DUKKAN TSANANI page 18

1.4K 135 1
                                    

💋💋💋💋💋💋
*DUKKAN TSANANI*
💋💋💋💋💋💋
           *Na*
*Jeeddah Tijjani*
         *Adam*
*(Jeeddahtulkhair)*

*Follow me on Wattpad @jeeddahtou*

           
              *18*

Tun bayan fitowar Izuddeen daga police station bai sake samun sukuni ba, kullum cikin damuwa da tunanin halin da Sa'adatunsa take ciki yake yi, yana ji a ransa baxai taɓa barinta ba har abada ko ana muzuru ana shaho, gaba ɗaya ya daina fita harkokinsa komai nasa ya tsaya cak saboda tunani, kullum cikin kuka yake duk ya rame yayi baƙi, ko abinci baya ci sai idan mama ta bashi shi ma sai ta rarrashe shi sannan zai ci.

Yau ma kamar kullum kwanon abincin yasa a gabansa, hannunsa rike yake da wayarsa ya kurawa wayar ido yana hawaye, hoton Sa'adatu yake kallo zuciyarsa sai radadi take masa, ji yake kamar yaje ya shaqi Baban Sa'adatu ya fito masa da ita, saboda idan akwai abinda yake da muradin gani yanzu bai wuce Sa'adatunsa ba. Sallamar mama ce ta katse masa dogon tunanin da ya tafi, tare take da abokinsa Kabir karasowa daf da shi tayi fuskarta a bayyane da damuwa.

"Wato har yanzu dai kana nan kana wannan tunanin naka ko Izuddeen, yaushe xaka cire yarinyar nan a ranka ne, tunda mahaifinta ya nuna baya sonka baya son tarayyarka da yarsa ya kamata indai da zuciya aka halicceka kayi hakuri ka kyale masa 'yarsa gudun kada a sake samun matsala, kana ganin dai irin cin mutuncin da yayi mana, aure indai yaxo da haka kamata yayi a hakura a canja she'ka sai Allah ya canja da mafi alkhairi. amma kai kaxo kana tunanin wacce bata damu da kai ba bata ma san kana yi ba, tana can tana rayuwarta cikin farin ciki"
muryar Izuddeen a sha'ke ya fara magana "wlh mama ta damu da ni,duk inda Sa'adatu take yanxu ina cikin ranta ita ma ba a cikin nutsuwarta take ba, ki fahimci yarinyar nan mama tana matuƙar sona bakin ciki ake so a yi mana kawai a raba mu, dan Allah idan kina da hali ki taimake ni ki haɗa Ni da ita"
ya karasa maganar yana kuka.

Ba ƙaramin tausayawa ɗan nata tayi ba saboda ta san yadda zafin ciwon so yake da ciwon rabuwa da abinda mutum yake so, cikin nutsuwa suka samu guri suka zauna ita da kabir, dago fuskarsa tayi "kayi hakuri d'ana ka karbi kaddara ka sanya a ranka wannan ita ce kaddararka idan kayi hakuri Allah xai canja maka da mafi alkhairi, na san abin da ciwo amma kayi hakuri wata rana zai wuce ya xamto kamar bai faru ba"

Shi ma kabir hakuri ya riƙa bashi a kan ya cire damuwa a ransa ya manta da komai kuma ya daure ya ci abincin da ke gabansa, kuka Izuddeen kawai yake sbd ko ya sa abincin a bakinsa baxai iya samun damar hadiye shi ba, duk magiyar da suka yi masa haka suka rabu da shi bai ci abincin ba. Duk ya xama wani iri ya fita a kamaninsa ba shi da aikin da ya wuce kuka kamar yaron da yayi rashin mahaifansa.

Hankalin mama a tashe ta tashi ta shiga wajen Mahaifinsa da sallama ta shiga tare da karasawa inda yake, xaunawa tayi da niyyar ta faɗa masa abinda ke damun ɗan nasu, amma sai ta kasa sai hawaye da ke fita a idonta, tashi mahaifin Izuddeen yayi daga kishingidar da yayi cikin kulawa yake tambayarta

"Lafiya Hajiya me ke faruwa naga kina kuka haka" gefen mayafinta tasa ta share hawayen da ya cika idonta
"A kan maganar yaron nan ne Izuddeen wlh Alhaji yana cikin wani hali tun bayan rabuwarsu da yarinyar nan ya daina ci ya daina sha, kullum cikin kuka wai dan Allah baka lura da yadda ya koma ba ne, duk yayi baƙi ya lalace, dan Allah dan Annabi idan da ɗan kokarin da xaka yi masa, ka taimaka kayi masa ka shawo kan mahaifin yarinyar nan saboda mu ceto rayuwar ɗanmu"
Da kuka ta ƙarasa maganar.

