganinsa suka yi a kansu yana musu masifa.
"Dama kaine munafukin da kake xuwa har gida kana hure mata kunne kada tayi zaman aure da ni ko, shi yasa na rasa duk wani farin ciki daga gareta, take wulakanta ni tare da tozartar da son da nake mata duk gwanintar da xan yiwa yarinyar nan baxan taɓa burgeta ba, to wallahi yau Allah ne kaɗai xai raba ni da kai, har gidanku xan kai ka naji idan kwangila ma ka karbo daga hannun wannan ɗan iskan yaron don kayi sanadin raba aurena da Sa'adatu"

Kafin ya salim yayi magana har ya sheke shi ya fara ƙoƙarin dukansa,
Kokawa suka shiga yi da ya salim, wuyan rigarsa ya kama yana xaginsa shi dai ya salim bai tanka Masa ba sbd yasan mutuncin na gaba da shi, duk abinda ya faɗa masa sai dai ya bi shi da kallo kawai.

Gidan su Sa'adatu suka nufa don gayawa mahaifinta abinda salim din yayi masa.

A yi hakuri ba kullum xaku rika ganin post dina ba sbd wasu dalilai

Kada a manta da comment da share

*Jeeddahtulkhair😘*

DUKKAN TSANANI Where stories live. Discover now