DUKKAN TSANANI page 35

1.5K 137 3
                                    

💋💋💋💋💋💋
*DUKKAN TSANANI*
💋💋💋💋💋💋
            *Na*
*Jeeddah Tijjani*
        *Adam*
*(Jeeddahtulkhair)*

*Follow me on Wattpad @jeeddahtou*

              *35*

Bayan wajen yayi shiru ana jiran umarnin police ya bada damar tafiya ko tsayawa, mikewa Adda saratu tayi tare da cewa ina da magana, damar yin magana ya bata.
Gyara tsayuwa tayi tana mai fuskantar mutanen da ke wajen.
"Ina ganin yallabai kamar mun yi suya mun manta da albasa, domin kuwa akwai wani abu guda daya da muka manta ba mu yi magana a kansa ba wanda barin nasa ba karamin illa bane ga rayuwar waɗannan bayin Allah, yallabai ina so a shiga tsananin yayata da wannan matar" nuna innah salamatu tayi tare da kafeta da ido, dafa kirji Innah Salamatu tayi, xata yi magana kenan Adda saratu ta katseta ta cigaba da bayani.
"Da kuma mijinta sannan da ragowar ƴaƴansu, abinda nake so shi ne yallabai ka jawo hankalin mijinta ya dinga sauke hakkin da ya rataya a wuyansa, sannan ya saurara da cikin zarfinta, ya kamata kuma ya kafawa matarsa da ya'yansa dokoki domin suna take hakkin wadannan bayin Allah ba tare da sun yi musu komai ba, kullum burinsu su zage su sannan su ci musu zarafi, cin kashin da suke yi mata ita da ƴaƴanta yayi yawa yanzu haka kafin mu taho nan sun yi yunkurin dukanta,  Allah ne bai sa sun samu damar hakan ba, sannan labari ya iske mu cewa ilahirin kayan dakinta duk sun fito da shi waje sun lalata mata, wannan Dalilin yasa nayi maka magana, don haka a shiga tsakanin su da ita, idan mutunci baxai hada su ba kada su kuskura su shiga gonarta ballantana har su yi tunanin dukanta"

Tana gama magana ta koma ta xauna.
A hankali ya juya ya kalli Baba nasiha mai ratsa jiki yayi musa, kasancewar police din mutum mai addini, ya kawo masa hadisai da ayoyi waɗanda suke magana a kan sauke hakkin aure.

Mayar da kallonsa yayi ga su Innah Salamatu da tawagarta.
"Naji dukkan abinda ake xargin ku da shi, don haka wannan ya xama karo na farko kuma na karshe idan muka sake jin wani labari makamancin wannan,to wlh gaba daya sai hukuma ta dauki mataki a kanku, duk abinda ya biyo baya kada ku zargi kowa sai kan ku"

Umarni yayi da a rubuta takarda dukkansu su saka hannu a kan baxa su sake cin zarafin mu ba, haka kuwa aka yi kowa ya saka hannu sannan aka bada su Baba muka tafi gaba ɗaya.

Kallo daya xaka yi musu ka san abinda ya faru bai musu dad'i ba shi kuwa malam Jibo da iyalansa basu biyo mu ba, sai da muka yi nisa sosai sannan suka biyo bayan mu, wani irin kallo Innah Salamatu take mana tana so tayi magana amma ba dama, sbd dokar da aka saka kafa mata.

gidan Adda saratu muka wuce su kuma suka tafi gida.

Zuciyar mu cike take da farin ciki, na dade ban ji dadi irin na yau ba Allah ya kwato ni daga hannun azzalumi Jibo.

shigar mu gidan ke da wuya naji sallamar Baba, don su innah ma basu san yaxo ba gabana ne ya yanke ya fadi, cikin xuciyata na fada "me kuma ya dawo da Baba wajenmu" sai da ya sake yin sallama ta biyu sannan na amsa.

A sanyaye na sanya hijabi na fita, tsugunnawa nayi har kasa tare da cewa "sannu da xuwa Baba ashe kaine kaxo ya hanya?" shiru yayi min ba amsa, jin bai amsa min bane yasa na dago ido don ganin yanayin da fuskarsa ke ciki. Idanunsa na gani sun yi ja da dukkan alamu yana cikin damuwa, a hankali ya daga baki yace.

