DUKKAN TSANANI page 19

1.6K 131 4
                                    

💋💋💋💋💋💋
*DUKKAN TSANANI*
💋💋💋💋💋💋
            *Na*
*Jeeddah Tijjani*
         *Adam*
*(Jeeddahtulkhair)*

*Follow me on Wattpad @Jeeddahtou*

              *19*

Yau tsayin wuni a daki nake ko tsakar gida ban leko ba, sbd ciwon kai mai tsanani da zazzaɓin da ke damuna, maganar da malam Jibo ya fada min ke min yawo a ƙwaƙwalwata duk da cewa ina addu'a amma ina tsoron sharrinsa, na lura da shi sosai akwai manufar da yake son cimmawa a kaina, ba alkhairi ne ya kawo shi wajena ba, duk kulle-kullen da ake yi a gidanmu ina ji, amma sai naki fitowa sbd kada na haɗu da Baba, sai da na tabbatar ya fita kasuwa Sannan na fito na ɗan yi abinda zan yi na koma.  kwanciya nayi da niyyar na huta sallamar Rukayya ce ta katse min baccin da nake yi, da sauri na tashi na rungumeta fuskata cike da farin cikin ganinta, muryarta a ƙasa take min magana sbd bata son su innah salamatu su san da xuwanta su haɗa mana tuggu a wajen Baba, gurin zama ta samu ta xauna. Tambaya ta jefo min
"Yaushe kika dawo Sa'adatu nayi kewarki sosai kuma na shiga tashin hankali da naji ance kin gudu tunanina kada ki faɗa hannun azzalumai kinga duniyar nan ba amana, tun lokacin ban sake samun nutsuwa ba sai da naji an ce kin dawo, naso naxo tun lokacin da kika dawo amma sbd matsalar gidan nan yasa nayi xamana kada na sa kiyi laifi"
Murmushi nayi wanda ya tsaya a iya hakorana, takaici da baƙin cikin da ke tattare da ni baxai bari nayi murmushi sosai ba.

"Ba fa guduwa nayi ba Rukayya ina gidan Adda saratu can na koma sbd naga cutata ake shirin yi, ya za a yi ina rayuwar birni na koma ƙauye ai ba a yi min adalci ba"

"Ni kaina naji dadin gudun da kika yi, amma daga baya da nayi tunani sai naga rashin dacewar hakan, sbd kada makiya su samu kofar da xasu yi miki sharri, kinga dai irin rayuwar da kike yi, yau zaƙi gobe maɗaci"

Rausayar da kaina nayi idanuna kamar zasu kawo hawaye "indai sharri ne ban ga ranar da xasu daina min ba har sai ranar da Allah ya raba ni da su, yanxu haka ma a tarkonsu nake suna son haɗa ni da malam Jibo kuma ina ganin alamun da wuya ne abin bai tabbata" A razane Rukayya ta miƙe "wannan wane irin zalunci ne da mugun hali, me yasa ake miki haka ne Sa'adatu?? Sai kace ba Baba ne ya haifeki ba innalillahi wa inna ilaihi raji'un Allah ya canja miki da mafi alkhairi Allah ya kawo miki mafita, shi ne kaɗai abinda xan iya cewa dan al'amarin ya wuce lissafina" komawa tayi ta xauna tana min kallo mai cike da tausayawa "wlh sosai nake jin tausayin ki Sa'adatu amma ba komai rayuwa ce duk abinda suka yi dan kansu, ke dai kiyi hakuri kuma ki riƙe Allah dukkan tsanani yana tare da sauki" mun ɗan taɓa hira sosai amma hankalina gaba ɗaya ba a kanta yake ba, yana wani wajen daban kawai tunanina ya zan yi da Malam Jibo, idan nayi tunanin na gudu sai naga hakan ba mafita bace saboda innah xan jefa a wani hali, sannan kuma har ga Allah bana son bijirewa umarni Baba, sbd bana so a zargi innata da laifin da ba nata ba, haka na kasance ina ta sakawa ina kwancewa har lokacin tafiyar Rukayya yayi, iya soro kaɗai na iya rakata sbd dokar da aka kafa min.

Bayan na koma daki Baba ya dawo daga kasuwa ya neme ni xai min faɗa a kan abinda ya faru jiya, duk kiran da yayi min ban amsa ba sai na nuna bacci nake yi, hakan yasa bai samu ganina ba. Ya zauna zai ci abinci kenan naji an aiko wani yaro cewa ana kiransa a waje,  ba tare da bata lokaci ba ya hau wanke hannu ya fita don ganin masu nemansa.

A kofar gida ya tarar da mutanen da ke nemansa, mutane ne dattijai masu kamala da mutunci kowannen su sanye yake da Babbar riga da hula, cikin karamci suka yi masa sallama, fuskarsa a ɗan d'aure ya amsa musu tare da tambayar su dalilin zuwansu ɗaya daga cikinsu ne yayi magana.
"Allah ya gafarta malam magana ce mai muhimmanci ta kawo mu, idan so samu ne mu shiga daga ciki xai ɗan fi sirri saboda idanun mutane"
bai yi musu ba ya kwalawa A'isha kira ta kawo musu babbar tabarma ta baxa musu suka zauna.

Bayan sun gama gaishe gaishen da xasu yi, wani dattijo ya fara masa bayani "mun zo wajenka ne neman wata alfarma  dangane da ɗanmu da yaga yar wajenka Sa'adatu yana so, idan da hali muna so a bamu dama mu fito, yaron bai zo da wasa ba kuma mu ma haka, don da shirinmu muka zo"

DUKKAN TSANANI Where stories live. Discover now