DUKKAN TSANANI page 44

1.4K 156 26
                                    

💋💋💋💋💋💋
*DUKKAN TSANANI*
💋💋💋💋💋💋
           *Na*
*Jeeddah Tijjani*
         *Adam*
*(Jeeddahtulkhair)*

*Follow me on Wattpad @jeeddahtou*

               *44*

'Daya daga cikin kujerun da na ajiye masa ya samu ya xauna yana fuskanta ta, tsananin kunyarsa da kwarjinin sa ne suka kamani, cikin kasalalliyar murya nace "mu'allim barka da dare" kafin ya amsa sai da ya bi ni da wani mayataccen kallo wanda yasa nayi saurin sunkuyar da kaina sannan ya daga baki yace "lafiya lau Sa'adatu" tun daga wannan maganar da nayi ban ƙara cewa komai ba, gyaran murya yayi min har yanzu idanunsa na kaina ya kasa ɗauke idonsa daga kallona, jikina har rawa yake yi ni ban saba da irin wannan kallon ba.

A hankali ya daga bakinsa yace "Na san dole za kiyi mamakin ganina a wajenki kuma a dai-dai wannan lokacin, sbd baki taɓa tsammanin hakan daga gare ni ba" kaina a sunkuye na amsa masa da "eh"

Gyara xama yayi cikin siririyar muryar shi ya cigaba da cewa "Tun bayan lokacin da kika bani labarin irin halin da kika tsinci kanki na kasa samun nutsuwa, hankalina ya tashi naji idan har ban kasance cikin rayuwarki na tallafa miki ba nima baxan iya cigaba da rayuwa mai daɗi ba, da fatan dai dukkan damuwa da fargabar da tsohon mijinki ya sanya ki a ciki kin manta da ita, ina fatan kuma xaki karkade xuciyarki ki manta da labarinsa da dukkan abinda ya shafe shi, ina so ki saki jiki da ni nayi miki sabon dashen farin ciki a rayuwarki, ina fatan dai ban miki shishshigi ba"

Duk maganar da yake yi kaina na sunkuye na kasa magana, kunyar shi ce ta mamaye ni, sake tsare ni yayi da manyan idanunsa yana tambaya ta, "baki ce komai ba Sa'adatu"

A takaice na amsa masa da na amince.

Sake kwantar da muryarsa yayi yace min dago ki kalle ni kiga sakon da ke cikin idanuna, na san shi kaɗai xai baku amsar abinda ke kunshe a cikin zuciyata.

A hankali na dago na kalle shi, Muna haɗa ido ya kashe min kyakkyawan idanunsa gami da sakar min kyakkyawan murmushi, da sauri na sunkuyar da kaina, sbd idanunsa baxa su jure kallon kwayar idanunsa ba, soyayyarsu na gani sosai a cikin su.
Murmushi yayi "me yasa kika yi saurin ɗauke idonki?"

Ban bashi amsa ba sai wasa kawai da nake yi da yatsun hannuna.

Na lura da shi sosai farin ciki ne ya mamaye shi,  fuskarsa a sake ya kuma cewa.

"Me yasa kika yi saurin amincewa da ni Sa'adatu don a kallon da kika min nima naga soyayyata a idonki?"

Sadda kaina nayi ina cigaba wasa da yan yatsuna "na tabbatar da cewa a wajenka ne kaɗai xan samu dukkan abinda na rasa a rayuwata, kana da kyawawan halayen da duk mace da kace kana so dole ne ta karbi soyayyarka, ga ka malami ga ka mai addini uwa uba kuma kai me kyau ne" ina gama fada na sa hannuwa na na rufe idanuna.

Murmushi naji yayi wanda sai da naji sautinsa a kunnena " yanxu wannan duk ni kaɗai Sa'adatu anya baki yi son kai ba kuwa"?

Murmushi nayi tare da girgixa kaina alamar eh, haka muka kasance cikin farin ciki da nishadi sai naji na manta da komai a rayuwata, sbd na shiga wani sabon darasin rayuwa, wanda malaminsa ya kasance kwararre kuma masani a kan aikinsa.

Bai wani dade sosai ba ya tashi xai tafi, sai naji kamar nace ya dawo mu xauna mu cigaba da hira, sbd yadda kalamansa ke bin dukkan wani jini da sassan jikina, amma kuma kunya da nauyinsa da nake ji baxa su bari na fada masa ba, tabbas na san idan na roki wannan alfarmar xai min amma ni din ce baxan iya ba.

