MASIFAFFAN NAMIJI..!

By JamilaUmar315

54.1K 4.3K 635

A mu"amalansa da kowa Sai son Barka....Kowa kuma zai iya Fadin kyakyawan Hallayarsa..Ammh ga Matarsa Hafsah b... More

01
002
008
009
012
010
011
013
014
015
016
017
018
027
03
019
020
021
022
023
033
024
036
025
026
04
034
028
029
005
030
031
032
037
038
06
035
040
039
007

FINALE

1.7K 104 16
By JamilaUmar315

*MASIFAFFAN NAMIJI..!*

*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty💞*

*Dedicated To:My Habibaty💞 Aisha Idris Abdullahi..*!

~Alhamdulillah...Dukkan Godiyata Ta Tabbata ga ALLAH shugaban Halittun Duniya...Salati Tare da Rahma Gafara Aminci Su Tabbata ga Annabin Rahma Annabi Muhammad Sallalahu alaihi wasallam Shida Iyalansa da Sahabansa gabadaya..~

*041*

Tunda Barkat ta Dawo Gidan bata kara yarda Tayi zaman Dakin data saba abaya ba,Tun Safe Zata Fito Bayan ta Gyara Dakunanta,Tafito tace Tana so Ta karbi Wani aikin ta Taya Hafsah ita kuma Hafsah sai taki Bata Daman Tun Dawowarta Tace mata Sai ta Haihu ta gama Jegonta kana zata bata Girki ammh Kwanan Miji yana nan ayadda yake in ya kwana Biyu Dakin Hafsah,Sai ya koma Dakin Barkat din ya kwana Biyu,Bai saka musu baki ba sai da Hafsah Ta nemi Daya koma kwana Dakin Barkat da kwana Gabadaya Saboda Tsohon Cikinta gashi kuma Haihuwan Fari kada wani Abu ya taso ba kowa a kusa Da ita.

Lokacin da Hafsah ke Fadamai Haka yana Zaune a kasan Cafet Dinta ne ya Tankwashe kafa yana Cin Tuwon Semo miyar kubewa Bushashiya wacce Hafsah Ta Dafamai Da Daddare,Ita kuma Tana Gefensa Zaune Rike da Noor tana bata Nono Amir da Amira kuma Suna Dakin Barkat tun Dazu Chan ma Sukayi Sallar mangariba Yanzu Chan suke zama Tunda Taja yaran ajiki Sosai.

Yana kai Lomar Tuwo bakinsa yana kallon Hafsah a karkace Gefe Daya na Cikin Zuciyarta Najin Haushin Shisshigin Hafsah na Wani Lokacin..Ina Ruwanta..? Waya aiketa Shiga Hurumin da ba nata ba bai gama mamaki ba ta katseshi da Fadin"Har ma Dazu nake ma Barkat din Zencen tadai Nuna min ba komai ammh ai nima Mace ne nasan Yanayin,kaga kuma Haihuwar Fari ce Gwara asamu wani kusa da ita Tunda bamu san Wani Yanayi Haihuwan zata zo Dashi ba Gashi kuma kai ba barinta Zakayi ta koma Gidan Gaban Hajiyarsu ta Haihu ba ko Zaka barta ne..?

Ta fada Tana kallonsa Mamaki ya kara kamashi bai samu Zarafin mgana ba sai da ya Koshi da Tuwon kana ya Ture Kololin gabansa yaja Roban Wanke Hannun Dake gabansa ya Wanke Tas ya saka Tissue ya Goge Bakinsa Tsaf kana yayi Gyatsa Lokaci Daya da Hamdala yana Fadin"Alhamdulillah..."

Yafada Lokaci Daya yana Mike kafa,Kansa ya jinginar kan Hannun Kujera Lokaci Daya yana Balle Botorin Rigan Shaddan Dake Jikinsa Dama Yana Shigowa da yunwa ya Dawo Abincin ya Fara ci kafin Wanka, Hafsah Ta Karkace kai Tana Fadin"Baka ce komai ba Abban Amira..Ina ta mgana..?

