NAJWA Complete ✔

By MSIndabawa

59.5K 4.5K 9

Najib yaron littafin bai dda buri da aaddu'a sai ta Allah yaya bashi mace ta gari mai ilimi Sumaiyya Yarinya... More

1-5
11-15
16-20
21-25
26-30
31-35
36-40
41-45
46-50
51-55
61-65
66-70
71-75
76-80
81-85
86-90
91-95
96-100
101-105
106
107-110
111
113
114
115
116
117
118
119
120
121
122
123
124
125
126
127
128
129
130
131
132
133
135
136
137
138
139
140
141
142
143
144
145
146
147
148
149
150
151
152
153
154
155
156
158
159
160
161
162
163
164
165
166
167
168
168 End

157

756 55 0
By MSIndabawa

*NAJWA*

BY *Maryam S Indabawa*
*Mans*

Dedicated to *Rashida A Kardam*
*Anty Rash*

*Allah dafa miki. Allah karawa Mama lafiya da nisan kwana. Ameen*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da juriya online writers*

*Allah kara mana hakuri da juriya.*
*Ameen*

*Gidan aminci da karamci. Allah kara basira Ameen*

Page
*157*



*Basira Sabo* jinjina gareki. Allah kara basira da zakin hannu.
*Ameen!"

Nagaishe ki.





Wai ina Sumaiyya ne.

Tinda Sumaiyya ta isa Kano take neman Antyn ta wacce bata gari, duk neman da tai mata a waya bata same ta ba.

Bata tashi samu  ta ba sai da tai sati biyu a kano sannan a lokacin Antyn ta ta ce, ai bata kasar amman zata dawo nan da sati biyu duk abinda ya kamata

Sosai Sumaiyya tai murna. Kullum kafar ta a waje yawo kamar ba matar aure ba.

Duk fadan da Mama take bata ji, kawayen ta kuwa duk sun kara junewa.

Dan har hotel rake binsu, ita bata ganin aibun su ma yanzu.

Abu daya shi ya fi damun ta shine ta raba Najib da Najwa.

Bata da buri da ya wuce wannan dan ita ce daga gun wancan malamin sai gun waccan malamin.

Kowa da abinda zai fada mata ba gaibu dan da akwai wanda ya ce, kafin ta koma auren zai mutu.

Amman komai aka fada mata shiru baya faruwa.

Duk ta daga hankalin ta, ta rame tayi baki, bata samun kwanciyar hankali.

Mama kuwa ba abinda take sai addu'a da take mata.

Sam bata kiran sa, sai dai in ya kira ta.

Duk kudin da ya bata sun kare a bin malamai, wannan yasa tai sa Najib ya kara turo mata kudi.

Be tambaye ta abinda zatai da su ba kawai ya tura mata.

Amman suma cikin sati  sai da ta gigita su.

Kawar ta daya ke mata fada ta nuna mata ta daina abinda take sannan ta bar Najib da Najwa.

Amman sam taki ji abinda yasa ta daina zuwa gun Hauwan ma kenan.

Dan wai da taje zata fara gaya mata Allah yace Annabi ya ce. Ita kuma abinda ta tsana kenan.

Yau tana zaune a gida sai kawai tajoyi sallamar Anty kaltum.

Da sauri ta mike ta taro ta ta a murnar dawowar ta

Mama bata nan dan haka a falo suka zauna.

Anty Kaltum ta ce,
"Sumaiyya ya na ganki haka duk kin rame sai kace ba Summy gaye ba."

"Uhmm kedai bari Anty. Dan Allah ji yadda kika kara haske da kiba har wani ja kike. Mene sirrin ne."

"Sirrin zawarci. Ba abinda yafi zawarci dadi yarinya. Kinga da Alhj lukuman fa muka dawo  jiya. Kudi sai dai na diba abinci sai wanda zanci mota sai wacce nake son haka. Ba ruwana da bacin rai bare nasa damuwa a rai na."

Kallo ta Sumaiyya take, ta ce,
"Anty wai ya zamuyi ne da wannan shegiyar Najwan. Anty kinga inda Najwa ta koma kuwa."

"Kinga ki kwantar da hankalin ki, kafin na dawo na kira wani malamina dake madobi, mu yake jira kawai  tashi muje."

Mayafin ta  dauko kawai suka fita.
Basu zarce ko ina ba sai madobi. Sun isa lafiya, sun yiwa malamin bayanin komai.

Inda ya buga kasa ya dago ya kalle su, ya kuma bugawa ya kalle su, can ya ce,
"Kaltum maganar gaskiya, wannan abin bazai taba rabuwa ba. Ba yadda zamuyi dan Allah ne ya hada su, kuma shi ne zai iya raba su, nidai na dubo duk hanya da zanyi naga na rabasu amman babu. Shawara daya kuyi hakuri kawai."

