DUKKAN TSANANI page 38

1.4K 126 7
                                    

💋💋💋💋💋💋
*DUKKAN TSANANI*
💋💋💋💋💋💋
           *Na*
*Jeeddah Tijjani*
         *Adam*
*(Jeeddahtulkhair)*

*Follow me on Wattpad @jeeddahtou*

              *38*

Sake bushewa yayi da wata irin dariya wadda har sai da ya tuntsura, Allah ne kaɗai ya san irin muguntar da yake shirin kullawa Sa'adatu wani abu zuciyarsa ke hasaso masa matuƙar ya samu Sa'adatu a yanxu shi kaɗai ya san irin garar da xai kwasa, domin ya dade da sanin Sa'adatu tana dauke da baiwa mai yawa, ƙoƙari ɗaya zai yi shi ne yayi duk mai yiwuwa  ta dawo cikin rayuwarsa,  tunanin irin  lugwigwitar da zai yi mata yake yi, saboda ya san dole yanzu yarintar ta taqara fitowa tunda ta samu huta tare da nutsuwa.

Kamar wanda aka zabura ya tashi ya janyo wata adaka da ke ajiye a gefensa, ya fara fito da wasu irin takardu yana ware wanda zai yi amfani da su fuskarsa na ɗauke da murmushin mugunta. Bincike yake yi sosai sai dai har yanxu ya kasa gano wacce xai yi amfani da ita, wacce da ya xuba aiki xai kama Sa'adatu.

Rigingine ya kwanta yana cigaba da dogon tunanin da ya saba.

★★★★★

Salamu alaikum nace sannan na sanya kaina cikin gida. Da murna "Adda saratu ta karɓe nii
Sa'adatu har kin dawo amma kin yi sauri sosai"
Zubewa nayi a ƙasa ina share gumin da ya ɗan taru a fuskata gami da cire hijabin da ke jikina.
"wash Allah wlh na gaji addah ko don na kwana biyu ban yi tafiya ba, ga shi kuma a qafa na taho ban samu abin hawa ba, shi yasa fa bana son fita sbd a gajiye nake dawowa"

Riƙe haba tayi tana kallona
"oh!! ni saratu  Yanzu yar tafiyar nan har kin gaji Sa'adatu, gaskiya ki rage lalaci abinda gidan ba wani nisa ne da shi ba, a ƙafa ma xaki iya zuwa, lallai yaran zamanin nan, idan bakwa motsa jiki wlh xaku tsufa da wuri"

Murmushi nayi ina gyara xama, mikewa nayi xan karbi wukar da take yanka salad na Taya ta aiki dakatar da ni tayi.

"A'a ki bar shi na kusa karasawa, shiga ki samu ruwa a fridge ki sha, baki dade da fita ba suka dawo da wuta"
Amsawa nayi da to Adda, dakko ruwan nayi na dawo muka cigaba da hira.

"Ya kika baro innar Ruqayyah da fatan dai kowa lafiya"

"Suna nan lafiya duk suna gaishe ki sosai ashe wai basu samu labarin abinda ya faru ba, sai da naje nake fada musu, abinda yake bani mamaki Adda babu wanda yake baƙin cikin rabuwata da Malam Jibo kowa murna yake min"

"Ai dole a yi miki murna Sa'adatu Allah ya raba ki da ƙaddara Allah dai ya kyauta ya kare ki daga sharrinsa, abinda nake so da ke yanzu Sa'adatu, ba zama za kiyi ki ta bacci ba, dole mu dage da addu'a don kin san wanan algungumin mutumin ba rabuwa damu zai yi ba, sbd ki san zuciyarsa babu alkhairi Allah ya shige mana gaba ya raba mu da sharrin masu sharri."

Jikina a sanyaye na amsa da "Ameen" tashi nayi na shiga kitchen na kama mata girki, har na fara haɗa miya naji kamar an tsikare ni na fito, daga gefenta na tsaya yana dubanta
"Adda kin ji izuddeen ya tafi training din custom dan Allah Adda ki taimake ni kije gidan su izuddeen ki jiyo min labarinsa"

Sakin wukar da ke hannunta tayi "Ke Sa'adatu ina raba ki da izuddeen din nan har yanxu kin ki karbar shawarata ko, wannan ai Bara a kufai kike yi, tunda kina son mutumin da ya manta da ke a rayuwarsa ya fita daga shirginki, dan Allah ke a tunaninki yanxu me izuddeen xai yi da ke, ai ya wuce ajinki kiyi addu'a Allah ya haɗa ki da wanda ya fi shi, amma kwallafa rai a kanshi ba naki bane"

Hawaye ne suka kwace min baxan iya cire son izuddeen daga raina ba har abada sbd shi ne mutum daya tilo da ya fara koya min soyayya, kuma duk duniya ina ji da shi kadai xan iya rayuwar aure, amma xan yi kokarin bawa xuciyata hakuri kamar yadda tace, kitchen din na koma na cigaba da aikin gabana.

