MASIFAFFAN NAMIJI..!

Galing kay JamilaUmar315

54.1K 4.3K 635

A mu"amalansa da kowa Sai son Barka....Kowa kuma zai iya Fadin kyakyawan Hallayarsa..Ammh ga Matarsa Hafsah b... Higit pa

01
002
008
009
012
010
011
013
014
015
016
017
018
027
03
019
020
021
022
033
024
036
025
026
04
034
028
029
005
030
031
032
037
038
06
035
040
039
FINALE
007

023

930 84 11
Galing kay JamilaUmar315

*MASIFAFFAN NAMIJI..!*

*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty💞*

*Dedicated To:My Habibaty💞 Aisha Idris Abdullahi..*!

*Intelligent writer' asso...*

*023*


"Haka Abdullahi yajema Hafsah Cikin Wannan Farincikin Wanda ya kasa Boyuwa Daga saman Fuskarsa,Tayi ta mamaki ganin Wannan Fara"a kamar me,Data Tambayeshi sai yace mata Bakomai koma miye zata ji Daga Baya.

Su Amira kuwa Auwal ya Dawo Dasu Bayan ya Dawo Daga Shago,Shi Abdullahi yama Manta Dasu ya Taho Shi kuma yana Dawowa Shago Mama tace ya Daukesu Amira ya kaisu Gida,ya Dade sai Wajen goma yayi musu sallama ya koma Gida Bayan yayi Dinner dinsa anan Suna ta Hira da Hafsah Abdullahi ko yana Ciki ya kwanta gajiya ta Saka Barci ya Daukesa da wuri.

Washegari Inna Abu ta kasa Zama sai da ta Shiga gidan Mama ta Fara Zegunta mata Hakika Mama tayi murna ammh acikin Ranta Tana Tunanin Jidda ne,ganin ai babu Soyayyah Tsakanin Nazifin da Jidda Tayaya wannan Halin zai yuyu,Koda yake Abdullahi ne in yace Eh din ne baya iya Sauyashi Duk Rigimar Jidda sai dai tayi Hakuri kawai.

Da Mama Taji Labari sai tayi Gum da Bakinta Tunda Abdullahin bai gayamata ba,Sai da ya taso Daga aiki,kana ya Biyo ya Kira Mama Cikin Dakin Auwal ya Gayamata komai Mama tayi Shuru kafin tace"Naji Dadin wannan mganar Domin Nazifi mutumin kirki ne,Ammh kana ganin Shi Nazifin zai so Jidda Har suyi zaman Aure..?

Abdullahi yace"Karki Damu da wannan Mama Abokina ya Tabbatarmin da Cewa Yana son Jidda Tsakani ga Allah kuma so na Aure.."Mama tace"Toh ita Jiddan Fa..? Zata so shi kuwa..? Kaga fa har yanzu Jidda Yarinya ce.."Abdullahi yace"Haba Mama Kina Wani mganar yarinya A yarinyar take Abunda ko Babban Albarka Ban damu Da tana son Shi ko Bata Sonshi ba nidai Hakkina na matsayin Babban Wa gareta Shine na Nema mata Gidan zama na Har Abada,ita ta isa tace bata son Nazifi ne..?dame tafishi...? Wlh shi ba ajinta bane sai dai kawai al"amarin Aure Ya gaji haka.."

Mama ta Rausayar Dakai Tana Fadin"Shikenan...Allah ya Sanya alheri ya Shige mana Gaba.."Yace"Ameen Na riga na Barma Baba wada wuka Da nama kan mganar Saboda haka zan Kira Zannira da Subai suzo gida muyi mgana inaso ayi komai Cikin Lokaci ne Mama.."Mama tace"Ya kamata..ammh Ya za"ayi zaka karbi Lambar Hajiya Sa"a ne ka Sanar da ita ko yaya..?

Cikin Mamaki yace"Wata Hajiya Sa"an..?Mama tace"Mahaifiyar Jidda mana.."Karamin Tsaki yaja kafin yace"Ni ba wacce zan Kira Mama..Yarta ta gayamata ko ke..! Jidda kuma gobe Ki Turomin ita Gidana Ta kwana zan sanar da ita Zuwa asabar ko Lahadi kuma Nazifi zai Shigo su gana in Allah ya kaimu.."Mama tace"Hakan ya kamata Allah ya nuna mana..ya kuma Sanya alheri.."ya amsa da Ameen da haka ya mata Sallama ya Fice Daga gidan..