Ran Sumaiyya kamar me dan bakin ciki. Antyn ta ce,
"Shikenan mun gide."
Suka mike suka bar wajen sa.

"Anty kina ganin haka zamu zauna mu zuba musu ido kenan."
Sumaiyya ta fada

"Ke wa ya fada miki. Ai nan takai muka nufa ki kwantar da hankalin ki kinji."
Murmushi Sumaiyya tayi, ta ce,

"Shiyasa nake kara sonki Anty nah."
can ma da sukaje ba sa'a sunje gu yafi biyar ana shidan ne ya basu wani magani ta sakawa Najwa a bin shan ta insha Allahu zata mutu gaba daya ma.

Ta tafi gida da murna, tinda ta koma ta fara shirin tafiya.

Watan daya ta shirya tafiya.

***************
Najwa da Najib kuwa soyayya tayi gaba kowa yana kokarin farantawa ran da uwan sa.

In kaga Najib da Najwa sai kai tsammanin sun fi shekara nawa da aure dan shakuwa.

Yau kamar ko yaushe suna zaune ita da Najib, kan ta na kan cinyar sa.

Shafa gashin kanta yake idon sa a lumshe, can ta zame kanta ta bude idon ta, ta ce,
"Hamma dan Allah ina son zuwa na gaida Mami."

Kallon ta yayi ya ce,
"Najwa yaushe kika baro gidan Mamin?"

Fuska ta marairaice, ta ce,
"Haba Honey, month fa, please kaji."

Ajiyar zuciya ya sauke, a duk lokacin da Najwa tayi masa shagwaba ba karamin karya masa lago take ba, dan Haka ya ce,
"Shikenan ki bari gobe na kai ki."

Rumgume shi tayi, ta ce,
"Nagode Hamma na."

Mamaki yake yadda take murnar zuwa gun Mami banda Sumaiyya da in ya ce tazo suje zata kawo masa uzuri.

To wajen Mahaifiyar ta ma bata fiya zuwa ba bare tashi. Lallai yanzu yasan yayi dacen aure da yarinya ta gari.

Tin daren ranar take shirya abubuwan da zata kaiwa mami.

Yana fita massalaci, ta hau kwabin cake, me inibi ta kwaba tayi baking nashi.

Sai meat pie da ta kwaba shima, ta zuba masa nikaken nama.

Kaji ta debo a firij, guda biyar ta yayanka ta dora akan wuta, ta zuba albasa da kayan kamshi.

Sai da suka dahu sannan ta soye su. Kayan miya ta diba ta markada ta tafashe su ta soya.

Ruwan tafasa kajin da dashi ta tsaida ruwan miya.

Kayan kamshi da curry da magi ta zuzzuba, sai da miyar ta hadu sannan ta zuba naman da ta soya ta bar su suka karasa dahuwa tare.

Tafiya ta dafa musu da miyar kwai, nan da nan ta gama ta kai musu sama.

Karfe taran dare ta ce lafiya Honey be dawo ba.

Waya ta dauka ta kira shi, be dauka ba, sai daga baya ya kira ta.

"Am sorry Baby na, naje turawa Anty ki kudi ne, tana son ta dawo gobe kiyi hakuri gani nan."

"To Allah dawo da kai lafiya."

A ranta kuwa yana ambatar Sumaiyya taji faduwar gaba.

Addu'a tayi, ta shiga bandaki. Wanka tayi, tai brush sannan ta fito duk jikin ta a sanyaye,

Shiryawa tayi cikin wata, farar doguwar riga wacce da kadan ta wuce gwiwar ta, an mata ado da pusher pink din zare, kanta tai parking nashi, ta feshe jikin ta da turare sannan ta murje jikin ta da burhan.

Tini ta hau fitar da wani fitinan nen kamshi.

Falo ta dawo ta zauna tana kallo, daga karshe ta zame ta kwanta.

Ido ta lumshe ta rasa me yake damun ta.

Tana kwancen nan bata ji shigowar Najib ba.

Kiss kawai taji an manna mata a saman kirjin ta.

Ido ta bude da sauri, kallon sa tayi tai murmushi ta mike zaune.

Fuska ta marairace ta ce,
"Hamma kana jin yunwa ko?"

Kai ya girgiza mata, ya ce,
"A'ah ai bakya bari na da yunwa."

Mikewa tayi ta dauko katon farantin da ta jero musu kayan abincin nasu.

Zaunar da shi tayi, kallo ya bita dashi, cikin nutsuwa ta zuba masa, tayo gun sa ta fara bashi a baki.

