DUKKAN TSANANI page 27

1.4K 126 4
                                    

💋💋💋💋💋💋
*DUKKAN TSANANI*
💋💋💋💋💋💋
           *Na*
*Jeeddah Tijjani*
        *Adam*
*(Jeeddahtulkhair)*

*Follow me on Wattpad @jeeddahtou*

*Yan uwa na gode da addu'o'inku Allah ya bar xumunci*

               *27*

Yau tunda innah ta tashi taji jikinta babu daɗi babu komai a zuciyarta sai tunanin Sa'adatu, ji take kamar ta tashi ta tafi gidan nata don taga halin da take ciki, amma kuma sai taji bata son xuwa sbd kada ta janyowa kanta abinda za a zo ana maganganu a kansa, har ta daure ta hakura sai taji baxa ta iya ba, tashi tayi ta nufi ɗakin mahaifin Sa'adatu don ta faɗa masa abinda take ji a ranta, har tasa Ƙafa ta shiga ciki ta juyo sbd ta ganshi tare da innah salamatu suna magana, don haka ta juya don bata son tayi magana a gabanta, juyawarta ke da wuya ya kirata a sanyaye ta dawo ta tsaya tana dubansa, fuskarsa a d'aure yace

"Ya naga kin shigo kuma kin juya lafiya dai ko?" A takaice ta bashi amsa
"Dama magana nake so mu yi kuma naga ba kai kaɗai bane shi yasa na koma"
Bin ta yayi da wani irin kallo "Ban gane ba ni kaɗai bane kina nufin ita Salamatu wata ce daban??"
Kanta a sunkuye tace "Ba haka nake nufi ba, naga ita ma tana magana da kai ne, kaga bai dace na katse muku hirarku ba"
Wani kallo innah salamatu ta watsa mata, mayar da kallonsa yayi ga innah
"Ba wani nan ke dai kawai akwai abinda kike son kullawa don kin ganta ne xaki canja magana, ke dai ki riƙa jin tsoron Allah wlh wannan halin da kika dakko ba halin kirki bane, gashi nan kin koyawa yarki baƙin hali bata kaunar yan uwanta gaba ɗaya, to ni baxan juri wannan abin ba ni bana son gulma da munafunci da raba ɗaya biyu, abinda ya yi ni shi yayi Salamatu duk abinda xaki fada min xaki iya faɗa a gabanta, ke ko baki faɗa ba ma sai na faɗa mata don tana da hakkin da xata san halin da kike ciki ke da yarki, tunda ita ce gaba da ke"
Mayar da ajiyar zuciya innah tayi tare da kallonsu gaba ɗaya, ba tare da tace wani abu ba ta juya  ta kyale su suna mayar da maganar, tana fita aka saka faifan gulamarta cike da makirci innah salamatu ta dube shi kamar xata yi kuka.
"Na rasa me na yiwa matar nan ta tsane ni, kullum burinta taga bayana ni kuwa xama a gidan nan daram don ni taxo ta tarar, mugun halin da yake kunshe a ranta ya fi karfin cikinta, Allah ne yaga niyyarta ya barta a haka, yanxu banda tsabar masifa maganar ce baxa ta faɗa a gabana ba sbd ga munafuka ko, kada na kwasa na gayawa duniya, tunda bata son naji ni kuma wlh sai na san halin da ake ciki, tashi ka bi ta daki kaji me ke tafe da ita"

Da sauri ya miƙe ya shiga dakin innah , yadda taga ya shigo yana tambayarta abinda ya kawota ne ya bata mamaki, hakan ne ya nuna mata cewa ba yin kansa bane aiko shi aka yi, don haka ita ma a takaice take bashi amsar duk abinda ya tambayeta ba tare da ta wani sakar masa fuska sosai ba.
A hankali ta fara yi masa magana "Dama a kan maganar Sa'adatu ne yau na tashi duk jikina ba daɗi banda tunaninta babu abinda nake yi ko aiki na kasa yi, shi ne naga ya dace na tambayeka ina so xan je na ganta, kaga tunda aka yi aurenta ban taɓa zuwa naga muhallin ta ba ballantana na san halin da take ciki"
wani kallo ya bi ta da shi gami da gyara tsayuwa "kinga dakata bana son kinibibi da son iyawa, sai kace a kanki aka fara aurar da 'ya xa kice xaki je ki ganta, duk yan uwanta da suke xuwa su ganta basu wadatar ba sai kin je da kanki dole kin ganta, wato salon kiga wani abin da bai miki ba ki kashe mata aure ko?? To ban yarda ba, kuma idan har kika je ban yafe miki ba, duk abinda kike so a yi mata ki faɗawa Salamatu xata yi miki, don ta fi ki kyakkyawar zuciya kece ma kike nuna mata baƙin hali amma duk abinda kake so xata yi miki"
Sai da ta bari ya kammala magana, cikin nutsuwa ta dube shi "Haba dan Allah malam idan aka yi min haka sam ba a yi min adalci ba, ya zaka yi min Allah ya isa a kan xanje naga halin 'yata ɗaya tilo da na mallaka a duniya, duk abinda Salamatu xata yi min ai ba kamar wanda xan yi da kaina ba, gaskiya ka janye maganar Allah ya isan nan sbd idan aka yi min haka an shiga hakkina tunda kowace mace a gidan nan kana bari tana xuwa gidan yarta ni me yasa zaka yi min haka?"

DUKKAN TSANANI Where stories live. Discover now