NAJWA Complete ✔

By MSIndabawa

64K 4.7K 9

Najib yaron littafin bai dda buri da aaddu'a sai ta Allah yaya bashi mace ta gari mai ilimi Sumaiyya Yarinya... More

1-5
11-15
16-20
21-25
26-30
31-35
36-40
41-45
46-50
51-55
61-65
66-70
71-75
76-80
81-85
86-90
91-95
96-100
101-105
106
107-110
111
113
114
115
116
117
118
119
120
121
122
123
124
125
126
127
128
129
130
131
132
133
135
136
137
138
139
140
141
142
143
144
145
146
147
148
149
150
151
152
153
154
155
156
157
158
159
160
161
162
163
164
165
166
167
168 End

168

846 59 0
By MSIndabawa

*NAJWA*

BY *Maryam S Indabawa*
*Mans*

Dedicated to *Rashida A Kardam*
*Anty Rash*

*Allah dafa miki. Allah karawa Mama lafiya da nisan kwana. Ameen*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da juriya online writers*

*Allah kara mana hakuri da juriya.*
*Ameen*

*Gidan aminci da karamci. Allah kara basira Ameen*

Page
*168*

*Nagaida ku duk writers ina mika sakon gaisuwa ta tare da jinkinar ban girma. Allah ubangiji ya kare mun ku daga sharrun mutum da aljan da duk abin ki. Allah kara basira. Allah kara hada kan mu.*
*Ameen*

Ina kaunar ku gaba daya.

*kuyi hakiri na jina da kukai shiru kwana biyu.*

*Hakan ya samune na zama na bana samun yi. Amman ayi hakuri.*

Kara gaisawa sukai Mami na tambayar ta ya jikin ta ya su Sumaiyya da me gidan.

Mami dai sai nan nan take da Najwa, Dan ba karamin dadi taji da ta ganta ba.

Haka nan Basma kamar ta goya Najwaa take ji.

Bamma salim ma yana dawowa daga kai. mami yazo ya saka Najwa a gaba wai tayi kiba shi da yake ya ganta da bata da lafiyar.

Ana fadawa Dadyy Najwa ta dawo ya baro office yazo ganin Najwan sa

Kowa yayi murna da zuwan Najwa. Inda aka debi. Kayan ta a kai dakin ta na da.

Mami da kanta ta hada mata ruwan wanka.

Bayan ta fito ne Najib ya kira suka sha hira abin su.



A bangaren Sumaiyya kuwa safiyya nayi ta kwashi kayan ta ta hada ta tafi tasha ta hau mota sai kano.

Ko da ta isa kano gidan su Antyn ta ta wuce, Antyn tasai zuga ta take akan ta bar wani Najib ta shigo gari kawai.

Sai da ta gama ziga ta sannan sukai gidan Mama.

Mama na zaune suka shiga kallon su ta tsaya yi taga daga ina suke tare.

Zama sukai sumaiyya ta mikawa mama takardar hannun ta.

Budewa mama tayi, ta zaro ido tana salati.

Ta ce,
"Yanzu abinda kikai kenan Sumaiyya. kin kaso auren kin dawo. Mene. Najib baya mana amman kika ki zama. Allah ya shirya ki sai kizo mu zauna tare ai."

Mikewa sukai ita da Anty sukai dakin Sumaiyya na da.

Da farko Sumaiyya taso ta sa damuwa aran ta sai daga karshe Anty ta hure mata kunna.

Inda tin kafin ta gama idda suke fita yawon su.

Lokaci kankani Summaiyya tai yi kudi da mota.

Duk yadda Mama zatai mata fada sai ta ce, ai a gidan su Antyn ta suke.

Daga karshe can ta koma da zama. shi kuma baban ta murna yake ta koma gidan Mahaifiyar sa da zama

Mama dai addu'a take mata dan sam ita bata son mu'amalar ta da Amtyn ta.

Najwa kuwa duk tabi kannen Mami da yayan ta da matan yayen ta tai musu alheri kowa da abinda zata kai masa duk da suna da rufin asirin su.

Har wajen Maman Sumaiyya sai da taje tai mata alheri.

Taje wajen su Ummah, inda ummah ta kara gyara jikar ta kamar me.

Najib kuwa yana can yana musu shirye shiryen tafiyar su.

Yau ya dawo da wuri dan ya gama da komai. Yana shigowa Dady ya kira sa.

Dagawa yayi suka gaisa, Dady ya ce,
"Son ina Sumaiyya ne?"

Kai Najib ya sosa ya ce,
"Dady na sake ta."

