NAJWA Complete ✔

By MSIndabawa

59.6K 4.5K 9

Najib yaron littafin bai dda buri da aaddu'a sai ta Allah yaya bashi mace ta gari mai ilimi Sumaiyya Yarinya... More

1-5
11-15
16-20
21-25
26-30
31-35
36-40
41-45
46-50
51-55
61-65
66-70
71-75
76-80
81-85
86-90
91-95
96-100
101-105
106
107-110
111
113
114
115
116
117
118
119
120
121
122
123
124
125
126
127
128
129
130
131
132
133
135
136
137
138
139
140
141
143
144
145
146
147
148
149
150
151
152
153
154
155
156
157
158
159
160
161
162
163
164
165
166
167
168
168 End

142

694 44 0
By MSIndabawa

*NAJWA*

BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da Juriya Online WRITERS*

DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

*ALLAH DAUKAKAKI YASA KI GAMA DA DUNIYA LAFIYA.*

*REALLY LOVE U ANTY NA*

*THANKS FOR UR LOVE ND SUPPORTING*

*PAGE*
*142*

Maman Nur, tnc for ur love nd supporting. Reallly appreciate.


"Hamma na zata mun gama wannan maganar."
"Akan me muka gama?"

"Nace mu hakura ko?
"au bama kiji abinda na fada ba kenan. Ni bazan iya ba toh."

Zatai magana ya ce,
"Bana son kice komai, kuma ni bazan taba barin ki ba."

Mikewa yayi, ya kalle ta, ya ce,
"Tashi mu tafi."

Mikewa tayi jiki a sanyaye, tabi bayan sa.

Mami da Dady har dasu Salim suna falo suka shigo.

Basma ce tayi gun ta a guje tana, cewa,
"Adda sannu ya jikin?"

Hannun ta, ta kama ta ce,
"Naji sauki."

"Sannu Adda!"
"Yauwah."

Suka karasa cikin dakin. Mami ce ta mike ta kamo ta sukai sama.

Ruwan wanka ta hada mata sannan ta fito mata da kayan da zata saka.

Kasa ta sauka ta hado mata abinci, sannan ta kawo mata.

Tana fitowa ta shirya ta haye gado dan baza ta iya cin komai ba.

Har karfe goma Najib na gidan, da ya tashi zai tafi Dady ya ce, sai ya kwana a gidan.

Kafin ya kwanta sai da ya leka dakin da take, tana kwance ta juyawa kofa baya.

Shiga yayi a hankali, leka fuskar ta yayi yaga hawaye na zuba.

Juyawa yayi ya tafi daki  Salim. A ransa yana mamakin Najwa, a ce mutun yana son abu amman ya gwammace ya hakura da abun.

In har ya biye mata akan a rmabun yasan daga shi har ita baza suji da dadi ba.

Wayar sa ya dauka ya kira ta. Sai da ta kusan tsinkewa ta daga.

"Me kike yi?"
"Ba komai."

"Aah Najwa ban sanki da karya ba."
"Hamma dan Allah ka bari."

"Me zan bari me nayi?"
"Ni zaka bari, kuma ka daina damuwa da halin da nake ciki."

"Tayaya zan barki, bayan kina kuma ko bamuyi aure ba dole muna tare. Tayaya ma kike son na daina damuwa dake. Dan ke zaki iya shine kike son nima na daina...."

"A'ah haba Hamma amman kasan nima na  damu dakai da duk lamuran ka, kasan dai ina son ka ko?"

"Anya? Gaskiya ban tabbatar ba tinda kike neman sani a wani hali."

Kuka ta fashe masa dashi ta ce,
"Basan ya zanyi ba. Ni wallahi ban sani ba."

"In fada miki abinda za kiyi."
"Eh!"

Ta fada da sauri.
"Kicire damuwa aran ki, ki bar ni na saka miki farin ciki a rayuwar ki. Ki bar komai a hannu na."

"Hamma..."
Katse ta yayi ya ce,
"Bana son jin komai. Kije ki kwanta sai da safe."

Ya kashe wayar, kasa kukan ma tayi, ta rasa me yake mata dadi da tunanin da zatayi.

Ji take kamar bata da damuwa, to amman bata san me zaije ya dawo ba.

Har ta dau wayar ta tayi dailing number Zahra sai ta tuna da dare nefa gashi tana tare da mijin ta.

Kashe wayar tayi ta kwanta. Lokaci kan kani bacci ya dauke ta.

Tin Asuba Zahra ta kirata da taga kiran sa.

Dagawa tayi ta ce, ya bari anjima sayi magana.

Summy kuwa ana can an koma gun bukan su, gwarin gwiwa ya kara basu.

A wajen bokan ta jiyo labarin barin kasar da zai yi  da an daura auren.

Wannan yasa ta shirya tayi gidan Mamin Najib da kukan ta.

Mami tayi mamakin ganin ta dan zata ce Sumaiyya befi sau biyu taje gidan ta ba.

A auren da yafi shekara uku. Mami ta amsheta hannu bibiyu sannan ta tambaye ta gida.

Anan ne ta fadhe da kuka. Mami kallan ta tayi hankali a tadhe ta ce,

"Kafiya Sumaiyya, ki kwantar da hankalin, ki fadan duk abinda ke damun ki ni kuma nai miki alkawarin taimaka miki."

