NAJWA Complete ✔

By MSIndabawa

59.5K 4.5K 9

Najib yaron littafin bai dda buri da aaddu'a sai ta Allah yaya bashi mace ta gari mai ilimi Sumaiyya Yarinya... More

1-5
11-15
21-25
26-30
31-35
36-40
41-45
46-50
51-55
61-65
66-70
71-75
76-80
81-85
86-90
91-95
96-100
101-105
106
107-110
111
113
114
115
116
117
118
119
120
121
122
123
124
125
126
127
128
129
130
131
132
133
135
136
137
138
139
140
141
142
143
144
145
146
147
148
149
150
151
152
153
154
155
156
157
158
159
160
161
162
163
164
165
166
167
168
168 End

16-20

1.2K 87 0
By MSIndabawa

*NAJWA*


BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*


🌐HAJOW📝🌐

👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧 HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍🏾✍🏾✍🏾



PAGE *16-20*


DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

GODIYA MAI TARIN YAWA GARE KI. ALLAH YASA KI GAMA LAFIYA AMEEN.


MASOYA NAGA SAKON KU NAGODE ALLAH BAR KAUNA DA ZUMUNCI.

*AMEEN*






Tana shiga. Wata dattijuwa tayo gun ta.

Murmushi ta sakar mata. "Barka da fito wa Hajiya."
matar ta fada.

Murmushi Mami  tayi, ta durkusa tana gaishe ta.
"Baba ina kwana."

Tsohuwar matar ta ce,
"Lafiya lou. Dafatan kun tashi lafiya. Ya najibullahi."

"Ai daga rakiya nake. Ya dan makara shi yasa be shigo ba."
"Allah sarki bawan Allah kenan. Allah bada sa'a toh!"

"Ameen Baba. Me kuka yi na karyawa ne."
"Kunu da kosai."

"Baba ke dai bakya gajiya da kunu nan."
"Yo ai dashi muka saba Ki bazan tacin wannan dankalin ba. Ya sani basir. Su dai in suna so suna yi."

Mami tayi murmushi ta ce,
"To shikenan. Ina talle da Bara'atu."

"Suna can wai indimo zasu dafa."
"Baba kenan ke bakya ci."

"Ina ni ina abincin yara."
"To bari na shiga daga ciki. Daman gobe zamu tafi kano nida Najib. Shine nace bari na fada miki."

"To Allah ya kaimu goben."
"Ameen. sai anjima."

"To sai anjima."
Mami ta mike tayi ciki.

Wanka tayi sannan ta gyare gidan ta zauna cin abinci.

Karfe sha biyu nayi, sai ga kiran Dady nan. Sun jima suna hira sannan sukai sallama.

Kiran Najib ne ya kara shigowa.

"Son Ya akayi ne?"
"Na kira naji lafiyar ki."

"ina lafiya. Shine kabar aiki ka kira ni ko."
"A'ah Mami na gama aiki sai karfe biyu zamu shiga aiki kuma."

"Ok Allah bada nasara."
"Ameen""

"Kaci abinci dai ko?"
"Yanzu zan ci."

Mami ta bata fuska ta ce,
"Yanzu Son!"

Najib ya marairace. Kamar tana ganin sa. ya ce,
"Eh! Aiki ne ya hanani ci."

Mami ta dan saki fuskar ta, ta ce,
"Oh toh maza kaci kaji."
"To mami sai na dawo."

"A dawo lafiya!"
ta kashe wayar.

Kafin dai ya dawo sai da ya kira Mami sau uku. Bai shigo gida ba sai bayan sallah isha'i.

Dakin Mami ya shige da sallama. Amsa masa tayi tana daga kan sallaya.

Fuskar sa a shagwabe, ya c,
"Mami nagaji."

Harara sa tayi.

Murmushi yayi. ya ce,
"Mami sannu ya gida?"

"Lafiya! Ya aikin?"

Najib ya marairai ce fuska. ya ce,
"Aiki da wahala kiga fa Mami wai sai yanzu na shigo gida yau mutum uku mukayi wa aiki wallahi."

Murmushi Mami tayi, dan tana son yaron ta yana kwazo ba lalaci ba. Duk da tasan beda lalaci.

Tasan ya aikatu amman tana nuna masa kamar ve ba dan kar ya sangar ce da rashin son aikin.

"To Sannu kaji. Allah sa anyi a sa'a. Tashi ga ruwan zafi can, kaje ka gasa jikin ka."
"Toh!"

Ya fada yan cire kayan sa.

Bandakin ya shiga ya gasa jikin sa sannan ya fito. Mami bata dakin.

Mai ya sha a jikin sa ya saka kayan bacci riga da wando.

Kan gadon ta ya hau ya kwana. Bude dakin tayi ta shigo da katon faranti a hannu.

Mikewa yayi da sauri ya karbo mata. Ya ce,
"Sannu Mami. Yau ke kadai kikai girki."

"Yauwah. kuma kaga abincin ka nayi maka ba."

Ido ya bude, yana murmushi, "Wayoo dan Allah fa. Wanne daga ciki."

"Wanda kafi so."
"Wow Mami Allah saka miki da gidan aljanna."

Ya fada yana bude fulas din gaban sa.

Waina shinkafa masa ita ta bayyana. Murmushi yayi. Ya sumbaci mamin sa a kumatu.

Miyar ya bude, wani.kamshi ya daki hancin sa. Ido ya lumshe yana hadiyar yawo.

Miyar agushi tayi wacce ta zuba mata naman kasuwa sai kamshi ke tashi tayi kyau da ita.

Sai lemon karas da tayi wanda ta saka tufa da lemon tsami da madara ya dau sanyi.

Zuba musu yayi suka fara ci. Sai santi yake mata. Har Mami ta koshi shikuwa zurawa yake.

Ragowar ya saka a firij yace da safe zai ci. Mami sai dariya take masa.

"Son Allah ya baka wacce ta iya girki dai dan bakin nan naka ko!"
"Ameen! Mami na."

Dady ne ya kira. Kallon sa Mami tayi, ta ce,
"Nasa a speaker."

Najib ya bude ido, ya girgiza kai ya ce,
"A'ah ku gama gaisawar ku tukkuna."

Dariya tayi ta dauki wayar.

Sai da sukayi kus kus din su sannan ta bude a speaker suka fara hira gaba daya.

Sai da suka gama sannan sukayi sallama. brush Mami tayo ta canja kaya ta kwanta.

Sallama Najib yayi mata. Sannan ya tafi dakin sa.

Yana zuwa ragowar abubuwan da yake bukata ya diba ya hade su gaba daya.


Kamar ko yaushe biyar saura ya tashi yayi wanka ya zauna karatu sannan ya shiga dakin Mami ya ganta zaune akan sallaya tana ta zikiri.



*INDABAWA*

Continue Reading

You'll Also Like

68.3K 7.5K 58
Murmushi tayi mishi wanda ya tafi da imanin sa yayin da ta juya kallonta ga duɓɓin mutanen wajen. Dogayen yatsunta biyu wanda suka sha jan lalle ta b...
262K 10.8K 37
Complete story of a young girl Ummy.
908K 30.9K 110
When Grace returns home from college, it doesn't go like she thought it would. With her past still haunting her everyday choices, she discovers a sid...
45K 702 16
DELULU & GUILT PLEASURE