DUKKAN TSANANI page 61

1.2K 113 9
                                    

💋💋💋💋💋💋
*DUKKAN TSANANI*
💋💋💋💋💋💋
            *Na*
*Jeeddah Tijjani*
        *Adam*
*(Jeeddahtulkhair)*

*Follow me on Wattpad @jeeddahtou*

              *61*

Cikin gida na shige tare da ajiye ledar da ya bani a gaban Adda, buɗewa tayi muka fara duba invitation card din don ganin ranakun da xa a gabatar da bikin namu, daurin aure ne a farko wanda ya kama za a yi ranar juma'a a babban masallacin juma'a na unguwar mu, sai dinner daga baya kuma sauran shirye-shirye suka biyo baya, yinin Innah ne a ƙarshe.

Ware invitation din ta shiga yi, ta ware nata da na innah, tare da miko min na kawayena, miƙa mata nayi ta rage kasancewar ba ni da wasu kawaye na a zo a gani, sai dai ban sani ba ko Rukayya xata gayyato nata kawayen, naira dubu ɗari izuddeen ya bani, nayi abubuwan walimata gaba ɗaya na dam'kawa Adda kuɗaɗen.

***********

A ɓangaren Innah Salamatu kuwa tuni ta gama rud'ewa, hankalinta gaba ɗaya baya jikinta ganin lokacin bikin Sa'adatu na ta matsowa ita babu labarin na ƴaƴanta, wajen salele ta koma yau a soron gidansa ta tarar da shi ya shimfida tabarma yana fito da hotunan yan matan da suka bashi ya samo musu mijin aure. Sallamar da tayi ne ya dawo dashi hankalin shi.

Da farin ciki ya karbeta gami da bata gurin da xata xauna.

Cike da damuwa ta dube shi.
"Salele har yanzu naji shiru babu wani labari lafiya dai ko"?

Murmushi yayi gami da kallonta
"Akwai labari mana Hajiya salamatu,  tunda gashi Alhaji yau yace xai zo yaga A'isha da fatan dai kun shirya, kin san shi yana zuwa sai magana baya jira shi haka halinsa yake baya yin abu da wasa"

Murmushi tayi
"Ni kuwa na shirya salele, ni da na matsu na kawar da su, ji nake kamar yaran nan gaba ɗaya a kaina suke, bana samun nutsuwa idan na gansu a gabana,. musamman ma zaliha yanzu da ta tsiri fitina kullum ba tada aiki banda yawon shakatawa ita da samari, na kosa na kawar da ita kada ta dakko min magana, ita ma da xaka taimaka ai da ka samo mata ko tsoho ne a samu dai a rufawa juna asiri"

Gyara xama yayi ai wannan ba matsala bace, tunda kina da ni a hannu, fatana dai ki cika min aljihu da kuɗi, yadda xan rika tuntubar manyan mutane don a samo mata mai dan tsoka"

Murmushi tayi
"Ni ba nida matsala indai a bayar da kuɗi ne, ga wannan ka karba kafin buƙatar mu ta biya"

Yau ma naira dubu biyu ta bashi tare da yi mata alƙawarin a yau ɗin nan Alhaji yawale xai zo a gama komai a wuce wajen.

Da rawar jiki ta tafi gida tana zuwa ta faɗawa ƴaƴanta halin da ake ciki, ba ƙaramin murna zaliha tayi ba, ita kuwa A'isha haushi ne ya cika ta sbd yanzu babu namijin da take so sama da malam Jibo, kawai don an fi ƙarfin ta ne shi yasa ta hakura, share tsakar gida innah ta shiga yi tana sharar tana wa'ka tare da yi wa innar Sa'adatu habaici, ita dai tana d'aki bata tanka musu ba sbd tasan ba komai ke damun su ba sama da ciwon hassada.

Karfe hudu dai-dai Alhaji yawale ya iso kofar gidan su, tare yake da salele shi ke rike masa jaka, ya sha shadda kamar gaske, a hankali yake taku d'ai-d'ai har ya iso soron, a tsaye ya tsaya yana karewa gidan kallo gaba ɗaya gidan bai masa ba don ba sosai yake son haɗa harka da talaka ba, cike da iyayi A'isha ta fito tana juyi ita a dole ta samu saurayi mai kuɗi..
gaishe shi tayi cike da izza ya amsa, dama shi haka dabi'ar sa take, akwai jin kai da girman kai musamman ga talaka, duk iyayin da tayi bata burge shi ba, haka nan dai suka yi hirar ba yabo ba fallasa, sai tayi magana goma da kyar zai bata amsa ɗaya. umartar yawale yayi ya duba bayan motarsa ya dakko masa lemukan da ya kawo mata, da rawar jiki tasa hannu ta karba, kallonta yayi yana wata irin dariyar mugunta, cikin zuciyarsa yace

"Ki karbi wannan iya rabon ki kenan, kwadayayyar banxa kina shigowa hannuna kin gama shan irin wannan don ya san kwadayi ne yasa ta aure shi, tunda duk garin nan babu wanda bai san halinsa ba da auri sakin da yake yi, sake murmusawa yayi wannan shi ne lemo na ƙarshe da zaki sha indai daga hannuna zai fito.