Daga Mariya Har Jidda ba wacce ta kawo Tunanin komai acikin Ranta,Zannira da Subai"atu sum Ji mamaki kiran da Abdullahi yayi musu da kanshi yace in sun samu Dama Cikin Satinan su Shigo yana son mgana dasu sai Zannira Tace sai Dai Ranar sati Saboda karatun yara Shima Abdullahin yace Hakan yayi Saboda Office Ranar duk da yana da Karatu a Abu in ya Dawo sai Su Hadu gidan Mama.

Kowacce ta kira yar"uwanta Tana Fadamata Kiran ya Abdullahi suna Hasashen Allah sa Lafiya,Koda suka Kira Mama kin Fada musu tayi tace Bata sani ba,Mama bata samu Tura Jidda ba sai Ranar Laraba da yammah Tace ta Shirya Tatafi gidan Abdullahi ta kwana da safe sai ta Dawo Tun da Taji haka sai tasha Jinin Jikinta Tana Tsaye a tsakar gida Tana Ninke kayan Mama Data wanke mata a kan igiya,Mariya kuma tana gefe kan Tarbama ta baje littafai Tana karatu,Mama kuma na Daga kofar Kitchen tana Tsinkan allaiyahu Zata saka Cikin Miyar Taushan da zatayi.

Jin Abunda Mama tace ne yasa Daga Jidda Har mariya suka Dakata da Abunda suke suka Dago suka kallonta Gabadayansu Cikin Mamaki Jidda tace"Mama gidan ya Abdullahi kuma..? Har na kwana..? Lafiya..?

Mama tace"Lafiya lau..yayanku yace na Tura mishi ke.."Jidda ta kwalalo ido Tana Fadin"Ni kuma Mama..?me nayi..? Mama Tace"Ni bai ce min wani laifi kikamai ba,Abunda na sani Shine yace ki Shirya kije ki kwana chan gobe da Safe sai ki Dawo.."Mariya tayi karaf tace"Kin Shiga uku Jidda..Ki Fara maimaita Lahaula walakuwwatu Tun yanzu.."Dakuwa Mama ta Sakar mata Tana Fadin""kaniyarki..Hala mala"ikan Mutuwa ne.."? Mariya na Dariya tace"Ko ba mala"ikan mutuwa bane Mama kiran ya Abdullahi ai ba alheri bane.."Mama ta Rike Tana Fadin"Haka kikace ko Mariya..? Tabbas kuwa zan gayamai.."

Jin Haka yasa Hankalin Mariya ya tashi ta Fara ma Mama magiyan ta Taimaka mata Karta Fadama Ya Abdullahi ita kuma Tana kara Tsoratata da sai ta Fada Jidda kuwa Fuskarta sam ba Walwala gabanta kuwa sai Fadi yake gaskiyan mariya ne Kiran ya Abdullahi Wlh D'aidai ku ne  na alheri kai bayama kiran mutun sai in wani Abu babba ya taso,gashi Mommy ta mata waya Tana nan Zuwa Cikin Sanyin Gwiwa ta kalli mama Tana Fadin"Mama gashi kuma Mommy ta Kira ni tace zata zo...ko zan Bari sai da Safe ne..?

Mama Tace"A"a da safe baya gida yana Wajen aiki..Yanzu ya kamata Kije ba Dadewa zai Dawo Daga wajen aiki..Hajiya Sa"a kuma sai ki Kirata ki gayamata Uzurin daya Taso.."Ba haka Ran Jidda yaso ba Jiki ba Dadi ta Shige Daki Dauke da kayan Mama Mariya ta Bita da Dariya Itama Jin Mama tace wasa take bazata Fadamai ba kana ta Saki Ranta.

Bayan Sallar mangariba Jidda tatafi Mariya ta Rakata ta Hau Mashin sai dai Hafsah ta ganta kamar Daga sama su Amira suka makalkaleta Suna Murnan ganinta Cikin mamaki Hafsah ta Fito Daga Cikin Bedroom dinta idar da sallanta kenan Taji ihun su Amira ganin Jidda yasa ta Bude Baki Tana Fadin"Jidda kece Tafe yanzu da mangariban nan..?