Waigowa yayi yana kallonta kafin yace"Na"am kika ce me..? Ban ji bane..! Ya fada yana Zabga Hamma Galala Hafsah Tayi Tana kallonsa Kafin tace"Kai Abban Amira yanzu Duk mganganun da nagama yi baka Jini ba..? Kai ya gyada mata yana Fadin"Ban ji ba sake maimaitawa.."Baki Hafsah kawai Ta Gimtse Ta Cigaba da Noor Nono ammh ta bata Ranta Sai Abun ya bamaa Abdullahi Dariya,Ganin yadda Hafsah Tasha kunu sai ya Matso Kusa da ita yana Fadin"Meye kuma na Fushi Hafsatun Abdullahi..? Uhmm gayamin yanzu ina Sauraranki kisan Dazu Ina cin Abinci Kuma kinga ba kyau ma kana Cin Abinci kana mgana..! Yafada yana Sosa Sajensa Cikin Dariyan Dayake ta Dannewa

Jin Haka yasa ta waigo ta kalleshi Tana Koramai Jawabin Da tayi mai Tun Farko,sai da takai aya kana ya Dage mata Gira yana Fadin"Duk wannan aikin waya saka ki ko waya aike ki..? Hafsah tace"Bangane waya aike ni ba Abban Amira gani nayi Hakan ne ya Dace kada ace mun kyaleta ita kadai.."Karamin Tsaki Yaja yana Fadin"Ace mana..Waya Damu..? wanda yaga an kyaleta yazo ya Taimaketa mana..ke banda ma Tsabar Saka ma kai Wahala da kuma aikata abu ba"a saka ka ba Ni kin yi mgana Dani nace Miki Eh na yarda..? Bafa ki min mgana ba ammh Har kinje kin ma  Barkat mgana,ai Tunda kinyi gaban Kanki kin kyauta ammh Nidai bada yawuna ba ban kuma amince ba..Raban kwana ne da kukayi zan Dinga kwana Bibbiyu dakin kowaccenku kamar yadda kuka Tsara Mganar kuma Wani Abu ya Faru Allah ke Tsarewa kuma ga waya Cikinmu Duk wanda ta Kira zai kai mata agaji,Bana son Mganar da bazata yuyu ba..!

Yafada yana Daure Fuska Kwabe Fuska Hafsah Tayi Tana Fadin"Haba Abban Amira...b..."Bana son Wani mgana Don Allah ina Ruwanki wai da ita..? Malama kiji da kanki kawai Mganar kuma ko zata koma Gida ne,ta Haihu ki Tambayeta indai tana son komawa Fine ni bani da Matsala...'Yafada yana Mikewa Cikin Mika Hafsah ta Bishi da kallo Ta kasa mgana kafin ta kada kai tace"Shikenan Tunda Haka kace...Ammh Ban ji Dadin yadda kamin Wannan Fahimtar ba.."

Shima kai Tsaye yace"Nima ban jin Dadin yadda kike yanke min Hukuncin batare da Sanina ba..Ki Tsaya iya matsayinki kawai malama mganar kuma Taya kwana nidai ga Abunda nace in kinga Zaki iya Taimakawa malama Hafsah sai Duk Ranar girkin ki ki Rika Tafiya Dakin Barkat kina Tayata kwana Fakat.."Da mamaki Hafsah Tace"Kai kuma fa..?

Yana Mirmishin Mugunta yace"Ina Inda ya Dace mana...Domin ba inda zani ki Tafi Dakin Wata Taya kishiya kwana Ki kwana Cikin Tsinuwan mala'iku Domin nidai bada yawuna aka Tafi ba Atoh.."Daga haka ya Shige Cikin Bedroom din yana ta Fada da kallo Hafsah ta Bishi kafin ta kadai kai ta Mike Tana Rike da Noor wacce tayi Barci Ciki ta Shiga Itama ta Shimfidar da Noor Daidai Lokacin da Abdullahi ya Leko Daga Ban Daki yana Fadin"Ina Ruwan zafin... ?ko baki saka bane naga Kittle din bakomai..!

Ko kallonsa Hafsah batayi ba Cikin Kufuluwa tace"Zan saka kenan suka Dauke Wuta...Sai dai in na Dafa maka a Gas.."Tafada tana kokarin Ficewa Daga Dakin,baki ya Rike yana Fadin"me yayi zafi..? Barshi zan yi da Ruwan sanyi ni ba bakon zafi bane..Ammh fa Dole akamin ba Daidai ba Zan Fada.."Yafada yana Komawa Cikin Toilet Din Lokaci Daya da Rufo Kofa Hafsah najinsa ta Fice tamai Banza Sanin Halinsa Tunda ya kuma Turtse Shikenan kuma.

Dakin Barkat ta Shiga ta iske Amir yayi Barci Amira ce Kadai Batayi ba Suna ta Hira da Barkat wacce Take zaune ga Katon Cikinta wanda yayi kasa alamun Haihuwa ko yau ko gobe,Sannu Hafsah Tayi mata kana ta kama Amir takai shi yayi Fitsari takai Daki ta kwanta kana ta Dawo tace Amira taje ta kwanta sai da Amiran ta Fita kana Hafsah tayi ma Barkat Zencen yadda sukayi da Abdullahi Mirmishi kawai Tayi kafin tace"Dama fa naji ki ne kawai Anty Hafsah..Bakomai kamar yadda yace ga waya In naji wani Abu zan Kira Insha Allahu.."