A gadarance yasa ta kira masa innarta, tana zuwa ta tsugunna kamar xata yi masa sujjada, shi kuwa yana tsaye a kanta babu girmamawa yake mata magana.

"Gobe nake so na aiko da komai na aure idan kun shirya" cikin rawar jiki tace
"A shirye nake mana Alhaji"

Shafa gemunsa yayi
"Shikenan haka nake son ji, gobe xa a kawo kayan lefe da kuɗin aure gaba ɗaya, amma fa ni ba karya xan yi ba, xan yi komai dai-dai ruwa dai-dai kurji, ba a harkar karya da ni"
Ya ƙarasa yana mata wani kallo, sam A'isha bata yi masa ba, idan yaxo neman aure yana kashewa mace kudi don ya mallaketa, amma wannan baya jin xai iya dukan jikinsa da d'anyen kara yayi mata hidima kamar yadda yake yi wa sauran matansa.

Duniyar tunani Innah Salamatu ta shiga.
"Yanzu abinda mutumin nan xai min kenan, amma bari na amince ban sani ba ko irin abun su ne na masu hannu da shuni, watakila mamaki xai bani shi yasa bai bayyana min abinda xai mata ba"

Katse mata tunani yayi da
"Kin amince"
Da sauri tace
"Sosai ma kuwa Alhaji ai mu albarkar muke nema"

Haka ya karkad'e rigarsa ya tafi ba tare da ya bata ko sisi ba banda wannan lemo katan biyu da ya kawo, ita kanta abin yayi matuƙar bata mamaki.

A tsakar gida suka ajiye lemukan, kowane d'aki sai da suka kai, amma banda na innah sai murna suke yi suna habaici wai A'isha ta samu miji mai arziki, Babansu yana dawowa aka faɗa masa, shi dai Allah ya sanya alkhairi yace, yayi ƙoƙarin ya nuna mata muhimmacin bincike kafin aure amma ta nuna 'kin amincewa dole ya kyaleta ba don ya so ba.

Washe gari da safe aka yi sallama da shi wai an zo kawo kayan lefen A'isha, gaba ɗaya ya manta da xancen sbd bai ɗauki maganar da muhimmanci ba, makocinsa ya kira suka xauna tare suka karbi kayan.

Dubu hamsin ya biya na aure, sai akwatuna biyar da yayi mata, kana ganinsu xaka san tsofaffi ne duk sun ji jiki sun goge sun lalace, 'yan kayan ciki kuwa babu tsiya babu arxiki, bra ma guda biyar kaɗai ya sako sai pant rabin dozen, atamfa kuwa ba a magana don duk kusan a leda ne, less da material kuwa ba a zancen su, don ko daya bai sako ba, shi dai tunda yake karbar kayan lefe bai taɓa karbar irin wannan ba, haka dai ya karba aka yi addu'a aka sanya biki dai-dai da ranar Sa'adatu sannan suka tashi suka tafi.

Innah Salamatu ta kame a daki tana jiran a kawo mata lefe ta gani, tunda aka fara shigowa da shi ta makale tana gud'a gami da yiwa yarta kirari wai yarinya tayi goshi, gadan-gadan aka yo dakinta da kayan a firgice ta buɗe ido tana salati gumi kuwa yanko mata yake yi ko ta ina, da sauri ta dubi baban Sa'adatu tace.

"Shi kuwa wannan mutum an yi matsiyaci ya rasa mai zai kawo mana sai waɗannan yan iskan kayan kamar mun roƙe shi dole"

Kallonta yayi ya tabe baki
"Ke dai kika gayyato shi, ba ni nace yaxo ya auri yarki ba don haka ba ruwana ku kare lafiya"

Yana gama faɗa ya juya ya kyaleta, jiki a sanyaye ta riƙa shiga da kayan d'akinta, cike da takaici ta riƙa budewa babu wani abin arxiki a ciki sai tarin tsiya, babu wanda ta iya nunawa kayan a gidan sbd kada a yi mata dariya.

Shiryawa tayi ta nufi wajen yawale, a fusace take tafiya kamar xata tashi sama.

Wlh typing akwai wahala ku yi hakuri mu haɗu gobe

*Jeeddahtulkhair😘*

DUKKAN TSANANI Where stories live. Discover now