Jidda na zama kan Daya Daga Cikin Kujerun Falon Tana Fadin"Eh Wlh Anty Hafsah ina Wuni yasu Amira..? Ta Fada Tana Daga Amir wanda ke Tsalle kan Jikinta Gefenta Hafsah ta zauna Tana Fadin"Lafiya lau yasu Mama..? Ina mariya da su Auwal..?

Jidda tace"Duk suna Lafiya..Mama tace agaidaki.."Hafsah tace'Ina amsawa..Lafiya kuwa naganki da Dadaddaran nan Jidda..? Jidda tace"Lafiya lau....ai Yaya Abdullahi yace nazo gida na Sameshi yana Nemana.."Cike da Mamaki Hafsah tace"Ok..gashi bai Dawo Daga wajen aiki ba gaskiya.."Jidda tace"Eh yace ne na Jirashi.."Hafsah tace"Au Toh..ammh Tafiya ba yau ba sai dai gobe domin ai Dare yayi.."Kai Jidda ta Sunkuyar Tana Fadin"Eh Haka yace sai gobe zan koma.."

Cikin Dariya Hafsah tace"Dakyau mijin Hafsatu gashi yau ya kawomin ke.."Itama Jiddan Dariyan Tayi Daidai Lokacin da wayarta Dake Hannunta Ta Dauki Kara Tana Dubawa Taga Mommy ne sai ta Dauka Tana Fadin"Hello Mommy..."

Jin Haka yasa Hafsah mikewa Ta Fita zuwa Kitchen,ta Duba miyarta in ta karisa ta Sauke,Tuwon Semo tayi da Miyar kubewa Danya wacce Taji Kifi Ta Gama Tuwon Tun dazu ta Nannadeshi Cikin leda Kubewar ne bata karisa ba,Koda taje har ta karisa ta Sauke ta samu karamar Kula ta Zubama Mai gayyah mai aiki Nashi,sai kuma ta samu Filet ta Zuboma Su Amira Nasu Saboda ya Huce,Jidda kuma bata sa mata ba, ta bari ta saka da kanta Tunda Gidan ba bakonta bane ita kuma Batama jin Tana Sha"awar Cin wani abu Haka kurum Cikinta Duk ya Tushe..

Dakin Ta Dawo Har Jidda Ta gama wayar dama kafin ta Fito Gida ta Kirata da Niyyar ta Fadamata Fitarta sai bata Daga ba Shine yanzu tabiyo bayan Kiran Nan take Sanar da ita Tana Gidan Ya Abdullahi nan zata kwana sai gobe Itama Hajiya sa"a sai tace mata Tana ma Kaduna kuma ba yau zata dawo ba,kuma ba gobe indai ta Dawo zata Shigo ,Da haka suka Yanke kiran.

Hafsah tace ma Jidda In zataci Tuwo Ta Shiga kitchen Ta Duba Zazzabi take ji yana neman kamata Kayan abincin Abdullahi ma Dakyar ta iya Jeramai Bisa Cafet nan Gefe Jidda ma ta kama mata,kan kujera ta koma ta Nade Tana kallon Jidda na cin Tuwon Ita Dasu Amira suna Damunta da mgana itama tana Biye musu Duk da bata da Hayaniya tafi mariya son yara.

Kiran Sallar Isha"i ya Tashi Hafsat taShiga Bedroom ta Kabbarta  sallah Dama tana da alwala ita kuma Jidda suna gama Cin abinci ta kwashe komai takai kitchen Ta share Saman Cafet din ta Goge inda su Amira suka Bata da Miya Tajasu zuwa waje sukayi alwala anan Falo Ta Shimfida musu Sallaya sukayi Sallar sun Idar kenan sukaji alamun Bude Kofa da Shigowar mashin da gudu su Amira suka Fita Suna Murnan oyoyo Abba Su suka Tarbesa,ledojin hannunsa ya mika ma Amira Karamar Jakarsa kuma Amira ta karba Shi kuma sai ya karisa shiga d mashin Dinsa ma"ajiyarta.

