DUKKAN TSANANI page 39

1.4K 116 10
                                    

💋💋💋💋💋💋
*DUKKAN TSANANI*
💋💋💋💋💋💋
           *Na*
*Jeeddah Tijjani*
         *Adam*
*(Jeeddahtulkhair)*

  *Follow me on Wattpad @Jeeddahtou*

            *39*

Washe gari misalin karfe tara na safe naji muryar mijin Addah yana kirana, fitowa nayi cikin shiga ta kamala sanye nake da atamfa na rufe jikina da dogon hijabi wanda sai da ya kawo min idon sahu, cike da nutsuwa na  tsugunna na gaida shi tare da cewa "Abba na shirya" Addah ce  ta fito daga daki tana yi mana fatan alkhairi da dawowa lafiya

Makaranta ce mai girma tare da wadatattun ajujuwa, cike take da dalibai manya da ƙanana, tsarin makaranta yana da kyau sannan akwai cikakkiyar tarbiyya uwa uba kuma ga karatu, makaranta ce da ta haɗa bangarori biyu boko da islamiyya, wannan dalilin ya sanya mutane tururuwar sanya ƴaƴansu a ciki, muna shiga office din shugaban makaranta muka nufa, a hankali mijin Adda yasa hannu ya tura kofar office din tare da yin sallama, da girmamawa aka karɓe mu tare da bamu gurin zama, form din da muka zo da shi ya miƙawa shugaban makarantar, duba form din ya shiga yi tare da kiran wani malami ya bashi umarnin ya tafi da ni ya gwada ni, a nan na bar mijin Adda saratu suna magana, ni kuma na bi bayan malamin ina taku cikin nutsuwa.

Bakin wani aji muka je zaunawa yayi a kan wani benci ya bude file din ya fara tambayata, izifi nawa na haddace yayi mamaki kwarai da nace na haddace Alkur'anin gaba ɗaya, gwada ni ya fara yi duk inda ya janyo min sai yaga na karanta shi dai-dai babu wani kuskure, Kasancewar mun yi karatu mai kyau a makarantar malam Jibo, bangaren littafai muka dawo a nan ne kaɗai na samu matsala, kasancewar makarantar da nayi Kur'ani kadai ake koya mana, don haka ya yanke shawarar sanya ni cikin wani aji da suka bude kwanan nan don na samu karatu tun daga farko.

Raka ni yayi tare da nuna min ajin da xan shiga, a ladabce na saka kai cikin ajin, tarar da su nayi suna ta tilawa ban yi wa kowa magana ba sbd bana so na katse musu abinda suke yi, guri na samu na xauna sai da suka kammala na miƙa musu hannu muka gaisa, wadda nake kusa da ita ne ta juyo ta dube ni fuskarta dauke da murmushi.

"Sannu da xuwa bakuwa, ya sunanki? Ni sunana Khadijah"

Nima murmushin nayi mata tare da bata amsa "Yauwa na gode Ni sunana Sa'adatu"

A hankali muka fara yar hira kafin malam ya shigo, a ɗan hirar da nayi da ita na fahimci Khadijah tana da kirki da san mutane, kwatanta min gidansu ta shiga yi, ashe ma makociyar mu ce gidansu yana kusa da gidan Adda saratu, naji dadin hakan sbd xan samu abokiyar tafiya kasancewar makarantar tana da dan nisa da gidan da nake. Muna cikin maganar malam ya shigo.

Gyara xama muka yi muka bada hankalin mu gare shi, yana shigowa, Ajin yayi shiru kamar ruwa ya cinye kowa da alama dai ana jin tsoron malamin yadda ya kamata, duk da kasancewar sa saurayi hakan bai sa dalibansa sun raina shi ba, kallo daya xaka yi masa ka fahimci mutum ne da baxai karbi raini ba, fari ne sosai yana da manyan idanuwa da dogon hanci fuskarsa kewaye take da saje wanda ya sha gyara, a hankali ya buɗe ɗan karamin bakinsa yayi sallama, cike da ladabi muka amsa gaba ɗaya.

Ji nayi yan ajin suna gaishe shi tare da kiran sunan shi da mu'allim Ahmad, a nan na san sunansa Ahmad.

Dora idonsa yayi a kaina da sauri na sunkuyar da kaina, tambaya yayi yaushe aka kawo ni gaba ɗaya yan ajin suka amsa masa da yau naxo, girgiza kai yayi ya samu guri ya xauna.

Ƙarin Bulugul maram yayi mana biyawa biyu naji na iya, don haka da aka xo biyawa gaba ɗaya muryata kadai kake ji a ajin,  malamin yayi mamakin kokarina da yadda na mayar da hankali kan karatuna kamar dama can a cikin ajin nake, duk abinda aka biya mana cikin kankanin lokaci na haddace shi, mamakin ƙoƙarina yan ajin ke yi a ranar mutane da dama sun so kulla alaƙar ƙawance da ni, amma ban saki jiki da su ba sbd ina so na fahimci halin kowa, dama ni a halittata ban fiye sakin jiki da jama'a ba, sai na san halin kowa nake sakin jikina.