Hafsah dai Duk Taji kunya Ta Dade Dakin Barkat din Har wajen karfe goma kana ta mata sai da safe ta Fice zuwa Dakinta,Sai da ta kulle kofarta ta kashe Duka Wutan Dakunan ta leka Dakin Su Amira ta gyara musu kwanciya tayi musu addu"a kana ta Shiga Bedroom dinsu ta iske Abdullahi har yayi Barcinsa bai Jira ta ba Bata damu ba Tunda Itama Taji Haushin yadda ya Nuna mata iyakarta Ta Fada Tiolet tana Jin Takaichin Abun Har Cikin Ranta.

Shi kuwa Bangaran Abdullahi ya Yi ma Hafsah Hakane Domin ta Kiyayeshi,In yana kyaleta gaba Sai Ta Rika bashi ma Umarni yana Bi,wani Lokacin Wajen Tsausayinta Cutar dashi Take bata sani ba,Shiyasa ya Taka mata Burki Tun yanzu kafin abun yayi gaba kuma ya kasa Controlling din Abun.

Washegari Haka Hafsah tatashi Tana wannan Fushin Abdullahi kuwa bai bi ma ta kanta ba ya nuna mata ma bai san Tanayi ba Dole ta Tattara Fushinta ta watsar ta saki ammh Duk da Haka bata Dandara ba Ranar da Daddare bayan ya Daawo ta kara Zuwar mai da mganar Yayi ma Hajiyarsu Barkat mgana Ko Kanwarta Data Dawo Gida Aina Aba Barkat din ta zauna mata kafin ta Haihu Tunda ta Dawo Gida Ta gama Candy,Abun sai ya koma Bashi Dariya da Tsausayi da wani kaunar Hafsah Acikin Ranshi Yana Tunanin samun Mata masu irin Zuciyanta ba, sai an Tona bai mata gardama ba,Yace zuwa gobe zai je gidan yayi mgana da Hajiyan Amina Hafsah Taji Dadi Sosai Tayi tamai Godiya Shi kuma ya Fanshe da cewa Sai ta Bashi Tukwaici,hakanan ta Saki Jiki ta bashi Abunda yafi so aduk Duniya ya kwana yana Moran Abunsa.

Washegari bayan ya tashi Daga Wajen aiki ya Nufi Gidansu Barkat ya samu Hajiya Amina ya Roketa alfarman da basu aron Aina Saboda ta Rika Taimaka ma Barkat din,Hajiya Batayi Gardama ba ta amince Daman Barkat din na Ranta Bai baro Gidan ba sai da Aina ta Hada kayanta ya Daukota suka Taho Tare sai dai Barkat ta gansu kwatsam Tayi ta Murna tana ma Abdullahi Godiya yace ta Godema Hafsah Domin ita ta kawo Shawaran ya Dauko mata Aina Din Lokacin Daya Fada mata Haka taji wani iri Ammh sai ta Danne Bata nuna ba tabi Hafsah Har Daki Tayi mata Godiya ita kuma Sai ta nuna bata ji Dadin yadda Abdullahi ya Fadama Barkat din komai ba,Har sai da ta gayamai Cikin Gatse yace"Toh karya zan yi..? Ke fa kika Kawo Shawaran kuma nayi aiki da ita Banga wani Abun mgana ba Mata dai bakwa Raina Abun Tsegumi..! Jin yace Haka yasa ta kama bakinta ammh ta sani Har ga Allah ba macen da zata ji Dadin Irin Abunda Abdullahi yayi ace Mijinka bai da Tunanin Dauko wacce zata taimaka maka sai Kishiya ta Bada Shawara hakan bai Dace ba ammh Dayake Abdullahi Audu ne Dole ta kama Bakinta ita kanta Barkat bata isa ba Domin Yanzu lallabashi Take bata Fatan Abunda ya Faru da ita ya kara Faruwa akan wata ma bama ita ba.

****

Zuwan Aina da kwana Hudu Barkat ta Haihu,Wanda Haihuwar ta Rana ce,Ranar laraba Abdullahi baya Gidan yana Wajen aikinsa Hafsah ne kadai agidan sai Mariya Datazo sai Aina sai ita Barkat din Tun Safe ta Fara Jin Ciwon mara batayi mgana  ba sai da Abun yayi yawa Lokacin Har ma Ta Fara ganin wani Ruwa Ruwa na Binta,Sai ta kira Aina tace ta Kira mata Hafsah ita kuma Bayan ta Kirata Tazo tagani sai ta Fahimci Haihuwa ne Ta Daga waya ta Kira Mama ta gayamata ita kuma tace Gatanan zuwa.

