DUKKAN TSANANI page 48

1.3K 112 5
                                    

💋💋💋💋💋💋
*DUKKAN TSANANI*
💋💋💋💋💋💋
           *Na*
*Jeeddah Tijjani*
        *Adam*
*(Jeeddahtulkhair)*

*follow me on Wattpad @Jeeddahtou*

              *48*

Na ɗauki lokaci mai tsawo ina ta faman rusa kuka ina tausayin kaina ina tausayin mu'allim da halin da na jefa shi, gaba ɗaya kaina ya kulle na rasa me ke min dadi a duniya, Hanan da ke gefena sai bi na take da kallon tausayawa, gami da share min hawayen da ya bata min ilahirin fuskata, na dade ina  jiransa amma bai dawo gare ni ba, Hakan yasa na dai-daita nutsuwata na share hayawena tare da ɗan wanke fuskanta, don kada yan uwana dalibai su gane wani abu ya faru tsakanina da mu'allim.

Ina fito wa na shiga duba ilahirin makarantar ko zan ganshi, amma babu mu'allim babu dalilin sa, hakan ya sanya ni komawa gida don ko na zauna a makarantar ma baxan samu nutsuwar yin karatu ba.

**********

A ɓangaren mu'allim kuwa gida ya wuce don baxai iya cigaba da zama a makarantar ba sbd mawuyacin halin da ya tsinci kansa, bai taɓa tsammanin Sa'adatunsa xata yi masa haka ba, yana zuwa ya faɗa dakinsa, kwanciya yayi rigingine yana xubar da hawaye masu zafi, bai taɓa tsanar soyayya ba irin yau, a zahiri yake Magana.

"Kin cuce ni Sa'adatu dama haka xaki yi min, sai da kika bari marainiyar zuciyata ta saba da ke, wacce bata san komai ba sai soyayyarki yanxu kuma xaki juya mata baya ki yaudare ta, baki kyauta min ba Sa'adatu wlh, kin xalunce ni"

Yana cikin maganar kuka mai ƙarfi ya sarke muryar sa sai a kasan xuciyarsa ya cigaba da maganar. a dai-dai lokacin ne yaji messages suna ta shigowa wayar sa, da sauri ya kai hannu ya ɗauka yana dubawa, sunan Sa'adatu ya gani, wannan dalilin ya sanya shi wurgi wayar gefe guda.

"Ba ki da wata kalma da xaki faɗa min a yanxu na yarda da ke amma kin ha'ince ni, kin riga kin san halina Sa'adatu bana iya hada soyayya da kowane da namiji, ina da tsananin kishin abinda nake so, wannan dalilin yasa bana kula yan mata, yanzu kuma ke da na yarda da ke, shi ne xaki ɓullo min ta wannan hanyar me nayi miki?me nayi miji kika azabtar da ni haka?"
Ya ƙarasa maganar yana cigaba da kuka mai ban tausayi.

Messages din ne dai suka riƙa shigowa ba kakkautawa, a hankali ya kai hannu ya fara buɗewa don ganin abinda ta aiko masa da shi.

*_ka saurare ni mu'allim ka yayyafawa xuciyarka ruwan sanyi ka nutsu kaji abinda xan faɗa maka, kada kaje ka yanke hukunci cikin fushi daga ƙarshe mu zo mu yi nadama, kaima ka san ina sonka baxan taɓa yaudarar ka ba, ka san halina ka san yadda nake sonka, don an bani waya ba shi ne yake nuna aurena mutumin nan xai yi ba, da ka kwantar da hankalin ka a lokacin nake da niyyar maka bayani, amma kuma sai kayi gaggawa, dan Allah ka taimaki zuciyata ka tsaya kayi bincike kada sanadin hakan ya sa mu rasa junanmu_*

Yana gama karantawa ya sauke wata gauruwar ajiyar zuciya sannan ya buɗe sako na biyu

*_Wata rana zaka fahimci irin yadda nake ji a kan ka, zaka fahimci gaskiyar mafarkin da nake yi a kowane dare, sannan kuma zaka gane muhimmancin irin matsanancin son da nake nuna maka a zahiri, amma a lokacin da zai zamo, babu wata sauran dama a tsakanina da kai ina mai baka hakuri a bisa abinda ya faru tsakanina da kai, na gode ina sonka har abada_*

Sake jefar da wayar yayi tare da 'kan'kama hannun shi a kirjin shi yana maimaita.
"Hakuri a kan me? A kan kin cuce ni, kin yaudare ni, kin nuna ni kadai ne a ranki ashe irina muna da yawa a gurinki, hakuri a kan marin xuciyata da kika yi, kika jefata a mawuyacin hali, ko wane irin hakuri kike magana nayi a halin yanxu?

Ya faɗa tare da mi'kewa zaune yana furzar da numfashi mai tsanani zafi, juyawa yayi ya kwanta tare da rungume pillown shi a kirjin shi yana jin wani radadi mai matuƙar xafi a xuciyar shi.

DUKKAN TSANANI Where stories live. Discover now