DUKKAN TSANANI page 49

1.3K 115 9
                                    

💋💋💋💋💋💋
*DUKKAN TSANANI*
💋💋💋💋💋💋
           *Na*
*Jeeddah Tijjani*
         *Adam*
*(Jeeddahtulkhair)*

*Follow me on Wattpad @Jeeddahtou*

*Dan Allah masu comment da thanks ko stickers ku riƙe abin ku ba gode, sharhi nake buƙata ba thanks ba, masu sharhi ina jin dadin abinda ku ke yi, ina nan insha Allah xan kira sunayen ku ɗaya bayan ɗaya*

               *49*

Ina shiga ciki na ajiye kayan a gaban Adda, fito da su tayi ta bai wa kowa nasa, ko da aka bani rabona ban iya ci ba sbd damuwar mu'allim ta cika zuciyata, Adda ta lura da damuwar da na shiga kallona kawai tayi ba tare da tace min wani abu ba, wayar da ke hannuna ce tayi ringing, Ina dubawa naga sunan doctor ya fito a hankali na tashi na shiga dakina gami da faɗawa kan gado.

Cikin kasalalliyar muryata da damuwa ta cika ta nayi masa sallama, sai da ya ɗan ja lokaci sannan ya amsa da cewa.
"Wa alaikumussalam amaryata, duk kin sanyaya min jikina ji nake kamar na dawo na cigaba da kasancewa da ke, kinga ko driving din na kasa, kin xama komai nawa Sa'adatu kece wacce nafi buƙata a cikin rayuwata yanzu"

Ya ƙarasa maganar yana kanne idonsa kamar tana ganinsa.

Ɗan gajeran murmushi na saki gami da mi'kewa zaune
"Nima kaine mutumin da nafi bukatar kasancewa da shi a rayuwata, sbd a duk lokacin da na kalle ka xuciyata na min haske naji kamar na bika ka cigaba da kulawa da ni"

Gyara xama yayi tare da ƙara saita wayar a kunnen shi
"Da gaske kike sa'ar mata ko dai na dawo??""

Rufe idona nayi da tafukan hannuna, a shagwabe nace
"A'a kada ka dawo so kake a ce ka xama mijin tace"

Dariya ya fara yi sosai.
"To ai ba laifi bane don na zama tace ni kan tace ne ma, indai a kanki ne a faɗa min komai ma na yarda"

Dan murmushi nayi gami da shafa fuskata.
"To shikenan naji amma dai kada ka dawo ka bari gobe kazo na ganka kuma kafin ka tafi office nake son ganinka"

"Shikenan da girman kujerar ki zan zo ranki ya dade"

Sallama muka yi na kashe wayar.

********

Yau mun kwashe sama da kwana ki uku bama waya da mu'allim, ko na kira shi baya ɗauka makarantar ma ya daina xuwa gaba ɗaya, ga shi ban san inda xanje naji labarinsa ba, tunda babu wanda na sani a unguwar su, a cikin kwana ki ukun nan har na rame na canja sbd nasa damuwar sa a raina, duk da cewa doctor yana kulawa da ni yana bani farin ciki amma hakan bai sa na manta da tunanin mu'allim ba.

A safiyar yau Alhamis na shirya kenan xan tafi gidan su Rukayya na faɗa mata halin da nake ciki naji ƙarar shigowar message ina dubawa naga sunan shi, da har nayi tunanin kada na buɗe na duba sai kuma na danne xuciyata na buɗe.

*_"Da fatan kin wuni lafiya, idan kin bani dama ina so naxo yau za mu yi wata magana, da fatan baza ki juyar da bukatar talakan masoyin ki ba don naga yanxu masu kuɗi ke buɗe miki ido"_*

Mamaki ne ya cika xuciyata da jin wannan kalaman nasa to "me yake nufi da masu kuɗi sun bude min ido?"

Komawa nayi na xame na rungume wayar a kirjina Ina jin radadi da zafin da zuciyata ke min.

Ƙara naji wayar nayi, da sauri na miƙa hannu na ɗauka, number doctor na gani a jiki, gefe na ajiyeta sbd yanzu bana buƙatar jin wata magana nafi so na xauna ni kaɗai nayi nazarin wannan bakar maganar da aka fada min.

A dai-dai wannan lokacin na sake jin ƙarar shigowar message din mu'allim.

