NAJWA Complete ✔

By MSIndabawa

59.6K 4.5K 9

Najib yaron littafin bai dda buri da aaddu'a sai ta Allah yaya bashi mace ta gari mai ilimi Sumaiyya Yarinya... More

1-5
11-15
16-20
21-25
26-30
31-35
36-40
41-45
46-50
51-55
61-65
66-70
71-75
76-80
81-85
86-90
91-95
96-100
101-105
106
107-110
111
113
114
115
116
117
118
119
120
121
122
124
125
126
127
128
129
130
131
132
133
135
136
137
138
139
140
141
142
143
144
145
146
147
148
149
150
151
152
153
154
155
156
157
158
159
160
161
162
163
164
165
166
167
168
168 End

123

560 53 0
By MSIndabawa

*NAJWA*

🌐  *HAJOW*  🌐

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

By *MARYAM  S  INDABAWA*
*MANS*

DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

*ALLAH YA SAKA MIKI DA GIDAN ALJANNA.*
*AMEEN*

PAGE *123*

"Allah yasa su zo, dan basa kula samari."

Ta fada tana yin cikin dakin nasu.

Kallo ya bita dashi, har ta kure masa.

Tana shiga dakin suka gaisa, sannan ta ce,
"Anty Najwa da Anty Zahra wani ne a waje yace dan Allah kuje wai."

Kai Najwa ta dauke ta hau kan gadon ta, dinkin da suka amso ta dauka tana karawa da mayafin da suka siyo.

Zahra kuwa kallo  ta, ta tsaya yi.
Je kice gamu nan."

Ta juya ta fita. Fada masa tayi, kudi ya debo ya bata kin amsa tayi sai da kyar.

Yarinyar na fita Zahra ta matsa gun Najwa tace,
"Wai ke mene haka kinji dai abinda aka ce ko? Kinsan waye?"

"Ban sani ba dan haka bazani ba."
Mikewa Zahra tayi ta Dauki Hijab din ta. Tayi waje.

Tin daga nesa take kallon sa tana son tina a ina ta sanshi.  A ranta ta ce, ko me kama dashi ta sani ne.

Karasawa tayi wajen sa da sallama.
gaisawa sukai cikin girmama shi.

Fuskar sa dauke da murmushi ya ce,
"Dan Allah kiyi hakuri nasan baki sanni ba, amman dan Allah yar uwar ki da kuka shigo yanzu nake son gani."

Kallon sa tayi, gayen yayi beda makusa kuma kowa zai yi kwadayin samun sa.

A fuskar nagarta kuwa daga kallo kasa mutunin kirki ne.

"Kinyi shiru?"
Ya katse mata tunani.

Murmushi tayi, ta ce,
"Najwa yanzu bazata iya fitowa ba kanta ke ciwo magani ta sha har ta kwanta ma."

"Ayyah to ki mata sannu amman dan Allah gobe zan dawo ko zuwa anjima."

Amsa masa tayi da
"Ba komai."

Godiya yayi mata ya shiga mota ya tayar.
Zuciyar sa kamar kankara dan murna da farin ciki.

Daga nan gari ya shiga zagayawa cikin nishadi abinda be taba yi ba a garin katsina ba kenan.

Tana shiga daki ta kara sa gefen gadon da Najwa ke zaune.

Kallon ta tayi, ta ce,
"Sis gunki yazo, amman nace baki da lafiya. Ya ce anjima ko gobe zai dawo."

Kai ta dauke kamar bata ji ba.
"Wai kuwa lafiyar ki kalou kuwa? Allah ina jin sai na hada ki da Mami."

Harara ta tayi, mikewa tayi ta koma kan kujerar dake dakin. Tana magana

"Amman fa gayen ya gama haduwa da badan ina da Mustapha na ba da ba abimda zai hana in so shi."

Tsaki Najwa tayi ta dauki littafin ta tana dubawa.

Dariya Zahra tayi itama ta dauki littafin ta tana dubawa.

Besamu komawa a daren jiya ba dan haka yau tin karfe goma ya dira a makarantar.

A lokacin ma suna jarabawa yafi awa daya sannan aka fara fito daga jarabawar.

Yarinyar jiya ya hango, dan haka ya dago mata hannu.

Da sauri ta kasa wajen sa tana gaishe dashi.

Murmushi yayi ya amsa,
"Dan Allah Su Najwa zaki kara kira min."

"Toh!"
Ta amsa ta nufi library dan tasan suna can dan tin dazu suka fito.

Tana shiga ta hango su suna karatu. Karasawa wajen tayi, ta ce,
"Ina yini  ku?"

"Lafiya!"
Suka amsa, Najwa ta dauke kanta.

"Anty Zahra, dan Allah kizo inji mutumin jiya."
Murmushi Zahra tayi ta ce,

"Allah sarki yazo ashe."
Najwa ta kall ta ce,

"Sis taso muje."
Hararar ta Najwa tayi ta cigaba da karatun ta kawai.

Murmushi tayi, ta kalli yarinyar ta ce,
"Muje!"