Da aka tashi tare muka taho da khadeejah muna tafe muna hira har muka xo kofar gidan Adda saratu, sbd gidan su yana ɗan gaban gidan mu, a nutse na saka kai na shiga soron gidan, me xan gani??? Malam Jibo ne jingine da bango ya tsura min ido yana kallona, ban bari mun haɗa ido da shi ba na sunkuyar da kaina sbd na san sharrinsa xai iya saka wani abin a idonsa don na rikice nace sai shi, shan gabana yayi ya tare min hanya, ki tsaya ki saurare ni Sa'adatu nayi nadamar abinda nayi miki a baya yanxu nazo gare ki na gyara kuskure na, ki daure ki kalle ni da wannan kyakkyawar fuskar taki, ina so kiyi min murmushinki mai kwantar min da xuciya, wlh na dade a cikin baƙin ciki da damuwa tun bayan da kika tafi kika barni, wani kululin bakin ciki ne ya tokare min kirjina, ban san lokacin da nayi kukan kura ba na hankade shi da karfina, da sauri yayi kokarin fixgo ni Allah ya bani sa'a na shige gida a guje ina haki.

A firgice na faɗa dakin Adda ina kuka, na shiga ukuna Adda wannan mutumin neman ganin bayana yake ban san wanda ya nuna masa gidan nan ba, kinga yanxu yaxo yana magiya wai sai na koma gidansa, na shiga uku ki taimake ni ki shiga tsakanina da wannan azzalumin kada ya salwantar min da rayuwa.

A birkice Adda ta tashi tana dubana, me kike son fada min haka sa'adatu? kada dai kice wannan masifaffen mijin naki ne ya sake biyo ki.
Girgiza kai nayi alamar shi ne, hijabinta ta dakko ta saka, tare muka fita da ita, duba soron ta shiga yi ko xata ganshi amma babu shi babu dalilinsa don haka muka dawo cikin gida.

Dakina na shiga na faɗa kan gado na fara aikin kuka, na tsani malam jibo ko sunansa bana so a ambata sbd muddin na kasance a ƙarƙashin sa, rusa min farin cikina xai yi na har abada, da na koma gidansa gara na mutu na gwammace mutuwa ba aure a kan dai na aure shi, ganin tunani na ƙoƙarin illatani ne yasa na tashi na dauro alwala na shiga jero nafila tare da karatun Alqur'ani, a ranar daga ni har Adda kasa cin abinci muka yi sbd tunani Allah Allah muka rika yi mijinta ya dawo mu sanar da shi halin da ake ciki.

Mun kasa aikata komai sai aikin tunani, bayan isha'i ya shigo ganin halin da muke ciki ne yasa ya tambaye mu Adda ce ta bayyana masa komai, yaji haushi kwarai sbd shi ma ya tsani malam Jibo, ba ƙaramin bata masa rai yayi ba da har yaxo gidansa.

A lokacin ya fita yaje har gida ya same shi, yau ma a kofar gida ya tarar da shi ya riƙe zungureren carbi yana ta faman muzurai, yana ganin shi ya san ba kalau ba don haka ya mike yana ƙoƙarin mika masa hannu su gaisa, bai karba ba ya bishi da wani kallo yana huci ji yake kamar ya rufe shi da duka, buɗe baki ya hau yi wato sakona ya isa gareka kenan, ai dama Sa'adatu tana sona shiga tsakaninmu aka yi, nayi farin cikin ganinka, na san ko ta qini kai mai tursasata ne ta so ni dole.

A fusace ya kalle shi bana son maganar banxa me kake so kace min  wannan ya xama na farko kuma na karshe da xan kara ganinka a gidana, idan kuma ba haka ba wlh wlh sai na daureka.

Matsawa kusa da mijin Adda yayi yana masa wani kallo, kai ka isa kaxo har kofar gidana ka fada min magana a kan matar da nake so, duk baƙin cikin ka sai Sa'adatu ta dawo hannuna idan kuma kace baxa ta aure ni ba ,ina mai tabbatar maka cewa ita ma har abada baxa tayi aure ba ko kare bai isa yaxo wajenta ba shashashan banxa da wofi.

Murmushin takaici yayi tare da furzar da numfashi mai xafi, sai me don ka hana Sa'adatu aure ka sani baka isa ka cutar da ita ba sai da yardar Allah, kaine jahili dakiki da har kake ganin xaka iya yin wani abu a kanta, amma babu wanda ya isa ya hana wani aure sai da yardar Allah, yana gama faɗa masa ya wuce ya kyale shi.

Wani tsaki malam Jibo ya buga, dole na dauki mummunan mataki a kanku, a sati biyu nake so yarinyar nan ta dawo hannuna, kafin shekara nayi mata ciki makiya su mutu da bakin ciki Sa'adatu ta zama ta malam jibo har abada, tattara babbar rigarsa yayi ya koma ya xauna..

A fusace muka ji ya shigo don ko sallama bai samu yi ba sai da ya ɗan nutsu, ya zama dole mu yi wa tufkar nan hanci saratu wannan mutumin son ganin bayan yarinyar nan yake yi, a firgice Adda ta dube shi me kake fada min haka Abba, da yake da sunan da take kiranshi kenan

Gyara tsayuwa yayi yanxu daga wajen wannan mugun nake, shi ne yake faɗa min wai idan Sa'adatu bata koma hannunsa ba ko kare baxai zo wajenta da niyyar aure ba, maimakon naga ta bata rai sai naga tayi murmushi.

Lallai sai yanxu na tabbatar da cewa malam Jibo jahili ne  da rigar malamai, shi har ya isa yace wani baxai yi aure ba, insha Allah yana ganin Sa'adatu xata yi aure ta haihu kuma ta bar hannunsa da yardar Allah.

Nima ko kadan maganar bata taɓa min zuciyata ba, sbd na san Allah shi ke bayarwa kuma shi ke hanawa, a ranar kwana nayi ina salloli gami da neman sauki a wajen Allah,


*Jeeddahtulkhair😘*

DUKKAN TSANANI Where stories live. Discover now