Hannu yasa a aljihu ya miko min yar ƙaramar waya kirar Nokia, karbi wannan idan naje gida ina so xa mu yi magana, don ni gaskiya ban gaji da sauraren zazzakar muryarki ba.

Makale kafada nayi alamar ya baxan karba ba, tsare ni yayi da ido ranshi a haɗe yace "Bana so idan na baki abu ki ƙi karba, da ni da ke mun xama abu daya"

Rausayar da kai nayi kamar xan yi kuka "Kada ka bani waya Game ta shagaltar da ni naƙi yi maka hadda ka dake ni" murmushi yayi wanda har sai da fararen hakoransa suka bayyana. "Ki karba ko ana dukan kowa kin san baxan daki gimbiyata ba, kuma ma ai wannan karama ce babu game din da xata ɗauke hankalin ki a ciki, ina so mu rika magana ne na rika jin lafiyar jikin ki" har ga Allah ban so karɓar wayar ba sbd yana amfani da abarsa amma ya ɗauka ya bani, sallama muka yi ya tafi.

Kwasar kujerun nayi na shigar da su gida, a inda na bar Adda a nan wajen na sameta, da gudu na ƙarasa wajenta na faɗa jikinta ina murna.

Kallona tayi tana mamakin yadda na shigo da farin ciki "lallai mu'allim yayi kamu, amma da doctor ne yace zai xo, da baxa a bashi dama ba"

Murmushi nayi kawai ba tare da na bata amsa ba, miƙa mata wayar da ya bani nayi, cikin farin ciki ta karba tana dubawa.

"Wato mu'allim da karfinsa ya faso baxai iya jure rashin jin muryarki ba shi ne har da baki waya to Allah ya riƙe miki Allah ya sanya alkhairi" amsawa nayi da ameen mun dade muna hira sannan kowa ya tafi dakinsa.

Wanka nayi na dauro alwala na saka kayan bacci, mamaki ne ya cika zuciyata ta yaya  mutane hadaddu masu kyau da ilimi, suke rikicewa a kan soyayyata, na san banda ikon Allah babu yadda za a yi mu'allim ya so ni, ya fi ni komai na rayuwa, tunda ni ba wani kyau gare ni ba ya ninka kyauna sau ɗari, amma yanzu ya rikice a kaina da ni kadai yake so yayi rayuwa, gaskiya dole na godewa Allah don ba kowa Allah ya yi wa baiwar da yayi min ba, sai da nayi Sallah raka'a biyu nayi addu'a, ina shirin kwanciya naga kiransa, a hankali na kara wayar a kunnena tare da yin sallama, cikin kasalalliyar murya ya amsa min yana tambaya ta me yasa har yanzu ban yi bacci ba, amsa masa nayi da yanzu nake shirin kwanciya.

Kwantar da muryarsa yayi yana cewa "Ni kuwa kinga tunaninki ya hana ni bacci sai juyi nake yi ni kadai na rasa me ke damuna" rufe fuskata nayi kamar yana ganina ban bashi amsar maganar shi ba, na kawar da tunaninsa muka shiga wata hirar.
Mun ɗauki lokaci muna hira sannan muka yi sallama.

Juyi mu'allim yake yi yana jin wani sanyi da daɗi a ranshi, idan da abinda ya fi so a yanxu bai wuce farin cikin Sa'adatu ba, yarinyar ta riga da ta gama yi masa, yana ji a ransa baxa su ɗauki lokaci mai tsawo suna soyayya ba za a yi maganar auren su.

★★★★★★

Da gari ya waye ma da text message dinsa naci karo, kalamansa na musamman ne, kamar yadda komai nasa yake abin burgewa, sai da na gama komai na tafi makaranta, da naje aji sai na nuna kamar ba shi ne yazo wajena ba jiya, shi ma bai nuna ya sanni ba, yadda yake min a baya haka muka kasance har aka tashi.


Rashin comment dinku da rashin nuna kuna jin daɗin labarin shi ke hana ni yin typing da hana ni yi da yawa, Sannan ina kira ga wadanda suke cikin groups dina dan Allah idan ke ba masoyiyar wannan littafin bace dan Allah ki fita.

*Jeeddahtulkhair😘*

DUKKAN TSANANI Where stories live. Discover now