Ba Dadewa sai ga Mama tazo Gidan da Farko Asibiti Hafsah tace su Tafi Har ta Hada kayan Haihuwan waje Daya sai dai kuma Allah ya kawo Abun da Sauki,Mama na zuwa Taga Haihuwan tazo Har Faya ta Fashe,Cikin kankanin Lokaci Mama ta Gyara ma Barkat din Kwanciya tana ce mata tayi Nishi Minti Talatin suka Dauka Barkat ta Haifi yarta mace Jajir da ita mai kama da Uwarta ta sak,Hafsah na Gefen Mama Duk da ita akayi Gumurzun Harda yi ma Barkat din kwallah Saboda Tsausayi Don ma Allah ya kawo mata da Sauki,Mariya dake Rike da Noor da Su Amira da Aina Suna Dakin Hafsah Cikin Zullumi Sai da sukaji Kukan Jaririya kana Suka Sauke Numfashi nan da nan Hafsah ta Fita ta Saka Ruwan zafi,Gefe Daya kuma ta Fito da kayan Jinin Da Barkat ta bata Duka ta wanke ta Shanya,Mama kuma ta juye Ruwa Ta wanke Jaririya Tas Hafsah ta Shiryata Cikin kayan Sanyi masu kyau Ruwan Zamzam kadai Hafsah ta bata Wanda take bama Noor Bayan nan kuma Mama ta Shiga da Barkat Bayi ta mata wanka ta gasa mata Jiki Sosai Gefe Daya kuma Ta Ganin kokarin Barkat Da bata nuna Raki ba ga kuma Saukin Allah a haihuwan Fari ko kari Barkat batayi ba,Wankan da Mama Tayi mata ko Hajiya Amina Abunda zata mata kenan ita kanta Barkat din ta sani Zuwa yammah Sun gama Gyara komai Daki sai Tashin kamshi Maijego na kame kan Gado Ta gama Shan Tea din da Hafsah ta Hada mata ta koma ta kwanta Tana Jin Zufa na yankoma ta Jaririya kuwa Tuni ta samu Barci Taji iskan Duniya.

Su Mariya kuma Suna waje Suna Girkin ganin aiki yayi ma Hafsah yawa,Allah yasa ma ga Mama,Kafin zuwa Dare Haihuwan Barkat ta isa kunnuwam Wadanda suka Kamata Bahiya da Bahijjat koda suka zo sun iske Hafsah Cikin yanayi mai kyau Suna ta mamaki nan take gaya musu Kokarin na Hafsah ne da Mama Su Subai da Zannira da Jidda Duk Mariya ta Kirasu ta Fada musu suka ce Allah ya Raya sai sunzo Abdullahi kuwa sai dai yaDawo Gida yaji kamshin Masu Jego Cikin mamakin komai Ya Shiga Dakin Barkat din ya Dauki Jaririyar yayi mata addu"a Da Huduba nan take ya Shaida Sunanta Habiba,Ita kuma Barkat din yayi mata sannu Mama kuwa nan take ta Kira Goggo Habiba ta mata albishir din tayi takwara Cikin Farinciki Tace Sai tazo Domin wannan Zuwan na Musamman ne.

Bahijjat ce ta kwana Bahiya Gida ta koma washegari sai gasu Matar yayansu Salisu da matan Wan Babansu,Ammi ma tazo Sai Dare Tatafi Tunda Mama na nan bata koma ba,Sai Washegari ta koma Gida Bayan Inna Talatu Tazo ta karbeta,Dama Ta Dawo Tunda Nazifin ya neman ma Jidda Nanny da zata Dinga kula da Zeezey din saboda karatunta.

Dangin barkat sai Godiya Suke na irin Hidiman da Hafsah da yan"uwan Abdullahi sukeyi kam Barkat din Hajiya Amina ma Ta Kira Mama tana ta Godiya,Subai ma tazo Tayi barka Hatta Jidda ma Tazo Ita da Zeezey dinta Data Fara wayau da Sakina,Zannira kuma tace sai Suna Hajiya Sa"a ma ta Leko Gida Dai kullum acike Inma Abu kam nan take wuni sai Dare take Tafiya Umman Sadiq dai ta Kira waya tayi ma Barkat din Barka Domin Bazata samu Zuwa ba tace,Sai ana Gobe Suna Abdullahi ya kai Barkat asibiti aka Dubata ita da Habiba wacce su Mariya suka ceza"a Rika ma alkunya da AYMANA..!