Yana Dauke da Amir a kafadansa Amira kuma yana Rike da Hannunta ya yo sallama ya Shigo Dakin Jidda Dake ninke sallayar da sukayi Salla dashi,Lokaci Daya Tana amsa Sallaman nasa Kallonta yayi kafin yayi magana Tayi Saurin Cewa"Sannu da zuwa ya Abdullahi.."

Yana zama Kan Daya Daga Cikin kujerun Falon yake amsa mata,Fuskarsa ba walwala Cikin waige waige yace"Ina Hafsah din..? Kan jidda na kasa Tace"Tana Ciki..Bata jin Dadi ne inaga Domin tace min tana jin zazzabi.."Cikin Damuwa ya mike Lokaci Daya yana Sauke Amir Dake kan Jikinsa yana Fadin"Subhanallah...Tun yaushe..?

Jidda tace"Bansani ba Wlh..Nima ban jima da zuwa ba..."Kai ya kada yana Fadin"ok..Tafi dasu Amira ki karbi ledojin Hannunsu kayan Lambu ne sai kaza ki Dibar muku Sauran ki saka Cikin Fridge din Tunda Hafsah bata jin Dadi.."Kai ta gyada kafin tace"Kai bazaka ci ba..? Da sauri yace"No am ok...Amira kuje wajen Anty Jidda ko..? Yafada yana Tura Mata su da gudu suka nufeta da ledojin ta karba ta jasu zuwa Kitchen Shi kuma ya Shiga Cikin Bedroom din nan ya iske Hafsah kwance Inda Tayi sallah ta Dunkule Cikin Hijabinta a saman Kanta ya Duka yana Kiran Sunanta Cikin Galabaitan zazzabi Ta Dago Tana kallonsa Cikin Tsausayinta yace"Hafsah baki da lafiya Shine baki Kirani kin Fadamin ba..?

Kokarin mikewa take yayi Saurin Rikota da Jikinsa ta jingina Goshinta ya Shafa yaji Zafi Rau,Saurin Dauke Hannunsa yayi Lokaci Daya yana Fadin"Kai kinji Zafin Jikinki..? Tashi maza muje asibiti Fever kike yi Sosai kila maleria ce.."Ya fada yana Shirin mikar da ita Hannunsa ta Riko Cikin Sanyin murya tace"A"a yanzu ka Dawo kana Bukatar Hutawa..karka damu Zazzabi ne kawai Bani panadol nasha nasan zai Fada Insha Allahu.."Tafada tana Kallonsa Bata Rai yayi yana Fadin"Wannan wata irin mgana ce..? Lafiyarki batafin mun komai ba Hafsah taya zan barki Cikin wannan Halin.."Kan Cinyarsa ta Maida kanta tana Fadin"Ba wani Ciwo bane Sosai..Don Allah kadaina Damuwa.."Sai Tsausayinta ya kamashi ya kamata ya Rumgume kawai yana Sauke Numfashi,Da ita ajikinsa ya mike ya maida ta kan Gado Drower din gadon ya Bude ya Dauko panadol ya ballamata Guda Biyu,Har zai mikamata sai kuma ya kalleta yana Fadin"Kinci wani abu..?

Kai ta girgiza Tana Fadin"A"a bana jin Cin komai bakina bayamin Dadi.."Maganin ya ijiye kawai ya Fice Jidda na kitchen din Ya Shigo Filet yace ta samu ta Debomai kayan marmarin,Da sauri ta Samu Filet din ta Zubamai ya karba da Ruwa ya koma Ciki Dakyar da lallashi Hafsah taci kadan tasha mgani kana ya kwantar da ita ya kunna mata Fanka,Ganin ta Fara zufa yasa ya Cire mata Hijabin jikinta ya barta Daga ita sai Doguwar Rigar Dake Jikinta ya Dade Tsaye kanta Sai da yaga ta samu Barci kana ya Shiga yayi wanka ya Sauya kaya zuwa Jallabiya koda ya Fito Falo Har Su Amira Sunyi Barci Umartan Jidda yayi da ta kaisu wajem kwanciyarsu tazo yana son mgana da ita cikin Fargaba ta kwashe su zuwa wajen kwanciyarsu ta Dawo yana Saman kujera ya koma kasa ya zauna yace ta Jawomai kulan Abincinsa da Hanzari ta mike ta Kaimai komai gabansa ya Bubbude Tuwon kuwa yaci Da yawa yana ci ammah Rabin Hankalinsa na Wajen Hafsah yafi kowa sanin Halinta in tana Ciwo haka take bata san Ta nuna mai wani Abu na Damunta saboda kar ya Shiga Damuwa sai Ciwon ya kaita kasa kana take yarda yakai ta asibiti,Ammh yanzu bazai Kyaleta ba Zuwa gobe in yaga Zazzabin bai Sauka ba zai Dauketa suje asibiti adubata abata magunguna.