"What?"
Dady ya fada cikin tashin hankali.

"Dady kayi hakuri, wallahi Sumaiyya tafi karfi na, Dady na. Gaba ni zata so ta kashe ba wani ba. Dady kayi hakuri ka gafar ce ni."

"Ba komai Allah maka albarka. Amman ka daina saurin yanke hukunci."

"To Dady. Gobe ma zan tafi Kano ta can zamu tashi."

"To shikenan Allah kiyaye hanya ka gaishe min da Najwan."

"Zata ji."
Suka fara hira daga ban sukai sallama.

Kwanan su Najwa shida Najib ya dira, Hamma Salim ne ya dauko shi, wannan yasa yayo gida dashi.

Najwa bata san da zuwan sa ba tana kitchen tana yin gulisuwa.
Fitowar da zatai sai ganin shi tayi yana shigo wa.

Yana ganin ta ya bude mata hannu da gudun ta ta tafi ta fada jikin sa.

"Sannu da zuwa Hamma."
"Yauwah Baby na."

Jin shigowar Salim yasa ta sake shi, ta ce,
"Mu shiga ciki."

Kitchen ta shiga ta dauko masa lemo da abinci ta zo ta zuna masa.

Kallon ta kawai yake ta dawo da jikin ta tayi kyau.

Sai da ya fara ci sannan Mami ta sauko suka gaisa.

Yana gamawa ya yi gidan su Ummah daga nan yayi wajen Mami.

*Agur guje*

Kwanan sa Biyar da zuwa suka daga. Su Najwa anyi yawon shakatawa sun sha soyayya ita da Najib.

Sun huta, sun ji dadi sun jiyar da juna dadi.

Rayuwa ta musu dadi sosai.
Sun kuma tabbatar wa da son junan su.

Basa da damuwar komai sai ta faran tawa junan su.

Suna kiran gida inda anan sukaji an sa ranar bikin Hamma Salim.

Fitowar su daga wanka kenan Najib yana shafa mata mai, kallon ta ya tsaya yi.

Iska ta hura masa, ta ce,
"Hamma lafiya?"

"Baby kin kara kyau, kinyi haske, kinga nan."

Ya nuna mata kirji, ya ce,
"Sun kara girma da kyau suna jan hankali na a duk sanda na gan su."

Zaro shi tayi, ta mika masa, ta ce,
"Ungo sha."

Wani yar yaji, na yadda tayi masa magana.

Janyo ta yayi suka rufa da bargo.

Sai da sukaje kasa biyar sannan suka wuce kasa me tsarki.

Kaya kuwa duk garin da sukaje sai Najib ya jidowa Najwa.

Watan su bakwai suka dawo, ta katsina suka sauka.

Gidan Mami, Mami sai murna take tayi nan da su tayi can dasu.

A ranar Najwa taje gidan Zahra, lokacin har Fauwaz ya kara girma.

Dan har ya fara tafiya. Kwanan su hudu suka tafi Kano.

Gidan su Ummah suka fara zuwa, inda Ummah sai nan nan take dasu.

Sai yamma suka tafi gidan su Najwa dan Najib ya ce a ranar zasu tafi Abuja.

Tafiyar dai batayi ba dan sai da suka kwana biyar a kano sannan suka daga.

Kowa Najwa tai masa tsara ta basu kayan su.

Gidan Mami suka dira suna sauka, Kowa yazo ya rungume Najwa yana mata sannu da zuwa.

Suna shiga falon Mami. Mami ta tawo da saurin ta ta rumgume Najwa.

Najwa na shakar kamshin turaren Mami taji juya na dibar ta, daga haka sai tashin zuciya.

Da sauri ta fita daga dakin tayi wajen famfo dake compound din gidan tana shara amai.

Najib ne ke rike da ita, tafi minti goma tana abu daya.

Sai da ya lafa mata sannan ta wanke mata baki, ya dago ta.

Mami ce ta komota, kara shakar turaren da tayi ne, yasa ta kara yin wani aman.

Najwa ta galabai ta dan sai da takai ba abinda take amayar wa sai kakarin.

Sai da ya wanke mata baki sannan sukai bangaren Mami tana maida haki.

Su Bara'atu sai sannu suke mata. Mami ce ta kalli Najib ta ce,
"Son daman bata da lafiya ne?"

"A"ah Mami lafiyar ta kalou."
Mami ta kalle ta ta ce,
"Sannu 'yata."

Cikin lokaci kadan kuma ta dawo dai dai dan har abinci suka ci suka koshi.