An Dubasu an Tabbatar da komai lafiya mangungunan karin Jini aka Rubuta ma Barkat Din,Suka Siya acikin Asibitin kafin Su Dawo Gida sai da ya ijiyesu gida kana Ya wuce wajen aiki,Sai zuwa yammah sai ga Auwal da kayan Abinci Niki Niki na Suna da Raguna guda Biyun inji Abdullahi,zannira ma alokacin Tazo Dama Subai Tana Gidam Ita dasu ya"yan Inna Abu kannen Nazifi,sai yan"uwan Barkat din Su Matar salisu da matan wan Babansu dasu Bahiya Sai Hafsah Da makotamsu aka Hadu ana ta Sha"ani Dinkin Suna Abdullahi ya kara musu Leshi da Atamfa ita da Barkat,Ranar suna Sai ga Goggo Habiba,Tun kuma Safe aka yanka Raguna Sukayi Abinci Kowa yayi wanka aka Sha Kwalliya anyi Hotuna Harda Kidan kwarya wanda Subai ta Buga su Mariya suka Chase,sai kuma Data gayyato mai Jego da Hafsah ta kida musu Kidan Kishinmata suka Rausayawa Abun sai wanda ya gani,Abdullahi dai gidan Mama ya koma kwana Dakin Auwal Nazifi kuma ya Tasashi Da Dariya Bai zo ba yadai aikoma da maijogo da Sako Shi da matansa washegari kuma Zuwa yammh kowa ya watse bayan Sun gama Soyensu suka Raba bayan Sun Tambayi Hafsah Tsarin Rabon ta gaya musu Harda Turmin Atamfa suka bama Mama da Inna Talatu Suna Godiya Domin Kowa yayi Bajinta su Subai su Zannira kowacce Tayi Turmi da Rigan yarinya Hafsah ma Haka Goggo Habiba ma Haka Abun sai wanda ya gani,Koda Abdullahi ya Dawo Gidan Haka Barkat din ta Dinga Nuna mai tana Nuna jin Dadinta Shima yaji Dadi Sosai Inna Talatu kuma Ta na nan Sai Barkat tayi kwana Ashirin zata koma Aina Ta koma Gidan Hakan ba karamin Dadi yayi ma Hajiya Amina ba ta Kira Mama Tana ta mata Godiyan Ranar kuma da tazo yi ma Barkat din Barka Har Dakin Hafsah din ta Shiga tana ta mata Godiya,Domin Barkat din da kanta tace ta Shiga Wajen Hafsah ta mata Godiya Ta tabbata samun kishiya irin ta sai An Tona tayi mata Abunda ko yar"uwanta sai Haka Shiyasa Tayi alkawarin Danne Duka kishinta kan Hafsah ta kuma Damaran koyon Duka Kyawawan Halayanta kodomin Rabauta anan Duniya da kuma Gobe kiyama.

Cikin kwamciyar Hankali Barkat ke jegonta gefe Daya kuma Inna Talatu na kula da ita Bata Tafi ba sai da Barkat Tayi kwana ashirin da Biyar kana ta koma Gida Da Sha Tara na arziki Daga Barkat da Abdullahi Harda Hafsah din ma Ita kanta Wanda takowani bangare take Shan Yabon Hatta ita kanta Barkat din Bakinta yanzu yabon kyawawan Hallayan Hafsah yake Fadi Domin Halin mutum Jarinsa.

****

*BAYAN SHEKARU BIYAR...*

Acikin wadanan Shekaru Biyar din da suka Gabata Abubuwa Dadama sun Faru masu Dadi da akasinsu Cikin masu Dadin Sune Harda kamallah Masters din Abdullahi,da kuma Samun Lecturing Da yayi A Federal Collage of Education FCE zaria,Shekaru Uku da suka Gabata da kuma Karin wani Farincikin ya kamallah Ginin Gidansa Tuni Sun Tare Wajen Shekara Hudu kenan da wani Abu Da Komawarsu sabon Gidan Tsohon Gidansa kuma ya barma Auwal wanda Har yayi Aure da Matarsa khadija suna Kiranta Dija Suna zaune agidan yagama Nd Dinsa ya Dora Hnd dinsa har ya kamallah ya samu aiki a NBYIS,mariya kuma Tuni tayi Auranta tana Auran wani Dan kasuwa akano aka kaita,Da komawarsu Sabon Gida Ba Dadewa Abdullahi ya mallaki Motan Hawa ya barma Auwal mashin Dinsa.

