NAJWA Complete ✔

By MSIndabawa

59.5K 4.5K 9

Najib yaron littafin bai dda buri da aaddu'a sai ta Allah yaya bashi mace ta gari mai ilimi Sumaiyya Yarinya... More

1-5
11-15
16-20
21-25
26-30
31-35
36-40
41-45
46-50
51-55
61-65
66-70
71-75
76-80
81-85
86-90
91-95
96-100
101-105
106
107-110
111
113
114
115
116
117
118
119
120
121
122
123
124
125
126
127
128
129
130
131
133
135
136
137
138
139
140
141
142
143
144
145
146
147
148
149
150
151
152
153
154
155
156
157
158
159
160
161
162
163
164
165
166
167
168
168 End

132

594 52 0
By MSIndabawa

*NAJWA*

🌐  *HAJOW*  🌐

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

By *MARYAM  S  INDABAWA*
*MANS*

DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

*ALLAH YA SAKA MIKI DA GIDAN ALJANNA.*
*AMEEN*

PAGE
*132*

*Ummu Ayda na gode sa kaunar ki gareni da littafi na. Nagode Allah bar kauna. Ameen*



Baffah da kansa yaje ya dauko Najwa dan ya ce, acan zasu je ta sauki bakon nata.

Duk abinda zatayi amfani dashi sai da ta diba sannan ta tafi.

Ranar da zai sauka tare da Ummah suka shiga kitchen suka tare shi da abinci kala kala na gargajiya da na zamani. Hakan nan lemo ma.

Ba wanda yakai su Ummah murnar hadin nan.

A gidan su ya sauka, da yamma ya kira ta, ta bashi address din inda take.

Murmushi yayi da yaji tana gidan su Ummah.

Kayan da ya kawo musu ya diba ya fito.

Cikin wata light brown din shadda an mata aiki da dark brown din zare dark brown din hula ya saka da takalmi.

Idon sa kuma sanye da farin tabarau ba karamin kyau yayi ba.

Sai tashin kamshi yake.

Ummah da kanta tasa aka kawo mata me yin kwalliya wai sai an wa Najwa kwalliya duk hakurin da ta bawa Ummah kin yadda tayi.

Me kwalliya ba karamin kwalliya tayiwa Najwa ba.

Dan tayi kyau ke kyace amarya ce.
wata atamfa ta dauka jikin ta siiblue, da orange a jiki.

An mata dinkin riga da siket, dinkin ya zauna a jikin ta sosai.

Dauri akai mata shima me kyau wanda ya kara fito da kyan ta.

Turare Ummah ta bata ta feshe jikin ta dasu.

A falon Ummah aka jere masa duk abinda zai bukata.

Biyar da rabi ya kirata yace, ya karaso.

Ummah ta fadawa ta fita shigo dashi. Yana tsaye a jikin motar sa ya harde hannun sa a kirji.

Kofar da zata fito ya zubawa ido. Duk gaisar dashin da suke hankalin sa na kan Najwa da ta fito.

Baki ya saki da hanci yana kallon ta. Har ta karaso be san ta karaso ba. Sai da ta tafa hannun ta sannan ya dawo cikin hankalin sa.

"Hamma wannan kallon haka."
ta fada kan ta a kasa.

Murmushi yayi, ya ce,
"Ai ke din ce."

Dan hararar sa tayi, ya ce,
"Ni shige muje."

"Haba sarauniyar mata, ina nasan gidan da zanyi gaba."
Gira ta daga, ta ce,

"Haka ne fa."
Tayi gaba ya biyo bayan ta.

Har babban falo ta dire shi, sannan ta zame kasa ta gaisar dashi.

Kasa amsawa yayi, sai kallo da ya bita dashi.

"Hamma!"
Ta fada a shagwabe.

"Menene?"
"Ina gaishe da kai kayi shiru."

"Ayyah yi hakuri wallahi duk na rasa control di nane."
Ido ta zaro, ta ce,

"Hamma gidan mutane fa."
"Gidan mu dai. Ba gidan kakan nn ki bane."

"Nan ne."
"To ai gidan da zamufi shan soyayyar mune."

Baki ta rufe da hannu tace,
"Dan Allah ka bari man."

Dariya yayi, ya ce,
"To na bari. My beauty."

Murmushi tayi, sanna suka gaisa dashi.

Lemon kwakwa wanda yaji madara da dabino ta zubo masa. Ya sha sanyi.

Amsa yayi yana mata godiya. Yana kurba ya lumshe ido, yana me jin wani sanyi a cikin jikin sa.

A hankali a hankali ya dinga sha, snaks ta mika masa, sosai ya ci.

Dan kasa cin girkin da tayi ma yayi, har magariba yana gidan dan sallah yaje ya dawo.

Tare da Baffah suka shigo, Baffa na tsokanar sa da bazai bashi Najwa ba.

Dariya yayi, ya ce,
"Ai Baffah da kun kaini kabaru kuwa, dan nasan na rasa Najwa na rasa rayuwata ne."