"Ki fito ina jiranki idan kuma kika ɗauki lokaci mai tsawo xaki iya nemana ki rasa"

A sanyaye na tashi na shiga wajen Adda na faɗa mata sannan na ɗauki kujera biyu na tafi wajensa.

A soron na tarar da shi ya harde hannun shi a kirjin shi, kallo ɗaya nayi masa na san yana cikin matsanancin tashin hankali, duk yayi baƙi ya rame, abinka da mai manyan maganai idanun shi duk sun faɗa rami, har naxo kusa da shi bai san naxo ba ya tafi duniyar tunani.

A hankali nayi masa sallama, kamar wanda ya farka daga mafarki ya juyo ya kalle ni ba tare da ya amsa sallamar ba sai ma juyar da kan shi yayi gefe ba tare da ya sake kallona ba.

Komawa nayi kusa da shi na sha gaban shi, cikin rawar murya nake cewa.

"Me nayi maka haka mu'allim da kayi min wannan tsanar har baka son ganina, me yasa xaka hukunta ni a kan dalilin da baka tsaya kayi bincike a kansa ba?"

Abin ka da me xuciya a kusa kafin yace wani abu, har hawaye ya cika fuskata ko ta ina.

A gigice ya dube ni
"Kiyi hakuri ki share hawayen ki ba kuka nace kiyi min ba, naxo ne mu fahimci juna wannan kukan da kike yi, shi ya ƙara tabbatar min da kina sona Sa'adatu kiyi hakuri na yafe miki komai ya wuce"

Wani sanyi da farin ciki naji a raina.
Xaunawa yayi a kujerar da na kawo masa yana kallona.

"Bana son xubar hawayen ki, tunda ni kika yiwa laifi na yafe miki, mu kulle wannan maganar mu shiga wani sabon babin"

Murmushi nayi tare da harar shi ƙasa ƙasa
"Sai da ka wahalar min da zuciya sannan xaka ce wani ka yafe"

A hankali ya shafi fuskar shi.
"Nima ai kin wahalar min da tawa xuciyar baki ga yadda na koma bane nayi baki duk na rame"

Murmushi muka yi gaba ɗaya muka shiga hirar yaushe gamo yana bani labarin halin da ya shiga bayan mun yi faɗa, nima labarin na riƙa bashi wani mu yiwa junanmu dariya wani kuma mu zaulayi junanmu.

Muna cikin hirar muka ji tsayuwar wata hadaddiyar mota a kofar gida, tsayawa fadar irin kyan motar ma xai iya zama kauyanci, gaba ɗaya muka bayar da hankalin mu ga masu fitowa daga cikinta.

Me xan gani?? Rukayya ce ke fitowa daga cikinta da gudu ta karaso wajena muka rungume juna muna murna, cikin farin ciki na dubeta.

"Daxu fa har na shirya xan xo gidan ku sai kuma wannan ogan ya tsare ni"

Sai a lokacin ta lura da mu'allim cikin girmamawa suka gaisa.

Sake jefa mata tambaya nayi
"Ke da wa kika zo kuma? kice masa ya shigo mana kin bar shi a mota shi kaɗai ko ba a so mu ganshi ne??"

Murmushin tayi
"Kin san ko ina boyewa kowa kayana ke baxan boye miki ba, da ni da ke abu daya ne"

Dafata nayi tare da cewa
"Haka ne kam kawata"

Kafin mu ƙarasa maganar da muke yi, tuni na cikin motar ya bayyana, sanye yake cikin wata tsadaddiyar shadda milk colour wacce aka yi mata aiki da brown din xare, takalminsa da hularsa duk kalar aikin da ke jikin kayansa ne, kana ganin kalarsa kasan hutu ya bi jikinsa.

Tun daga nesa yake sakar min kyakkyawan murmushinsa wanda ke sanya ni farin ciki a duk lokacin da nayi tozali da kyawawan hakoransa, ban san lokacin da na tafi da gudu ba ina kiran sunansa................

Ko wane ne Wannan saurayi da Sa'adatu ke muradin gani a rayuwarta yau kuma Allah ya haɗa su??

Sai ku biyo ni don jin kowa wane ne shi

*Jeeddahtulkhair😘*

DUKKAN TSANANI Where stories live. Discover now