Babu Abunda  zai ce sai Godiya ga Allah Domin ta ko"ina ya samu Cigaban Rayuwa da Wadata a Halin yanzu ya kara zama magidanci Yayansa Kimanin su shida kenan Hafsah Bayan Noor ta kara Haihuwam mai Sunan Daddy Hamza Suna Kiransa Daddy,sai Barkat Datake da Guda Biyu,Ta Farkon mace ce mai Suna Habiba Suna Kiranta Aymana,sai Karamin Datake Shayarwa mai Suna Abubakar suna Kiranshi Abba,Gidan ya gama kamallah ta ko'ina Jidda ma ya"yanta uku Bayan Zeezey,takara Abdullahi Da kuma Abdul"aziz sai sakina nada Daya Mai Sunanta Aka maida Sakina suna Kiranta Namesake,Sai Hajiya Subai itama ya"yanta Shida yanzu Zannira kuma ta kai wajen bakwai Mama sai dai Godiyan Allah Domin Ta ko"ina Jikoki Sun Baibayeta,ga jin Dadin Rayuwa Data samu Bayan Mariya tayi Aure saboda zaman kadaici sai ta Dauko Diyar dan"uwanta Tana Rokonta kuma Abdullahi ya bata goyon Baya Sosai,Bangaran Su Inna Abu suma Abubuwa duk sun Sauya Tunda shi kanshi Nazifi ya koma Abuja da aikinsa Gabadayansa Shida iyalansa Sakina ta koma chan tana aikinta Ita da Jidda Barkat dai ta Gama Service ta karbi Resuilt Dinta ammh Aiki kam Abdullahi yace ba'a gidansa ba Dole ta Hakura Domin dai tasan Halin Abdullahi kaifi Dayane,Duk Hakurin Data Dauko ta yafama ksnta wani Lokacin gazawa take in Masifan Abdullahi ya tashi sai tace ma Hafsah Abdullahi sai ita,bata iyawa dashi itakuwa sai Tayi Dariya Domim ko Fushinsa ne ya Tashi da masifarsa Hafsah ce ke biyemai Tana Lallashi Barkat komawa take gefe  tana kallo Domin bata iya Jure wannan Hallayar na Abdullahi Duk da Tana Kishin Hafsah ammh ba kamar na Baya ba yanzu Kishin Tsabta suke yi acikin Gidan,Saboda duk iya Abunta bata kama kafar Hafsah ba Hakurinta Daga Allah ne.

Bangaransu Daddy da Ammi Suma Alhamdulillah sun samu Cigaba sosai Hankalinsu kwance Tunda Duka ya"yansu suna Gidan mazajensu Cikin kwanciyar Hankali,Hakama Gidansu Barkat Hajiya Amina Hankalinta ya kwanta Duka ya"yanta sunyi Aure Hatta da Aina Tayi Aure a kaduna,bangaran Su Umman Sadiq itama dai sai godiyar Allah Domin Har Makka Mijinsu yakaita ita da Abokiyar zamanta kannen Abdullahi Duk sun girma sun zama manya samari Ga Zahra ma an zama yan Mata,Goggo Habiba ma Tana Danja Itama Ita da ya"yanta da Mijinta Tana kuma Godema Abdullahi Domin bai manta da ita ba,Hajiya sa'a Tayi Aure Tana zaune agidanta Tagaji mutane nata mganar taki Aure tana zaman kanta Lariya ma ta kara Aure Ammh ita wani Soja ta aura tabi Mijinta Chan Lagos suna zaune sai kuwa indan sunzo ganin gida.

Mariya Ta na chan kano Tsohon Ciki Gareta ita da matar Auwal Ana ma Tunanin kusan Lokaci Daya zasu Haihu sai Shiri Su Hafsah suke Domin Sun yi alkawarin sai sunje kano Tunda sanda za"a kai Amarya Hafsah ce kadai Taje Barkat bata je ba Abdullahi ya Hana yace Shi ba mahaukaci bane da Zai saki mata Biyu alokaci Daya su Tafi kano kai Amarya.

*****

Wajen kwanansu Hudu,akano Suna Dagargazan Sunan Mariya Data Haifi yarta mace,Wacce taci Sunan mahaifiyar Mariyan Suwaiba,Dakyar Abdullahi ya barsu suka Taho sai da Mama ta saka baki ya barsu suka Tafi Chan suka bar Su Amira dasu Noor agida Hafsah ma agida ta bar Daddy Tunda ta yayeshi Barkat ne tazo da Abba,kwana Biyu yace suyi suka karyamai Doka kowacce ta Kashe wayarta suka Biye ma Subai,Daga gidan mariya Gidan Anty Hadiza suka yada Zango suka mata kwana Daya kama suka Dawo Gida koda suka Dawo Abdullahi baya Gida ya Shiga Cikin makaranta Su Amira kuma Suna gidan mama Suna da key din Gidan suka Bude suka Shiga Abunsu Barkat dai Sai Tsoro Take ji ita kuwa Hafsah Taci Dubu sai ceto ko ajikinta.