Da dare suna zaune a falo Mami da Dady sai Najib da Najwa dake kasa a zaune.

Mami ta ce,
"Son amman anan dai Najwa zatai min kwana biyu ko?"

Shiru yayi, wannan yasa ta kalli Najwa ta ce,
"Najwa zaki kwana ko?"

"Eh!"
Ta fada tana gyada kai.

Kallon Najib tayi da ya zurawa Najwa ido.

Dady ne, ya ce,
"A'ah Najwa gidan ta zata tafi, ai an gama komai ko?"

Da sauri Najib ya daga kai, ya ce,
"Eh Dady daman sallama zamuyi muku."

"To shikenan ku tashi ku tafi Allah yayi albarka ya bada zaman lafiya."
"Ameen!"

Najib ya amsa. Mikewa mami tayi tana kama hannun Najwa.

Dakin Mami suka shiga, nan ta bata kayayaki tai mata bayanin su.

Daga nan sukai bangaren Baba sukai mata sallama.

Tin a hanya taga sun dauke hanyar gida, wani waje ya je ya siyo musu gasaaun nama da lemuka.

Daga nan suka kara dauke wata hanya ita dai tana zaune tana kallon sa.

Wani katon gida suka shiga me kyau dan daga nesa kai ka zata zane ne. Dan kyau da tsarin sa.

Ko kuma kayi zaton ba a kasar kake ba.

Kallon Najib tayi, ta ce,
"Ina ne nan?"

Murmushi yayi ya ce,
"Gidan ki."

Ya bude kofa ya fita. Tana zaune har ya bude mata ita ma ta fita.

Bata kara tabbatarwa da gidan nashi bane sai da suka shiga falon gidan.

Wani katon pics din sune manne a dakin. Ba karamin kyau sukai ba.

Kallon dakin ta tsayi yi, dakin ba karamin kyau yayi ba.

An saka masa pursher pink din kujeru sai adon black a jiki.

Katon falo ne dan su kansu kujerun sun fi set daya a dakin.

Hannun ta ya kama ya fara nuna mata cikin dakunan. A kasa dakin bacci biyu ne, da falo biyu.

Duk an cika su da kaya. Haka sama babban falo ne, sai kofofi guda hudu.

Kofa farko, falo ne da bed room hade da ban daki, dayan ma haka sai daya da aka zuba masa set din gado na yara dayan muka normal daki ne.

Duk gidan an kawata shi yayi kyau haka nan kitchen an cika shi da kayan amfani.

Gidan dai masha Allahu yayi kyau sai tashin kamshi da sanyin AC ke ratsa gidan.

Sama suka shiga kowa ya shige dakin sa. Wanka Najwa tayi ta canja kaya zuwa kayan bacci.

Doguwar riga ce, yar karama iya cinya, ta murje jikin ta da mai me saka kamshi a jiki.

Sai wani turare da ta shafa, tana gaban madubi tana parking din kan ta ya shigo.

Ribom din hannun ta ya amsa, ya ce,
"Yau adon sa nake so a haka"

Ya fada yana Barbaza gashin. Juyowa tayi ta rumgume shi.

Hugging nata yayi, ya ce,
"Baby nah bana taba gajiya dake. Ina kaunar ki."

Murmushi tayi. Gefen gado ya matsa da ita ya zaunar sannan ya fita.

Be jima ba ya dawo rike da Faranti da kofina a hannu sai leda.

Juye musu naman yayi ya sauko da Najwa ya zaunar akan cinyar sa, a baki y dinga bata tana ci yana ci har suka koshi.

Suna gamawa suka fita da kayan sannan suka dawo suka wanke baki suka haye gado suna kashe junan su da soyayya me tsayawa a rai.







*INDABAWA*

Continue Reading

You'll Also Like

49.1K 2.4K 51
"Don ubanki wanki dana barmiki kimin shine kika kiyimin Kika zauna kika rungume wannan shegiyar d'iyar taki wallahi koki aje ta ko kuma yanzu jikin k...
21.6K 1.4K 47
Rayuwa wani abu ne da kan zo mana da kalubale iri iri, wani muna iya fin karfinshi da taimakon Allah wani ko sede mu zubawa sarautar Allah idanu zuwa...
41.6K 2.1K 19
Labarin sanyayyar tacacciyar soyayyar ruhi biyu.. Wanda akai wa auren dole da juna, Amman basu san da hakan ba. Shin ya zaman nasu zai kaya idan suka...
129K 7.3K 45
Complicated🤐🤐🤐 Find out👇👇👇