"Ja'iri toh nagodewa Allah da ya hada Najwa da me son ta kamar ka. Allah baka ikon rike ta amana.
Najib na dade ina rokan Allah ya bawa yarinyar nan miji na gari kamar yadda kai ma nake maka addu'ar nan.
A duk cikin jikokina kun fita zakka. Bbawai nafi son ku bane. A'ah, kai Allah ya baka hankali da nutsuwa tare da ga ilimi. Kuma kuna amfani dashi. To haka ma Najwa. In ka zauna da Najwa nasan zaka gane nagartar ta.
Najib na baka amanar Najwa karike min ita hannu bibiyu,"

Kasa Najib ya dauka daga kan kujera, hannun Baffa ya kama ya ce,
"Baffa na maka Alkawarin bazan taba  yarda amanar nan taka ba. Zan rike ta hannu bibiyu insha Allah, ka tayani da addu'a Allah bani ikon rike ta."

Kansa Baffa ya dafa, yana shi masa albarka.

Dai dai lokacin su Najwa suka fito daga dakin Ummah.

Kallon su take yi cike da sha'awar su, Falon suka karasa,

Kan Najwa a kasa, ta ce,
"Baffa barka da dawowa!"

Kallon ta yayi, Cikin so da kauna, ya ce,
"Yauwah Najwa ya bakon naki."

Fuskar ta, ta rufe a jikin Ummah, dariya su ka, saka gaba dayan su.

Najib kuwa murmushi yayi, yana kallon ta. Ji yake kamar yaje ya rumgume ta.

Ummah ya kalla, ya matsa kusa da ita, ya ce,
"Tsohuwa me ran karfe ina yini?"

"Kai ni ban amsawa ace, tin dazu ka kasa zuwa kazo ka gaushe ni."

Dariya Baffa yayi, ya ce,
"Ke dai kishi kike kawai."

"Affuwan uwar gida na, amaryar taki ce akwai siye mutane, Allah Ummah in ina tare da ita bana iya tina koma."

Hannu ta fara tafawa tana salati. Najwa kuwa kara makale Ummah tayi, a ranta kuma tana mamakin ko Najib yasan san su haka ne.

Sun jina suna hirar su da tsokana tsakanin su ta jika da kakanni sannan Baffa ya kalli Najwa da har lokacin ta tana makale da Ummah.

Kai ya girgiza, yana murmushi, a ransa yana jin dadin halin Najwa na Kunyar nan.
"Najwa ai sai a bashi abinci ko?"

Kamkame Ummah tayi, Ummah ta ce,
"Oh ni "ya su, dan Allah sake ni, kai haka kake fama da ita da wannan kunyar tata."

Dariya Najib kawai yayi, a ransa kuma ya ce,
"Allah dai yasa kar wannan kunyar ta cuceni. Amman kuma tana mata kyau."

Da kyar ta mike ta hada masa abinci a babban falo.

Bema ci ba, sai kallon ta da ya tsare ta dashi.

Da zai tafi ya kaiwa Su Ummah kayan da ya kawo musu yai musu sallama.

Abincin ta kwashe ta saka masa a motar sa.

Sai da ya zauna sannan ya miko mata tata ledar.

Da kyar ta amsa tana masa addu'a. Inda sukai dashi akan gobe zai dawo.

Cike ta shige ciki da jin kunyar kakannin nata.

Kayan da ya kawo mata ta dire musu tayi cikin Dakin Ummah.

Kwanciyya tayi, tana tunanin Najib. Ta tabbata son Najib ya vama gauraye jikin ta, zuciyar ta kuma sonsa kadai ta sani ta kuna saba dashi. Rabata da Najib ba karamin abu bane.

Yanzu ta gane ba karamin kamu son sa yayi mata ba.

Tana godewa Allah da ya bata shi, tana kuma addu'a Allah yasa shine Alheri a rayuwar ta.

Ido ta lumshe, fuskar sa ta gani tana sakar mata da murmushi me santaya zuciya. Itama murmushin ne ya subuce mata.

Fulo ta jawo ta rumgume, a ra ta kuma tana cewa
"yanzu fa sauran wata biyu ta zama mallakin Najib."

Wata fadywar gaba taji kirjin ta yayi, wanda sai da ta dafe shi.

Ita tsoron sama takeyi gaba daya.

*INDABAWA*

Continue Reading

You'll Also Like

44.7K 701 16
DELULU & GUILT PLEASURE
256K 10.1K 32
""SIT THERE AND TAKE IT LIKE A GOOD GIRL"" YOU,DIRTY,DIRTY GIRL ,I WAS TALKING ABOUT THE BOOK🌝🌚
276K 13.5K 61
My name is Alex Cruz, I'm a omega, so I'm just a punching bag to my pack. But Emma, Queen of werewolves Sam, queen of dragons Winter, queen of vampi...
37.8K 738 10
A girl that was raised by a single Mum, she's a Baker, a henna designer meet the love of her life, but In between their love lies another love, what...