Sai Dare ya Dawo Gidan bayan ya Biya Gidan Mama ya Dauko su Amira Data zama yanmata Tana Jss1 ne Amir na Primary 5,yana Zuwa yaga sum Dawo Dukkansu Suna mai Sannu da zuwa yayi musu banza ya wuce Shashenshi Barkat da Hafsah suka kalli Juna Cikin Sarewa Barkat tace"Kinga wannan Fushin Wlh bazai sauka kaina ba..Sai da nace mu Dawo kika ji..Ki Kwashi Abincinsa ki kaimai Ciki kisha Fadanki ke kadai Nidai kinga Shigata Daki sai da Safe.."Hafsah na Dariya ta Rikota Tana Fadin"Allah baki isa ba..Tare mukayi laifin nan kuma Tare za"mu sha Fada nan.."Barkat ta bata Rai Tana Fadin"Bafa Ruwana laifinki ne.."Su ka kama Ja'in ja Har sai da sukaji gyaran Muryan Abdullahi saman kansu kana suka Natsu kallonsu yayi Dukkansu yaga suna wani karya wuya kamar munafukai sai Dariya ta kusa kamashi ya kanne Cikin Kakkausan Murya yace"Wato ma Tsabar kun Raina ni Da gangan kuka Share kafa kukayi zamanku ko..? Har kuna Kashe woyoyinku saboda kar Masifaffe Abdullahi ya Kira ko..?

Atare suka kwashi Rantsuwa ya Dakatar dasu yana Fadin"Hmmm..Ku kuka sani..Allah dai na ganinku..Fadan ne da aka min Tambari yau Bazan yi ba..Kun kyauta ba gashi kun Dawo ba Na zata Chan zaku Dauwama.."Sunne kai sukayi Suna Dariya Juyawa yayi yana Fadin"Abani Abinci ina Jin yunwa in kun kungama Gulmar taku..."Da Sauri Barkat tace"Toh Yallabai.."Lokaci Daya Suna Tafawa da Hafsah karaf kuwa Abdullahi ya waigo yana kallonsu sai Suka Fara kame kame Hafsah tace"Kinga kije ki Kwantar da Abba yayi barci ni bari naje na hadamai Abincin..'Barkat ta kama Hanyar Dakinta Tana Fadin"Tom Anty...!

Mirmishi Abdullahi ya saki kafin yace"Allah ya Shiryaku.."Yafada yana Shafa kanshi Su Amira Dake gefe suka Saka Dariya Hafsah ta Makamusu Harara tana Fadin"Kuwuce Shashenku marasa kunya.."Abdullahi yace"ji karfin Hali..? Ku kuyi ku Hana yara yi..? Kai kuce da karfi Allah ya Shirya Anty daMommy .."Suka ko wage baki suna Fada kunya ta kama Hafsah Ta juya zuwa Kitchen Barkat Daman Tuni ta Shige Dakinta Tana Dariya Abdullahi ya Bisu da kallo Shima yana Dariya Lokaci Daya ya Juya zuwa Shashensa yana Fadin.

*ALHAMDULILLAH...*

*Tammat Bihamdulillah...*

*Alhmadulillah anan na kawo karshen Wannan Labarin nawa na Masifaffan Namiji Abunda na Fada Daidai Allah ya bani ladansa  kuskuran Dake Ciki Allah ya yafemin...Ina godiya ga Mutane Dabam Dabam Masoyana wandanda suka yi Jimarin Bin wannan labarin nawa,Har zuwa yau da muka zo karshe Ina godiya ga Sauran groups Dina na WhatsApp Da wadanda nake Ciki da wadanda bana Ciki Nagode sosai da Salon Soyayyarku gareni Har gaban Abada bazan manta daku ba..Sai kuma Dubin gaisuwa da Godiya zuwa ga My Wattpadian pipu's Hakika nagani kuma na Yaba Tundaga Farkon fara wannan Labarin Kuke gudanar da kayattacen Sharhi  kuma Sharhi mai ma"ana wanda zai Taimake ku nima ya Taimakeni Wajen kara sanin Rayuwa da Zamantakewa Nagode sosai Allah ya saka muku da alheri Allah kuma ya baku ikon Daukan Duka Darussan dake Cikin wannan Rubutun nawa Ameen ya Allah..*