Jidda kuwa na gefe Rakube har ya gama cin abinci kala bai ce mata ba Tashi yayi yana Fadin"Ke Dauke wadanan kwanukan ki maida kitchen Ki Dawo.."Da Hanzari ta mike tayi kamar yadda yace Shi kuma Bedroom din ya koma ya Shiga Tailet ya wanko Hannunsa yazo ya kara Duba Hafsah ganin kamar Zazzabin ya sauka ne yasa ya Rage mata Gudun Fankan ya Rufa mata Blanket Daidai Kafarta Zuwa saman Cikinta kana ya kashe mata Wutar Dakin ya Fito.

Inda Jidda Tatashi nan ya Isketa Zama yayi kan kujeran Dake Fuskartata Lokaci Daya ya Kiran Sunanta.."Hauwa"u..."! cikin mamaki Ta dago Tana kallonsa Lokaci Daya tana Fadin"Na"am Cikin mamaki Sanin ba kasafai ya Cika Kiran Sunanta ba,Zama ya gyara yana Cigaba da Fadin"Nasan baki san Dalilin Daya sa Nace Mama ta Turo min ke ba ko..? Da kai ta amsashi bai bata Zarafin mgana ba ya Cigaba da Fadin"Very good..Ba wani Dalili bane mai karfi..Ko nace ba laifi kikayi ba Na ce ta turomin ke ne Saboda bana samun Lokacin kaina In na taso Daga wajen aiki wani Lokacin bana samun Tsaya agida a nan kuma zam samu Lokacin da zan miki Bayani Sosai yadda zaki Fahimta Dama ba wani abu bane..Mganar Auranki ce Tataso.."

Dam! Gabanta ya Fadi da Sauri ta Dago Tana Kallonsa Cikin kwalalo Ido waje tace"Mganar Aure kuma Ya Abdullahi..? Wlh Allah na Daina kula kowa Kama Tambayi Mama ko Anty Mariya kaji.."Tafada idanuwanta suna Cika da kwallah kallonta yayi kai Tsaye kafin yace"Wayace Dama kina kula wani..? Ki Saurareni Dakyau...abokina Nazifi yamin mganar yana Sonki kuma so na Aure ni kuma na bashi har ma yayi ma Baba wada mgana Bana son mganar ta Dau Lokaci na Farko ke yarinya ce Wacce kika kasance amana gareni Babban Burina da Fatana ki samu miji na gari Dake da mariya kamar yadda Sauran yan'uwanku Suka samu...Ba Domin Nazifi yana abokina Zan yabeshi ba A"a sai Domin ya Chanchanta kuma ya Dace Da Duk yarinyar daya Nuna yana so abashi saboda bashi da wani makusa atare Dashi,kana Abu na gaba zai kula Dake kamar yadda ni zan kula Dake saboda Haka na Riga na Furtamai na bashi ke,Ranar Lahadi zai zo ku ga Juna kuyi mgana mganar karatunki kuma karki Damu zaki cigaba adakinki in dan Har Shi Nazifin ya Amince miki.."Tun sadda ya Fara mgana Jidda ke Tsiyayan Hawayen Tsausayin kanta Sadda ya Furta Sunan Nazifi sai da kirjinta ya Shiga Bugwa Taya ya ma za"a ce Zata Auri Ya Nazifi wanda take gani kamar ya Abdullahi Alhalin ga mariya wacce ke gabanta ba"a ce ita ba sai ita Karamarta  da ita za"a aura mata Abokin yayanta kuma ma bama Saurayi ba mai Mata,gashi Tana da Burin yin karatu mai zurfi Burin Mamarta ne wacce tace zata nema mata ko Base University Abuja ko Maryam Abacha,gashi Lokaci Daya wannan mafarkin nata na Neman Rushewa Tuna,hakan Datayi yasa ta kara Volume din kukanta Baki Abdullahi ya saki yana Kallonta kafin yace"Ke lafiya kika Tasani kina min wannan kukan..?ko na Dake ki ne..?

