DUKKAN TSANANI page 67

1.4K 121 10
                                    

💋💋💋💋💋💋
*DUKKAN TSANANI*
💋💋💋💋💋💋
            *Na*
*Jeeddah Tijjani*
          *Adam*
*(Jeeddahtulkhair)*

*Follow me on Wattpad @Jeeddahtou*

*Kada a manta yan uwa gobe akwai azumin nisfu sha'aban, azumin yana da matukar muhimmanci don haka a daure a yi, wannan dalilin yasa na saki post din gobe a yau sbd bana son rubutuna ya shagaltar da mutane*

               *67*

Satina huɗu a gidan izuddeen Rukayya ta kira ni a waya cewa xata kawo min xiyara, tun safiyar ranar nake murna shi kanshi ya lura da yadda nake xumudin xuwanta, don haka ya siyo min abubuwan da xan bata kyauta, tashi nayi na girka mata nau'ikan abinci kala-kala, kafin ta iso har na dameta da kira sbd ina bukatar ganin ta akwai maganganu da yawa da nake son yi da ita.

Ƙarfe biyu dai-dai ta iso gidana, da gudu na ƙarasa na rungumeta ina farin ciki, wani kallo take bi na da shi.
"Kinga yadda kika canja kika yi kyau kuwa Sa'adatu lallai izuddeen ya iya kiwo"
Gaba ɗaya muka kwashe da dariya.
"Mun iya kiwo dai, nima baki ga yadda na mayar da shi ba har ya fara tumbi"
Murmushi tayi gami da dukan bayana.
"Daga aure kuma sai tumbi tsabar sharri Sa'adatu"
Jan hannunta nayi muka shiga ɗaya daga cikin dakuna na, a kan gado muka xauna muna hirar mu ta aminai, labarin bikinta ta shiga bani, da irin hidimar da doctor yake yi mata, don yanzu zancen da ake yi ma har an kusa kawo kayan lefe, ba ƙaramin murna na taya ta ba, don na san xata samu cikakkiyar kulawa a wajen doctor sbd Mutum ne mai saukin hali, kamar yadda nake samu a wajen izuddeen, bata tafi ba har sai wajen sallar magariba kamar baxa mu rabu ba haka naji a raina, sai da muka haɗa mata sha tara ta arxiki ba ƙaramin dadi taji ba, har bakin gate nayi mata rakiya sannan na dawo.

Kitchen na wuce na shiga haɗa mana abincin da xamu ci da daddare, shi kuma ogan nawa yana daki ban san me yake yi a ciki ba, sai da na kammala na shiga, tarar da shi nayi ya fito daga bathroom d'aure yake da towel yana goge jikin shi, kyakkyawar fatarsa da muradadden jikinsa na lafiyyyen qaqqarfan ɗa namiji ya bayyana, jikinsa sai she'ki yake yi sbd hutun da ya bi fatarsa, gashi ne kwance a kirjinsa, ko kaɗan bai lura da shigowata ba.

Tsayawa yayi gaban mirror yana cigaba da goge jikinsa tare da taje gashin kansa, da kwantaccen sajen da yake ƙara fito masa da ainihin kyawunsa, a hankali na ƙarasa kusa da shi ina sakin siririn murmushi, shaukin son shi da kaunar shi na dokar min xuciyata, ta cikin mirror ya hango ni ina yi masa masa murmushi juyo wa yayi tare da lumshe kyawawan idanunsa, a hankali cikin sigar rikitarwa nasa hannu na fara shafo kwantaccen gashin da ke kirjinsa.
Sake lumshe idonsa yayi yana bi na da wani irin kasalallen kallo tare da bin hannuwana da kallo.

Bai yi tsammani ba yaji hannuna a bayan shi ina shafa shi tare da sabule towel din da ke jikinsa, a hankali ya saki wani shu'umin murmushi tare da kwanto da ni jikinshi, yana shafar duk wata gaba ta jikina.

Haɗa fuskata yayi da tashi, tare da danna kanshi cikin jikina yana shaƙar kamshin turarena, cikin wani salo ya ɗauke ni cak ya dora bisa bed din da ke ɗakin, ya shiga aikin da ya saba a ranar na gane kuskure na domin kuwa ni na fara tsokano shi cikin salo da kwarewa da baiwar da Allah yayi masa ta rikita 'ya mace ya fitar da ni daga hayyacina, sarrafa ni yake ta ko'ina.

Sai da na sarrafu iya sarrafuwa sannan ya dawo cikin nutsuwar shi wanka muka yi, sannan yaja hannuna muka fita zuwa dining.

A baki na riƙa bashi abincin har sai da ya ci ya koshi, juyo da fuskata yayi ya sakar min wani hoto kiss, sannan ya jawo ni jikinshi cikin rad'a yake min magana.
"Kina da baiwa sosai Sa'adatu, baxan gajiya da yi miki hidima ba fatana Allah ya bani abinda xan cigaba da kulawa da ke har ƙarshen rayuwata, amma ni ban hangi wata mace bayan ki ba"

Wani malalacin murmushi na saki tare da sake manna kirjina da nashi.
"Ina jin dadi idan na bude idona naga kaine abokin rayuwata, bana fatan ranar da xan wayi gari na ganni ba tare da kai ba, burina kullum na kasance cikin kulawarka da soyayyarka"

Shafa fuskata yayi
"Har abada baxan taɓa barin ki ba ko mutuwa tare da ke nake so ta ɗauke mu, idan kika tafi kika barni ban san irin halin da xan tsinci kaina ba"
Murmushi nayi tare da kamo hannun shi ina wasa da 'yan yatsun shi.

Juyo da ni yayi yana fuskanta ta, xuba min ido yayi na wasu mintuna sannan ya fara magana.
"Na manta ban faɗa miki ba farin cikina yau saura kwana uku na koma gurin aiki"
Xaro idanu nayi ina shirin sakin kuka, gaba ɗaya na manta izuddeen yana aiki kuma aikin ma ba a cikin garin mu ba, ban san lokacin da kuka ya kufce min ba.

Kwanto da ni yayi yana rarrashina gami da bubbuga bayana.
"Kiyi hakuri babyna baxan dad'e ba xan dawo gare ki, niyyata sai nayi wata biyu xan tafi yanxu ma kiran gaggawa aka yi min shi yasa xan tafi, amma baxan dade ba xan dawo, kuma idan na dawo tare da ke xan tafi, kema kin san baxan iya rayuwa ba tare da ke a jikina ba"

Idanuna cike da hawaye na d'ago na dube shi, cike da shagwaba nace
"Amma ni baxan kwana a gidan nan ba sai dai ka mayar da ni gidan Adda ko wajen innata"

Kwantar da ni yayi a kafadarsa cikin kunnnena yake rad'a min
"Gaskiya babu inda xaki je ki kwana alhalin kina da dakin mijinki, sai dai ki xabi duk yarinyar da kike so tazo ta taya ki kwana ni kuma na yarda xan je na dakko miki ita, idan aka ganki a gida yanzu ai sai mutane su yi tsammanin ko matsala aka samu"

Dagewa nayi sai na tafi gida da kyar ya shawo kaina na hakura na zabi ƴaƴan Adda da ƴaƴan yayarsa su ne xasu zo su taya ni xama.

*Jeeddahtulkhair😘*

DUKKAN TSANANI Where stories live. Discover now