_Labarin nan ba Labarin Gaskiya bane Kirkiran Labari ne Wanda na Kirkireshi da Kwalwalwata Bawai nayi Dogon Tunani bane A"a Lokaci Daya naga ya Dace nayi Wannan Rubutun Kyauta ga Yanmatan mu Da Zawaranmu da Samarinmu da Uwargida da Amarya da Megida da ango da Amarya Saboda musan yadda zamu gyara mu"amalan Gidajen mazajenmu,Na samu Wayoyi da Dama da Sakona kan wasu Suna Fadin Labarin Hafsah yayi Daidai da Labarinsu Bla bla dai Toh Abunda nake so ku gane ga wannan Labarin Abu Daya ne Aure IBADA NE,kuma Aure HAKURI ne Jigonsa Duk macen Dake Tunanin bazatayi Zaman Hakuri agidan Mijinta ba Am Sorry To say haka zata tai ta Shiga Tana Fita Domin bazata Zauna ba Soyayyah Da kuke gani Duk awaje ne Gidan Aure ya Bambamta da zaman Gidan Iyaye Duk da Shima sai an yi Hakuri...Yan mata masu Shirin Shiga Gidan Miji Sai kun yi Hakuri Ga wacce zata Shiga ita Dayan da wacce Zataje ta Tarar ku Tuna Hakuri Shine Ginshikin Inda kika Rasashi Kin Rasa Dukkan Wani Jigon Zaman Aure Kana kada ku manta IBADA kuke je yi kuma zaman Ibada zaman Hakuri ne Allah ya bamu Ikon Hakurin Allah kuma yasa Mu zama Mataye na Gari ga Mazajenmu Nan Duniya da Gobe Kiyama Ameen.._

_*Bazan Rufe Littafin nan ba Batare da na Mika sakon Godiyata ga Wasu mutane masu Muhimmanci Arayuwata Guda Biyu ba na Farko Sisinah AISHA ALTO,hakika ke din Ta Dabamce awajen Jamila ina kaunarki Har Cikin Raina Sisinah,Da Taimakonki wannan Littafin ya kamallah kin Taimaka Wajen kokarin Posting Dinshi Nagode Sosai Allah ya saka miki da Gidan Aljannah Firdausi Allah ya Jibanci Lamarinki Allah ya sa ki gama Da Duniya Lafiya Allah ya baki miji na gari Allah ya kareki Daga Dukkan Sharri Allah ya barmu Tare..Sai Uwata Ta kaina Ni Daya Ummina KHADIJA SALISU YUSUF uwata Alherin Allah yakai miki Har gadon Barcinki Kyawawan Hallayanki Abun koyi ne garemu Allah ya Biyaki da Gidan Aljannah Firdausi Allah ya Shayar Dake Ruwa Daga Cikin Ruwan na ALKAUSAR Ameen*_

*Sai Allah ya kaimu Bayan Sallah In da Rabon mu sake Haduwa Cikin Wani littafin Batin Tunda naga Shi kuka fi so Ammh fa Banyi Alkawari ba...Har yanzu ana Cigaba da payment kan Littafin Ra"ayi ne ko Buri..? Kan Farashi mai Sauki mai Neman karin Bayani sai ya Tuntubani ta wannan Layin Insha Allahu 09069067488...*

Tanque All....And god bless u Alwys and Forever Fans❤️

*Janafty...*
*Shakira..*
*Anitha..*
*Jamilaumar*
*Intelligent Writer"s asso..*

Continue Reading

You'll Also Like

1.1M 66.8K 58
သူ႕နာမည္က ' ေတာ္၀င္မင္းခက္ထန္ ' တဲ့... ကြၽန္ေတာ့္ရဲ႕ ခက္ထန္ ၊ ကြၽန္ေတာ့္ကို မုန္းတဲ့ခက္ထန္ ၊ ကြၽန္ေတာ့္ကို ေျမႀကီးေပၚက သဲမႈန္႔ေလးလို စုပ္ေခ် ဖ်က္စီးပ...
125K 5.8K 174
Bota e Mafies është një botë e errët ku jo të gjithë zgjedhin të jenë pjesë e saj. Ajo nuk kishte zgjedhur të ishte pjesë e asaj bote...ishte fati q...
81.6K 11.2K 78
Author - 麟潜 (Lin Qian). Bai Chu Nian x Lan Bo 白楚年×兰波 Original Title - 人鱼陷落 / ရန်ယွီရှန့်လော့ Eng Title - The Fallen Merman / Preference of Poseid...