NAJWA Complete ✔

By MSIndabawa

59.4K 4.5K 9

Najib yaron littafin bai dda buri da aaddu'a sai ta Allah yaya bashi mace ta gari mai ilimi Sumaiyya Yarinya... More

1-5
11-15
16-20
21-25
26-30
31-35
36-40
41-45
46-50
51-55
61-65
66-70
71-75
76-80
81-85
86-90
91-95
96-100
101-105
106
107-110
111
113
114
115
116
117
118
119
120
121
122
123
124
125
126
127
129
130
131
132
133
135
136
137
138
139
140
141
142
143
144
145
146
147
148
149
150
151
152
153
154
155
156
157
158
159
160
161
162
163
164
165
166
167
168
168 End

128

598 49 0
By MSIndabawa

*NAJWA*

🌐  *HAJOW*  🌐

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

By *MARYAM  S  INDABAWA*
*MANS*

DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

*ALLAH YA SAKA MIKI DA GIDAN ALJANNA.*
*AMEEN*

PAGE
*128*

"Wayoo ido na!"
Ya fada yana kallon ta.

Ai kuwa da sauri ta dago kanta tana kallon idon nasa.

Kallon juna suke, duk sun kasa kawar da idanun su.

A ran Najwa ta ce,
"Tabbas nasan wannan fuskar da idon,"

Ita ganin kamar su ma takeyi ta wani fannin  haske kadai zata nuna masa.

Allah me iko, Gaskiya Najib kyakyawa ne, dan dai shi baki ne kawai. Amman bakin nasa me kyau ne.

Ga ido da hanci, ga bakin sa dan karami dashi, haka gashin kansa ma me kyau dashi a kwance.

Ba abinda take gani a cikin idon ta face so da kaunar ta da suka mamaye shi.

Shima kallon sanin yake mata, amman yana daukar wannan sanin da ganin da yayi mata sune suke sawa yake kallon ya santa.

Idonun ta ba karamin burgeshi suke ba. Manya ne, masu kyau da su. Gasu farare tas dasu.

In ta saka kwalli wani kyau suke karawa da girma.

Yana son mace mai ido sai gashi Allah ya bashi Najwa me idanu abin shawa'a.

Haka nan bakin ta ba karamin son su yake ba. Dan dan karami ne abin sha'awa gasu pink da su  daga ido ma kasan masu laushi ne.

Haka hancin ta dogo ne gashi siriri. Gaban goshin ta kuwa gashi ne kwance luf luf dashi.

Haka jirar ta me kyau da ita a gyare kamar wacce aka yanke ta.

Suna jima suna kallon sunan su. Kuwa na aikawa da dan uwan sa sakon su ta idanun sa.

Najwa ce tayi karfin halin dauke idanu  ta tare da rufe fuskar ta da hannun masu kyau tsirara dasu.

Dariya yayi, ya ce,
"Muje mu zauna in fada miki abinda nace sai mun hadu."

Gaba tayi a ranta tana son tuno da me zai fada mata.

Akan wasu kujeru suka zauna, kallon ta yayi, ya ce,
"Najwa yau baki tambayen Antyn ki ba."

Murmushi tayi, ta ce,
"Ai haduwar mukenan shiyasa. Ya take, ka baro ta da kewar ka. Allah in nice kafata kafar ka."

Wani dadi yaji a ransa. Murmushi yayi ya ce,
"To Allah kaimu lokacin! Abinda nake son fada miki kenan. Ina da mata. Zaki iya aure na haka."

Kai ta girgiza masa ta ce,
"A'ah!"

Ido yayo waje dasu, ya ce,
"Dan Allah Najwa ki taimaka ki soni a haka muyi aure dan  Allah."

Ganin yana neman ya sauka ya durkusa yasa ta ce,
"Da wasa nake maka fa."

Kallon ta yayi dan ya gano da gaske take.
Kai ta daga masa ta ce,
"To mene dan kana da mata. In ban auri me mata ba. Watakila ni a kawo min ita.
Ba yabon kai ba. Allah bana kin kishiya in har zamu zauna lafiya.
Bana ganin aibun ta sam."

kallon ta ya tsaya yi dan ba karamin burge shi tayi ba.

Kuma ya gano gaskiyar abinda take fada ta cikin idon ta.

"Gaskiya Najwa samun kamar ki sai ansha wuya. Allah ya mallaka min ke."

A ran ta, ta amsa da
"Ameen!"

Kallon ta yayi, ya ce,
"Baza kice Ameen!"

Murya ta marai raice, ta ce,
"Haba na fa, fada."

Dariya yayi kawai. Da haka suka dinga hira har Mustapha ya zo shima suka zauna suna tayi.

Sai magariba suka tafi, bayan ya bawa Zahra kayan da ya kawo musu. Da kyar ta amsar musu ta ce, kada ya kuma. Bayan godiya da addu'a da tayi masa.