"Kira min babarki xan yi magana da ita, sannan ina so kuma ku taho tare da kanwar uwar taki duk ina son ganin ku a nan"

A sanyaye na tashi na shiga ciki, abinci na tarar suna ci don haka na nemi guri na tsaya sbd bana so na katse musu abinda suke yi, gaba ɗaya na kasa zama sbd ban san da sabon abinda yaxo mana da shi ba, maganar Innah ce ta dawo da ni daga duniyar tunanin da na tsunduma a ciki.

"Tunanin me kike yi haka Sa'adatu kika yi shiru ke kadai, ni fa bana so kike yawaita wannan tunanin kada ki je ki cutar da kanki" A hankali na dago
"ba tunani nake yi ba Innah Baba ne yaxo yace yana so xai yi magana da ku, shi ne ban fada muku ba na bari ku gama cin abinci"

Xare hannunta tayi daga kwanon da dukkan alamu ita ma jikinta yayi sanyi "Me kuma ya dawo yayi ba yanxu muka rabu da shi ba?"
Ita ma Adda saratu tayi mamakin dawowarsa, ajiye abincin suka yi suka  saka hijabansu muka fita.

Sallama muka yi masa amma babu wacce ya kalla a cikinmu ballantana har mu sa ran zai amsa mana, waje muka samu, su Innah tsayawa suka yi, ni kuma na samu gefe na tsugunna.

Innah ce tayi ƙarfin halin cewa "Malam lafiya naga ka sake dawowa naga yanxu muka rabu ko wani abin ne ya sake tasowa?"

A yatsine ya dago Yana bin mu da wani irin kallo.
"ko ban ce komai ba kema kin san abubuwa sun dade da tasowa, kuma burinki na son toxarta ni ya cika, kin wulakanta ni kin tozarta amanar da Allah ya baki, kin yi sanadiyyar girgizar al'arshin Allah a yau, da sannu xaki girbe abinda kika shuka, ba wani abu ne ya kawo ni ba illa dai na fada miki cewa tunda kika yi kokarin da har auren Sa'adatu ya mutu, to sai ki nema mata wajen da xata koma ta cigaba da rayuwa don ni dai baxan iya rike karuwa a gidana ba, taje duk inda zata je amma ko a hanyar gidana na ganta duk abinda nayi mata ita ta siya.
Sannan abu na biyu kina da xabin da xaki dawo ki ci-gaba da xaman aure da ni, idan kema kin xabi zawarcin ne sai ki faɗa na sawwake miki, kinga yarki ta samu yar uwa kenan, na bar ku lafiya"

A fusace ya fice ya bar mu, bin sa muka yi da kallon mamaki, a cikin mu babu wanda ya iya yin magana sbd mamakin jin waɗannan kalaman nasa.

Murmushin takaici innah tayi tare da kallon Adda saratu "ko kaɗan waɗannan kalaman nasa basu tayar min da hankali ba, sbd idan da sabo na saba jin su, kuma batun komawa gidan sa nima na gama baxan koma ba, Gara na koma ƙauye nayi xamana ina jin xan fi samun kwanciyar hankali a can, amma wannan masifa har ina"

Girgiza kai kawai Adda saratu take yi, cikin nutsuwa ta dube ni "Sa'adatu kada ki damu da wannan abin da yake faruwa jarrabawar rayuwa ce kowa da irin yadda take xuwar masa, ni nayi alkawari xan cigaba da riƙe ki baxa kiyi kuka ba matuƙar kina tare da ni, ke kuma yaya kada kice baxa ki koma, tunda aure ya xama ibada dole kici karo da abinda zai sosa miki ranki, sbd ita aljanna ba a samunta da sauki, kiyi hakuri ki koma sbd rashin komawarki ba shi ne xai warware waɗannan matsalolin ba, kuma idan kika ƙi komawa kamar kin bawa salamatu wata kofa ne na cin karenta babu babbaka, amma xamanki a gidan shi kansa nasara ne tunda baxa ta sake tayi yadd take so ba, tunda dai yanxu an shiga tsakanin ku da ita, nafi tunanin duk wannan abin ita ce ta shirya masa yaxo ya faɗa, don haka ki koma xaman gidan ya xama dole ko tana so ko bata so"

Ni kaina nafi so Innah ta koma sbd baxan so a ce ni ina gida ita ma tana gida ba, abin xai iya zama abin magana, tunda mutane basa raina abinda za a yi ta xance a kansa.

Jikinmu ba ƙarfi muka koma daki, rarrashin mu Adda saratu take yi da kalamai masu dadi sai da Innah ta huce sannan tafi gida.

Comments nd share

*Jeeddahtulkhair😘*

DUKKAN TSANANI Where stories live. Discover now