DUKKAN TSANANI page 21

1.4K 129 12
                                    

💋💋💋💋💋💋
*DUKKAN TSANANI*
💋💋💋💋💋💋
           *Na*
*Jeeddah Tijjani*
        *Adam*
*(Jeeddahtulkhair)*

*Follow me on Wattpad @Jeeddahtou*

             *21*

Sanye yake da wasu kaya marasa fasali, su dai baxa a kira su da manyan kaya ba haka ma baxa a kira su da ƙanana ba, amma kusan surar jikinsa a bayyane yake sbd kayan ba masu kauri bane, kuma da dukkan alamu sun dade basu ga ruwan wanki ba, babu abinda kayan suka yi masa sai ƙara bayyanar masa da asiritaccen muninsa, sai a lokacin na ƙare masa kallo naga ilahirin gashin sa babu baki sai kaɗan amma majority din gashin ya xama furfura.

ina ganin shi nayi karfin halin miƙewa duk da cewa akwai bacci a idona amma hakan bai sa naji kasalar miƙewa ba, a fusace na dube shi.

"lafiya ka shigo min daki a wannan daren, me ya kawo ka me kake nufi da xuwanka a dai-dai wannan lokacin, tun wuri ka fita kafin nayi maka abinda ranka xai ɓaci, na riga da na faɗa maka baxa ka taɓa samuna a matsayin matarka ba ka ƙaddara cewa rainona aka kawo maka, insha Allah sai na kai budurcina gidan izuddeen"

Gyara wuyan rigarsa yayi tare da matsowa inda nake warin jikinsa ne ya daki hancina miƙa hannu yayi xai riko ni, da sauri na bar wajen sbd idan na tsaya xan iya yin amai, cikin tausasa murya ya fara min magana "ki tsaya ki saurare ni Sa'adatu na lura har yanxu kuruciya na damunki, wanda ya samu miji kamata me yasa xaki tafi hangen wani saurayi daban wanda ba shi da niyyar aurenki sai niyyar lalata miki rayuwa, abinda ya kawo ni yanxu naxo ne mu yi sulhu da junanmu, mu kuma bawa juna kulawa da haqqin auratayayya, ina ganin wannan hanyar da muka dakko baxa ta bulle da mu xuwa alkhairi ba, ni da ke ma'aurata ne masu fatan ganin sun zama ɗaya har abada ki bani dama na nuna miki irin yadda nake sonki, da yadda nake jinki a cikin xuciyata"
Wani kallon raini na bi shi da shi "Allah ya kiyaye nayi rayuwar ma'aurata da mutum irinka ina neman tsarin Allah, ka manta irin maganganun da ka fada min a gaban matanka, kai fa ka kira ni da yar iska karuwa wacce aka baka sadakarta, me yasa kuma yanxu ka shigo dakin karuwa baka tsoron na shafa maka cutar HIV ne tunda duk kace na gama bin maxa kafin a haɗa ni da kai, wlh da xaka burge ni da ka sake ni yanxu, don xamana da kai ba mai dorewa bane, duk son da kake min haka wata rana zaka kyale ni na auri wanda nake so"

Kafin na ankara ya dako tsalle ya dawo inda nake, ji nayi ya rungume ni yana sumbatata kokarin dauke numfashi nayi sbd muddin na shaki warin jikinsa xan iya amayar da abinda ke cikina, cikin kalmomi masu taushi ya fara min magana "ki tsaya ki fahimce ni Sa'adatu duk abubuwan da na faɗa miki na faɗa ne a cikin ɓacin rai amma ba don na wukakanta ki na fada ba, na san baxa ki gane girmanki da matsayinki gare ni ba sai a wannan lokacin da xan dandana miki dadin soyayyata, ki bani haqqina kada ki shiga sahun matan da Mala'ikun Allah suke tsinewa"

kokawa muka riƙa yi sosai yana kokarin sai ya zame mayafin da ke jikina da karfin hali na tunkude shi ya faɗa baya, na fita da gudu tsakar gida ina mayar da numfashi.

A gigice ya biyo ni, kallo ɗaya xaka yi masa ka gane yana cikin matsananciyar jaraba komai nasa ya canja, hanyar kofar gida na kama ina ƙoƙarin zare sakata, biyo bayana yayi yana min magana.

"Sa'adatu ina xaki je a wannan tsohon daren yanzu fa karfe biyu da rabi ina hankalinki yake tafiya ne, so kike ki fita kiyi gamo da aljanu"

Kuka na fara yi "ka sake ni wlh bana sonka bana kaunarka ka kyale ni na tafi duk inda naga dama, hakan ne ya fi dacewa da rayuwata, a kan na xauna a wannan kurkukun wlh gara na fita ko duniyar aljanun ne na koma na xauna"
Ina gama faɗa na juya baya ina ta rusa kuka, a yadda nake ji ban ki na fita ba duk abinda zai same ni ya sameni.

Jin shi nayi ya jingina jikinshi a nawa ya hade ni da bangon soron yana sake sumbatata a fusace na juyo na ture shi na wuce dakina da gudu na turo kofa, a daren haka na sha gwagwarmaya da shi duk yadda ya so yaga ya keta alfarmarta ta "ya mace Allah bai bashi dama ba, haka muka sha kokawa a ranar gaba ɗaya ban samu na runtsa ba.

Washe gari da safe da misalin ƙarfe goma sha daya Rukayya taxo min, yan kayan aiki da labule umma ta bata ta kawo min, ina ganinta na rungumeta ina rusa kuka abinda ta fara tambayata shi ne babu abinda malam Jibo yayi min ko da na fada mata yadda muka yi da shi ba ƙaramin dadi taji ba.

Daya daga cikin yaran gidan ne ya shigo hannun shi rike da kwanon abinci sallama yayi tare da ajiye kwanon a gabanmu, abincin karyawa ya kawo min ko da na bude kwanon ido huɗu nayi da tuwon dawa miyar kuka, a take nace ya mayar musu da abincinsu bana ci.

Ina jin matan na yan maganganu a kan rashin cin abincin da ban yi ba ni kuwa hakan bai dame ni ba don ni neman dukkan abinda xai raba ni da gidan nake yi a yanzu ko na huta da jarabawar wannan mugun tsohon.

A yi hakuri da kaɗan abin ne sai a hankali yau da gobe sai Allah

*Jeeddahtulkhair😘*

DUKKAN TSANANI Where stories live. Discover now