Hawayen gulmar ta share ta ce,
"Mami daman Najib ne, yanzu wulakanta ni yake dan zaiyi aure, kina gani shekara nawa dashi yana fice fice sauran kasashen amman be taba zuwa dani ba. Amman ynx tin kan yayi auren yace min da matar zai tafi. Mami yanxu an min adalci kenan."

Kai Mami ta jinjina gaskiya tasan ba ai mata adalci ba.

"Kiyi hakuri, kar ki damu dake zeje ba inda zai tafi da amaryar tasa. Ki kara hakuri akan wulakancin da yake miki kinji."

"To Mami nagode, bari na tafi."
ta mike sukai sallama tayi waje.

Su Talle ta hadu dasu a compound din gidan suna ganin ta suka tuntsire da dariya.

Kallon su tayi, tai kwafa tayi wajen motar ta ta shiga ta fice daga gdn a guje.

A ranta tana murna da abinda Mami ta fada.

Wannan abin ya dan kara kwantar mata da hankali da abinda Anty ta tayi, kuma ta aikata.

Zahra kuwa hankalin ta duk ya tashi game da Najwa.

Wajen karfe bakwai bayan ta gama shirya mijin ta ya tafi aiki ta kira ta.

"Najwa lafiya kuwa?"
"Zahra ina fa lafiya."

"Innalilahi wainna ilahir rajiun! Me ya faru?"
Kuka Najwa ta fashe da shi ta ce,

"Zahra, Najib ashe  mijin Sumaiyya ne."
"Wacce Sumaiyyan."

"Sumaiyya dai da kika sani, 'yar Mama "
"To shine me?"

"Au wai kema haka zakice. Haba Zahra kinsan fa wace Sunaiyya ko?"

"Na sani, amman kuma mene a ciki. Kina son shi yana sonki, to menene da ita zaki zauna ko, kuwa itace mijin ki. K bansan irin halin ki ba. Da kika ce ba lafiya na zata wani abu ne ashe akan Sumaiyya ne. To nidai shawara zan baki in har iyayen ki na son auren nan kuma shima Najib din yana kan bakan shi kada ki soma cewa bakya yi. Wallahi Najwa kika bar Najib da kyar zaki samu wani namijin irin sa. Kinsa dai Najin kinsan halayen sa to ki rike abin ki gam kada ki sake kiyi wasa da damar ki."

"Zahra....."
sauri katse ta zahra tayi, ta ce,
"Kinga Najwa, kefa ba yarinya bace, akan me ma kina son abu dan wani ki bar shi, bayan auren ku ba haramta yayi ba. Kinsan adadin mutanen dake fatan auren nan kuwa. Kinsa farin cikin mutane nawa kuka kara a dalilin auren na. Najwa ki tsaya kiyi karatun ta nutsu kisan abinda kike so. Kina son sa to in kin rabu dashi ya zakiyi. Kinsan kuwa illar kana son abu ka bar shi, komai zai iya faruwa daku na dadi da akasin haka. Wai kinsan ma tin yaushe Najib ke son ki. To bazan fada miki ba amman ki same shi ki tambaye shi  Najib masoyin ki tin kafin yasan ki ko wani abu naki. Najib ya cancanci so daga gareki."

Murya ta sasauta ta ce,
"Kiyi hakuri Najwa duk dan samun farin cikin ki ne, ina son ki ina son farin cikin da kwanciyyar hankalin dan Allah ki kwantar da hankalin ki, ki bashi goyon baya ayi komai a gama."

"Nagode Zahra,"
"Ba godiya a tsakanin mu."

Murmushi tayi. Sukai sallama.

Tana gama waya sai ga kiran Najib nan.

Tana dagawa ya ce,
"Zahra ya kike ya gida."

"Lafiya lou."
"Zahra kinji abinda Najwa zatai mana ko? Najwa sam ta juyan baya, dan Allah ki mata magana."

"Kar ka damu, wallahi yanzu muka gama waya kuma na mata fada da nasiha insha Allahu komai zai dai dai ta."

"Toh Zahra Nagode Nagode."
"Ba konai Hamam ai yiwa kai ne. Nida nasan komai ai ba zan yadda ta bar ka ba. Kaima ya kamata tasan duk wahalar da ka sha aka ta."

"Ba komai. Nagode."
Sukai sallama ta kashw wayar

Najwa kuwa ranar ko falo bata fito, sai dai Mami ta kai mata abinci da magani, daga kwanciya sai kwanciya.

Najib ma be neme tta ba dan ya bar ta ta gama tunanin ta ne.

*INDABAWA*

Continue Reading

You'll Also Like

258K 10.1K 32
""SIT THERE AND TAKE IT LIKE A GOOD GIRL"" YOU,DIRTY,DIRTY GIRL ,I WAS TALKING ABOUT THE BOOK🌝🌚
81.2K 6.5K 44
Labarin budurwa mai rayuwar Kwad'ayi da buri, cike da rashin godiyar Allah,........................
908K 30.9K 110
When Grace returns home from college, it doesn't go like she thought it would. With her past still haunting her everyday choices, she discovers a sid...
2.1K 121 21
YAR AREWA (THE NORTHERN GIRL) Meet JASMINE BILAL SHAREEF In her journey of becoming a lady pilot" Kalma daya ta daddy i need a mom shi ne mafarin t...