Dadi yaji dan bai taba bawa Sumaiyya abu tai masa godiya ba.

Haka Najwa da Zahra takai musu itama godiyar tayi masa da jadadda masa dan Allah kada ya kuma.

Shi abin ma har dariya yake bashi sai kace wanda ya kai musu wani abu.

Haka wai kada ya kuma shikan bai ga lokacin da zai daina bata abu ba.

Haka da dare ya aika musu da kayan abinci su idomie lemuka madera bisit.

Ba yadda sukai haka suka karba. Godiya Zahra tayi masa. Najwa kuwa kin kiran sa ma tayi.

Dan ta fada masa kada ya kuma gashi ya kuma.

Duk kiran da yayi kin dauka tayi sai da ya hada ta da  Mustapha da Zahra.

Su suka shawo kanta. Godiya tayi masa tana kuma me kara jan hankalin sa da kada ya kuma.

"Wai me yasa kike fadan haka?"
Ya tambaye ta.

"Ni bana son mu daura maka nauyi. Kuma in a gida akaji fada za ayi mana. Dan Allah ka daina kashe kudin ka akan mu."

Gaskiya halayen Najwa na burge shi, dan da wasu ne karba zasu yi tayi.

Banda roko da yan matan yanzu suke wai ace saurayi shi zai na maka komai.

Ai wadan nan abubuwan su suke jawo wa yan mata su baci.

Wannan ta ce, saurayin ta ya mata abu. In ya mata dan Allah wata ba dan Allah zai mata ba.

Ko ta wacce hanya ce zatabi dan ganin an mata shi.

A koda yaushe yana godewa Allah da kuma kara addu'ar Allah mallaka masa Najwa.

Dan yasan  ya'yan sa zasu samu tarbiya da nagarta.

Yana tuna kullum sukai waya sai ta tambayi ina Mami ko ta ce a gaishe ta.

Abinda Summaiya bata taba yi ba, bare ta ce zataje.

In ya ce ma tazo suje sai ta kawo wani abu duk son da Mami ke  mata amman ita ta wufantar.

Abubuwa da yawa na  dada masa son Najwa.

Kullun sai yazo da yamma har lesson yake musu.

Haka in yana Abuja ta whatsapp ma yake musu ko ya koya musu assignment.

Ana haka har suka gama level three suka tafi hutu.

Duk yadda yaso yazo cikin hutun hana shi tayi ta ce ya kula da Antyn ta da aiki.

Yaso yazo ta nuna bacin ran ta wannan yasa ya hakura.

Tasan in har yazo sai yayi sati biyu ko uku.

To matar sa fa, da aikin sa. Ai zasu shiga hakkin ta.

Shi ita nauyi take ji ace wani yazo gunta.

*Bayan shekara daya*

Abubuwa da yawa sun gudana. A ciki har da kara shakiwa tsakankn Najib da Najwa.

Wanda duk wata sai yaje ya ganta duk da basu taba haduwa a gida ba.

Su Najwa har an kammala makaranta sun fita service.

Inda aka saka ranar bikin Zahra wata biyu da fara seevice din su.

Wannan yasa Najwa ta ce, sai ta kammala service din ta zata koma gida gaba daya.

Su Mami da Dady duk sunzo graduation din su dasu Hamma Salim.

Da first class suka fito, Najib be samu damar zuwa ba saboda baya kasar.

Ba karamin rashin jin dadi sukai ba. Ranar da zasiyi dinner din su a ranar ya dawo dan haka katsina ya sauka.

Ranar kawai ya samu hallartar bikin kammala karatun su.

Sun sha hotuna inda ya basu kyaututuka masu yawa dan har waya ya sauya musu.

Lokacin dai dole suka amsa suna masa godiya.

Washe gari ya koma Abuja.

Sumaiyya kuwa ba abinda ya canja sai gaba da abubuwa suka karayi.

Dan kazantar ta ta kuma yin gaba.

Ta kuma samun ciki wanda Najib be san da shi ba ma ta zubar da shi.

Kawaye sai kara rudar ta suke bata yin abu dan kanta sai kawaye.

Gata kullum bani bani. Najib kuwa sai addu'a yake mata.


*INDABAWA*

Continue Reading

You'll Also Like

2M 100K 37
Presenting the story of ISHIKA MEHRA Whose innocence made the king bow down to her AND ABHIRAJ SINGH RATHORE Whose presence is enough to make the per...
10.1K 591 13
Hamida was an ordinary girl trying to fit in, into the world entirely. after the death of her father, she and her mother moved in to stay with her Un...
85K 9.2K 14
Ku biyoni don jin Labarin Hauwa... Its a True Life Story... Kyauta ne, ba na siyarwa ba 😉 Its Free Y'lls ♥️