Kai ta girgiza Cikin kuka Take Fadin"Ni bana son Shi Yaya Kuma nayi karama da Aure..Ga Anty mariya nan."Ransa ya baci yakai mata Dakuwa yana Fadin"kinga naki nan da baki Sonshi..? Dama wayace ki Soshi..? finshi kikayi..? Me kike dashi da Naazifi zai ce yana Sonki..? Baki da komai Wlh Domin yafi karfinki nesa ba kusa ba..Balle ki Bude baki ki gayama Mutane mganar banza kuma ai yafi ki sanin mariyan kuma yace ke Saboda Haka mgana Babu fashi ki zama Cikin Shiri xai zo ku gana Kuma Wlh in naji wani Rashin Mutumci ya Fito Daga barayinki kinsan Allah Dakaki zanyi Da sai kin gane Ni ba sa"an wasanki bane Tashi ki bani waje sakarya kawai mara wayau.."Jidda da kuka ya gama Cinta ta mike tana Rangajin kuka ta Fada Dakin su Amira kan Katifarsu ta Fada Lokaci Daya Ta saki Volume din kukanta Kamar wata Karamar yarinya.

Hafsah dake Tsaye kofar Bedroom dinsu Tana Cikin Barci Taji kukan Jidda da Sauri ta Farka ta Sauko Daga kan gadon ta Fito Falo Daidai Lokacin da Jidda ke Shigewa Dakinsu Amira Da mamaki ta kariso Kujeran da Abdullahi yake ta Zauna tana Fadin"Wai lafiya Abban Amira.? Meya faru naga Jidda na kuka..?

Kallonta yayi Lokaci Daya yana Taba Goshinta Jin Sanyi kalau yasa yayi ajiyar zuciya yana Fadin"Zazzabin ya sauka ko Hausina..?

Kai ta gyada mai tana Tsareshi Da manyan Idanuwanta Cikin Sanyin Murya tace"Meya faru..? Kansa ya Lamgwabar kan kafadarta Yana Fadin"Bafa wani abu bane...Iskanci ne kawai da samun waje wai kuka take saboda Nazifi yace yana Sonta ni kuma na Bashi,daga cewa Ranar lahadi zai zo suyi mgana Shine ta sakamin kuka Hardacemin bata isa Aure ba ga Mariya nan ba.? Ido Hafsah ta waro Tana Fadin"Wani Nazifin..?

Abdullahi ya Dago yana Fadin"Wanda kika sani Mijin Sakina.."Baki Hafsah ta Rike tana Fadin"Wai da gaske kake yace yana son Jidda.."? Mikewa Abdullahi yayi yana Fadin"Mun taba irin wannan wasan dake..? Har Baba wada ma yagamawa kuma ya nuna Murnan sa Sosai Yace baya bukatar jan Lokaci so ku Shirya nan da wata uku Insha Allah komai zai kamallah indai na isa da Jidda To na Bama Nazifi ita Amatsayin mata har Abada.."

Kai Hafsah ta Jinjina tana Fadin'Ikon Allah...Matar mutum kabarinsa..Allah ya sanya alheri..ya sakina taji..? Ko bai yagamata ba.? Hannu ya mikamata ta mikomai ya kamata tatashi yana Fadin"Kai mata abarku da gulma ni kuwa ina Ruwana..Ban sani ba ban kuma Tambayeshi ba kuma bai gayamin ba"Dariya ya kama Hafsah,Sai da ta Dara shima Abdullahim mirmishin yake Cikin Bedroom din ya maidata ya kwantar kana ya Fito waje ya kulle Kitchen ya dawo ya Kulle Kofar Falon ya Shiga Dakinsu Amira Har yanzu kuka Jidda Take Abun ma sai ya bashi Dariya Da mamaki yace"Lalle aiki ya sameki Cigaba da kuka...lalle kuwa in akan wannan mganar ne kukanki  bazai kare ba.."Daga haka ya kashe musu Wutar Dakin ya Fito ya kashe na Falo ya koma Cikin Daki ya iske Hafsah ta Shiga tayi wanka ta Fito Shi ya taimaka mata ta Saka kayan Barci ya Dauketa Cak suka Dira kan gado tana Cikin Jikinsa Ya kamkameta suke ta Fira yana gayamata irin Farincikin Dayaji Lokacin da Nazifin ya nuna yana son Jidda Hafsah kuma tana bashi Wasu Shawarwarin yadda komai zai tafi Daidai.