Tun daga wannan ranar na  dage da addu'a tare da kiyamullaili ina gayawa Allah ya kare ni daga sharrin malam jibo ya haɗa ni da dukkan alkhairi idan kuma izuddeen alkhairi ne a gare ni Allah ya tabbatar min, ita kanta Adda saratu tana taya ni wannan dalilin ne ya ƙara min nutsuwa na daina shakkar komai tunda ina gayawa Allah kuma na san xai min maganin matsalata.

Ranar wata Lahadi ina zaune a dakina ina tsifa, Ihsan yar Adda saratu ta shigo da gudunta ta faɗa jikina, rungumeta nayi ina kallon kyakkyawar fuskarta. Cikin siririyar muryata ta fara min magana.

"Aunty saadatu kizo inji Abban mu yana kiranki"
Sauke ta nayi daga jikina na mike
"Kice ina zuwa Ihsan" Hijabina na saka na tafi amsa kiran mijin Addah

Cikin nutsuwa na janye labulen dakin tare da cewa
"Salamu alaikum"
Fuskarsa a sake ya amsa min
"wa alaikumussalm"

Jikin kofar dakin na damu na tsugunna kasancewar dakin Karami ne kuma Adda da sauran yaranta duk suna ciki shi yasa dakin cunkushewa har na rasa wajen da xan xauna.
Cike da kulawa ya dube ni
"Shigo mana Sa'adatu"
A ladabce na shiga na samu kusa da Ihsan na xauna, kaina a sunkuye nace
"Barka da dawo wa Abbah ya kasuwa"

"Alhamdulillah Sa'adatu ya zaman hakuri Allah yayi mana jagora, dama wata shawara muka yi da Auntynki naga yana da kyau ki koma skull saboda zaman a haka ba dadi, kinga yanzu rayuwa ta canza sai kana da ilimi za'a tafi da kai, na samo miki wata makaranta a nan kasan layin mu ta manya ce akwai fannin ilimin boko dana islamiyyah kinga riba biyu kenan, tunda kina da haddar Alkur'ani babu wani abu da xai miki wahala, ina fatan zaki mayar da hankalin ki har muga abinda Allah zai yi a nan gaba"

Wani irin hawayen farin ciki ke bin fuskata tare da wani dadi mara misaltuwa daya mamaye ni, ban taɓa xaton wannan ranar xata riske ni da wuri haka ba, ashe burina zai cika Allah kenan mai yadda yaso, wanda yayi hakuri zai ga ribar hakan, wanda yayi gaggawa kuma xai yi nadama"

Ban san lokacin da na xube ina godiya ba tare da yi masa addu'a, tabbas mijin Adda saratu mutum ne mai karamci da kirki, na dade ban ga mutum irinsa ba, iya xamana a gidan bai taɓa banbanta ni da ya'yansa ba, kuma ko a fuska bai taba nuna min bai son na xauna a gidansa ba, wannan dalilin yasa nima nake girmama shi don yayi min rikon da ko mahaifinta bai min irinsa na.

"Na gode sosai Allah ya kara girma insha Allah bazan baka kunya ba"

Yaji dadin godiyar da nayi masa, cikin sakin fuska yace

"Tashi kije kinji insha Allah gobe zaki fara zuwa Allah yayi miki albarka"

Amsawa nayi da Ameen na fita.

Alhamdulillah Allah kalmar da nayi ta maimaitawa kenan bayan na dawo dakina, ina san karatun sosai musamman na boko amma sbd an fi karfin mu aka danne hakkina ko primary ban yi ba, banda arzikin Alkur'ani da ko Hausa baxan iya karantawa ba, sai ga shi cikin falalar Ubangiji, Allah ya dube ni zan yi karatu kamar kowace diya mace.

Kasa cigaba da tsifar nayi sbd farin ciki, fita nayi naje na dauro alwala nazo na fara jero nafil filun godia ga Allah da ya nuna min wannan rana.



*Jeeddahtulkhair😘*

DUKKAN TSANANI Where stories live. Discover now