Kallon ta yake yana bude baki tana bashi  har ya koshi ta bashi lemo ya sha.

Kallon sa tayi cikin kauna ta ce,
"Sannu Honey."

"Yauwah Baby na."
"Akwai abinda kake bukata."

"A'ah! Nagode Najwa Allah miki albarka."
"Ameen!"

Ta amsa da, janyo ta yayi, ya taba cikin ta, ya ce,
"Baby na baki ci abinci ba."

Fuska ta marairaice, ta ce,
"Honey bana son cin abincin."

"Saboda me? Me kike so na samo miki."
Kanta ta kwantar a kirjin sa ta ce,

"Shawarma nake so, amman kaga dare yayi."
Ajiye ta yayi akan kujera yace,

"Baby ko karfe nawan dare ne in kina bukatar abu dole na samar miki. Kamar yadda bakya bari na da bukatar komai."

"In zo muje?"
"A'ah kar a gane min ke."

"Please love."
"Toh! Ina zuwa."

Yayi cikin daki. Bakar doguwar riga ya dauko mata. Shi da kansa ya saka mata, sannan ya dago ta suka fita.

Hannun sa sakale da nata, a haka yake driving din, zata iya cewa yau ita ce ranar da ta taba fita tin da ta shigo gidan wata daya kenan.

A mota ya barta yaje ya siyo mata sannan suka ya dawo, garin ya zagaya da ita, sai sha dayan dare suka koma gida.

Shi da kansa ya bata a baki, har ta koshi. Tana gamawa suka kwanta.

Washe gari tin asuba bata koma ba, duk abinda ya kamata tayi ta fara yi, tai share sharen ta da goge gogen ta ta turare gidan ya dau kamshi.

Sai da ta tabbatar ta gama duk abinda zatayi sannan ta shiga kitchen.

Break fast ta hada musu, ta shige daki tai wanka, Najib na zaune yana aiki a system din shi ta fito daga wanka.

Sai da tayi kwalliyar ta sannan ta yo wajen sa, yana ganin ta ya ajiye system din ya janyo ta jikinsa.

"Baby na kin iya kwalliya, kinyi kyau."
Murmushi tayi, ta ce,
"Nagode My love. Amman ya kamata ka tashi kai wanka ko? Kaga zamu gidan Mami."

Kallon ta yayi ya ce,
"Toh! Karfe nawa ne?"

Baki ta dan turo ta kalli agogon dakin ta ce,
"Kalli fa har goma da rabi, kaga kafin kai wanka muyi break wajen sha daya fa."

"Bari na karasa aikin."
"A'ah jeka zan karasa maka."
Kai ya make ya ce,
"A'ah ni na gaji ma, hannu na bazai iya cudani ba."

Kallon sa tayi, ta motse baki ta ce,
"Honey wayo ko? To muje nai maka."

"Yauwah Baby nah."
Ta kamo hannun sa sukai ban daki.

Da kanta tai masa wanka wanda daga nan tare suka yi wankan bayan sun gama wasa da ruwan su da soyayyar su. ita ta gyara masa fuska dan har aski tai masa.

Suka fito tana rumgume dashi, da kanta ta tsane masa jiki, sai da suka dau awa daya a wanka ya shirya shi.

Wajen break ma haka ya dinga mata shagwaba sai lallaba shi take yi da kyar suka gama ta shiga ta shirya cikin wata Ash kalar atamfa, me adon ja.

An mata dinkin riga da siket dinkin yai mata kyau, turare ta burshine jikin ta dashi.

Ita ta taya Najib shiryawa cikin ash kalar shadda sai maiko take.

Cikin akwatin ta, ta bude ta dauko, atamfa turmin biyar sai shadda kala biyu, kayan kwalliya ta diba duk ta zuva a wata katuwar jaka.

Da kyar Najwa ta  iya fito da jakar daga daki, Najib na ganin ta ya karaso wajen ta.

Kallon ta ya tsaya yi bayan a amshi jakar hannun ta.



*INDABAWA*

Continue Reading

You'll Also Like

22.4K 2K 29
if you are looking for story that touch your heart and soul this is it
1.5K 160 52
Rayuwar auren su abar kwatance ce. Soyayyar da sukewa junan su, mai girma ce. Tarbiyyar da sukayi wa yaransu mai kyau ce. Komai na Mukhtar da Hafsah...
44.8K 701 16
DELULU & GUILT PLEASURE
276K 13.5K 61
My name is Alex Cruz, I'm a omega, so I'm just a punching bag to my pack. But Emma, Queen of werewolves Sam, queen of dragons Winter, queen of vampi...