*****

Washegari Koda Jidda tatashi Idanuwanta sun kumbura saboda kuka Hafsah kuma Taji Sauki Sosai kamar ba ita ba,Abdullahi kuwa ko ta kan Jidda bai bi yau din da wuri ya Fita su Amira ma mai mashin dinsu ya kira yazo ya kaisu Bayan Tafiyarsu ne Hafsah ta Zaunar da Jidda ta Dinga mata Fada tana nuna mata Riban yin Biyayyah ga na gaba Dakai ba laifi Jidda taji mganarta har ma ta Daina kukan Datake Misalin 12 tama Hafsah Sallama Tatafi bayan ta bata kudin Abun Hawa.

Haka ta komama Mama tana Kuka Mama na Lallashinta,Mariya da Auwal sai Ranar sukaji labari Auwal kuwa mamaki ya kamashi ganin Jidda na kukan bata son ya Nazifi Cikin Dage gira ya kalleta yana Fadin"Dillah mama ji wannan yarinya..? Don ma kin samu kinci Darajan ya Abdullahi ammh Me ya Nazifi zai ci Dake..? Kyan banza da ilimi matarsa bata Fiki ba Don ma kin samu zai Taimaka miki har wani Cewa kike baki sonsa..? A kyaleki sai ki kawo wanda ya Fishi Tunda kin zama wawiya.."Jin haka yasa ta kara saka kuka Sai Da mama ta tsawatar ma Auwal din kana Mariya kuwa Baki ta Rike tana Fadin"Lallema yarinyar nan..Kin samu Dami a akala har kina wani iskanci..? Wlh dama nice ke Danace nafi kowacce mace sa'ar samun Miji na nuna Sa"a yarda Maza ke tsada a wannan zamanin"

Wannan mganar tasa Jidda tace ma Mariya ta Bar  mata taje ta Aureshi Mganar har ta kaisu ga Sa"in sa sai da mama ta Shiga mganar Jidda saboda kuka da Damuwa wayartama kasheta tayi Gabadaya Hajiya Sa"a tayi kiran Duniyan taji a kashe,gashi tana kaduna wajen kokarin Bude Shagunanta ,balle tazo gidan Taji lafiya ammh takira Lariya tace tazo Tagani ko Jiddan Tana lafiya.


*Domin Biyan Kudin Karatu akan Littafin Ra"ayi ne ko Buri..? Zaku iya Tura kudin karatunku ₦200 Kachal akan wannan asusun bankin 0552179550...JAMILA UMAR GTB,Sai a turo Shedar Biya ta wannan layin wayar 09069067488,In kuma Katin Waya ne zaku iya Turowa ta wannan Layin 09027767783 kai Tsaye Bayan Mutum ya Dauki Hoton katin...Ga masu Bukatar VIP zasu Biya ₦500 ne ta Lambar asusun Dana bada a sama....! Mutanenmu na Niger kuma Zaku iya Tuntumbar My Jika aglan Nissa ta wannan Layin +22794131747....Sai kunzo Masoyana*




*Shakira...*

Ipagpatuloy ang Pagbabasa

Magugustuhan mo rin

125K 5.8K 174
Bota e Mafies është një botë e errët ku jo të gjithë zgjedhin të jenë pjesë e saj. Ajo nuk kishte zgjedhur të ishte pjesë e asaj bote...ishte fati q...
1M 77.8K 64
"မင်း သေချင်လို့လား" "ကျွန်တော် ချစ်ချင်တာပါ" My Own Creation (စကားအသုံးအနှုန်း 16+)🚨 CV photo by Pinterest
116K 4.4K 26
Short novel Mixed by Sakurak🌸
81.6K 11.2K 78
Author - 麟潜 (Lin Qian). Bai Chu Nian x Lan Bo 白楚年×兰波 Original Title - 人鱼陷落 / ရန်ယွီရှန့်လော့ Eng Title - The Fallen Merman / Preference of Poseid...