Fita sukai Najwa na bin su da kallo da takaicin fitar Zahra.

Karatun ma kasawa tayi da kyar dai ta dawo da hankalin ta kan karatun ta.

Tana karasawa ya saki murmushi, gaishe shi tayi cikin girmamawa.

Amsawa yayi yana tambayar jikin Najwa.
"Jiki da sauki!"

"Tana ina ne?"
Ya tambaya.

"Zo mu karasa can."
Ta nuna wajen wasu bishiyoyi  da kujeru agun.

Can suka zauna. Kallon sa tayi ta ce,
"Bawan Allah a ina kasan mu da har kazo gare mu."

"Zan fada miki amman kada ki fadawa yar uwar ki."
"Saboda me?"

Ta tambaya cikin mamaki.
Murmushi yayi ya ce,
"Saboda ba yanzu nake son ta sani ba."Shikenan! Ina jin ka."
Kallon yayi ya ce,

"Sanin Najwa a guna abu ne da dade wanda zance na shekara uku da ganin ta. Abin mamaki kuma ba a garin nan ba."

Murmushi Zahra tayi ta ce,
"Ina ji."

"Na fara ganin Najwa ne a kano ta taso daga makaranta rike da hannun wata karamar yarinya. Abin alajabi kan nayo UTurned na zagayo har sun bace min."
Shiru yayi, ya cigaba da magana

"Ban taba soyayya ba wannan yasa na furtawa Mami mahaifiya ta. Ina fada mata ta ce, ai son ta nake abin ya bani mamaki dan a lokacin ban san so a rai na ba. Ashe so kan shiga ne ba sai an shirya masa ba."

Kallon Zahra yayi ya ce,
"Tin daga ranar kullum sai naje unguwar amman bana ganin ko me kama da ita.
Ganina na biyu da ita shine a Ado bayero mall shima kan na karasa wajen ta sun bar wajen.
Nasha wahala akan Najwa duk da ban santa ba."

Numfashi yaja ya ce,
"Tin lokacin ban kara ganin Najwa ba sai last year a garin nan. Kunje green house shima kuka guje min."

"Kinsan banyi wata da barin garin nan ba wajen neman ta, abinda ya dawo dani shima neman ta ne. Nayi addu'a sosai kafin na zo sai Allah ya amsa min addu'a ta. A ranar da na dira jiya  a ranar na ganku. Wannan yasa na biyo ku."

Kai Zahra ta jinjina tana tausaya masa.
"Ina son Najwa ba dan kyan ta ba. Haka kuma ba dan na santa ba. Allah shi ya daura min santa."

Nunfashi Zahra ta sauke ta ce,
"Najwa na da taurin kai Bawan Allah amman tana da saukin kai."

Murnushi yayi, ya ce,
"Sunana Najib."

"Ah kace Me sunan Yayan mu ne."
"Yanzu dai ina fatan Ba ta da wanda take so."

Kai ya gyada ta ce,
"Najwa bata kula kowa bare har taso wani. Duk yadda ake mata fada bataji indai akan samari ne."

"Alhamdulilah!"
Ya fada yana daga hannun sa sama.

Kallon sa tayi da alamar tambaya.
"Dole nayi Hamdala, saboda Allah naso na da har yasa Najwa bata kula samari bare taso wani a ciki."

"Kar ka fadi haka.  Dan kaima da wuya" ta kula ka. Jiya na mata maganar ka amman ko kala bata ce ba. Yanzu ma kaga taki ta fito."

Murmushi yayi ya ce,
"Ba komai yar uwa. Ya sunan ki."

"Sunana Zahra."
"Ke kanwar ta ce,"

"Ni Kanwar ta ce, mamana kanwar maman ta ce, a kano take tazo nan garin wajen Momyn mu ne."

"Allah sarki. Dan Allah ki tayani bata hakuri ta yadda mu hadu zuwa anjima zan dawo."

"Ba komai zan yi iya bakin kokari na dan na lura kai mutumin kirkine. Kuma Allah shi ya hada ka da Najwa insha Allahu zan baka ita."

"Nagode Zahra. Nagode Allah saka miki da alheri."
"Ameen Yayan mu."

"Kije kuci gaba da karatun sai anjima."
"Toh sai anjima."

Ta kamo dakin karatun nasu.
Najwa na ganin dawowar ta, ta sauke ajiyar zuciya.

Dan ita a tsorace take da ta fita. Hararar ta tayi kawai ta cigaba da karatun ta.


*INDABAWA*

Continue Reading

You'll Also Like

10.2K 591 13
Hamida was an ordinary girl trying to fit in, into the world entirely. after the death of her father, she and her mother moved in to stay with her Un...
45.2K 702 16
DELULU & GUILT PLEASURE
262K 10.8K 37
Complete story of a young girl Ummy.
1.5K 160 52
Rayuwar auren su abar kwatance ce. Soyayyar da sukewa junan su, mai girma ce. Tarbiyyar da sukayi wa yaransu mai kyau ce. Komai na Mukhtar da Hafsah...