Sauke ajiyar zuciya yayi "Hmmm Hajiya kenan dan Allah ki kyale maganar mutumin nan ki manta da su, mu taya shi da addu'a Allah ya canja masa da wacce ta fi ta, wai dan Allah duk kin manta da abubuwan da suka faru da mu ne? Kin manta irin cin mutuncin da mahaifin yarinyar nan yayi mana, ɗaukan ɗanmu yayi fa ya kulle sai da ya shafe wasu adadin kwanaki sannan ya fito, duk fa yayi haka ne da niyyar tozarta mu  Allah ne ya kiyaye ya takaita abin, a tunaninki da Allah bai yayyafawa abin ruwa ba me kike tsammanin zai faru? Indai gidan wannan mutumin zan je nemar masa aure sai dai idan baxai yi ba gaba daya, saboda ni bana shiga harkar mutumin da baya ganin 'kima da mutuncin na gaba da shi, kije ki cigaba da bashi hakuri Allah ya canja masa da wacce ta fi ta alkhairi"
komawa yayi ya kishingida yana sauraren amsar da xata faɗa masa.

Magiya ta cigaba da yi masa "Ba halin mahaifinta xamu duba ba, nagartar yarinyar xamu duba da yadda mutane suke yabon kyawawan halayenta, idan ka lura da wani abu ita kanta yarinyar ba jin daɗin mahaifin nata take yi ba, kawai don ya zama dole a kira shi da mahaifinta ne amma da tuni ta canja wani uban, don Allah ka duba rokona ka taimaka ka samowa yaron nan mafita, ko baka je da kanka ba ka daure ka aika yayyensa tare da abokanka su nemar maka alfarma a bamu dama mu fito a yi biki"
Har yanxu dai kalamanta ba wani ratsa shi suka yi ba kawai yana bin ta da kallo ne, ɗan murmushi yayi wanda ya ƙara bayyanar masa da kamalarsa.

"Dadina da ke kafiya idan kina son abu, mutumin da bai duba mutuncin Musulunci da ma'kotaka ya ɗagawa ɗan da na haifa ƙafa ba, shi ne xan je wajensa na nemi alfarma yayi min? kawai wannan bata lokaci ne ki tashi kiyi hakuri"

Magiya take yi masa sosai amma har yanxu yaƙi sauka, umarni ya bata taje ta kira Izuddeen yana son magana da shi, da sauri ta tashi ta nufi ɗakin nasa faɗa masa tayi cewa mahaifinsa na son magana da shi, jikinsa babu karfi ya tashi ya bi bayanta.

Cike da ladabi ya shiga dakin tare da yi masa barka da rana, cikin sakin fuska mahaifin nasa ya amsa.
"Yanzu duk a kan soyayya ka xama haka Izuddeen, ka manta da dukkan abinda suka faru a baya? Me yasa kake son jefa rayuwarka cikin wani hali, kaifa malami ne bai kamata ka manta da kaddara ba ka jefa kanka a damuwar da xata iya kai ka ga halaka, bana so na cigaba da ganinka a wannan halin kayi hakuri xan nemar maka wani auren da kaina, kuma baxa a ɗauki lokaci ba za a daura shi"

Kan Izuddeen a sunkuye ya fara magana "Dan Allah Babana mai tausayina kayi hakuri ka taimaka min ka aika gidan su Sa'adatu ka nemar min aurenta wlh Baba ita nake so da ita na tsara rayuwata, baxan iya xaman aure da wata ba idan ba ita ba" da kyar ya iya ƙarasa Maganar sbd kukan da ya ci karfinsa.

Cike da tausayawa mahaifinsa ya dube shi, "shikenan kaje magana ta ƙare xan aika gobe da kuɗin aure idan sun amince sati mai zuwa ma za a sa muku rana a daura aure tunda haka kake so amma duk abinda ya biyo baya babu ruwana"
Wani farin ciki ne ya bayyana a fuskar Izuddeen bai san lokacin da ya saki murmushi ba.

"Na gode na gode Baba Allah ya kara girma Allah yasa kafi haka"

Amsa masa yayi da ameen ya tashi ya tafi, a ranar da farin ciki ya wuni sbd dadin albishir din da aka yi masa, ita ma mama tayi farin ciki sosai sbd ɗanta zai samu abinda yake so.

Kada a manta da comment da kuma share

*Jeeddahtulkhair😘*

DUKKAN TSANANI Where stories live. Discover now