MASIFAFFAN NAMIJI..!

By JamilaUmar315

54.1K 4.3K 635

A mu"amalansa da kowa Sai son Barka....Kowa kuma zai iya Fadin kyakyawan Hallayarsa..Ammh ga Matarsa Hafsah b... More

01
002
008
009
012
010
011
013
014
015
016
017
018
027
019
020
021
022
023
033
024
036
025
026
04
034
028
029
005
030
031
032
037
038
06
035
040
039
FINALE
007

03

1.3K 115 21
By JamilaUmar315

*MASIFAFFAN NAMIJI..!*

*Wattpad:JamilaUmar351*

*003

      *TUSHE...*

"Abdullahi Usman Direba Shine Babban d'a Namiji na Farko agidan Marigayi Alhaji Usman Zaria wanda asalinsa Haifaffan Garin Zaria ne,kuma Tashin Zaria a anguwar Babban Dodo Dake Cikin Birnin Zaria.

Alhaji Usman Direba kafin Rasuwarsa ya kasance Mutum ne mai Dabi"ar Aure Saki ya saki mata Sunfi Biyar Ciki harda mahaifiyar Abdullahi,Wato Hajara wacce ta kasance Haifaffiyar garin Zamfara ce Dake Babba birnin Jahar Gusau,A birnin Tarayyan Nageria,Wanda suka Hadu da ita wajen Wani bikin wani abokinsa Da yajema Biki nan garin Zamfara Shikenan Soyayyar ta Kullu Har takai su ga Aure,Hajara itace Matar Usman ta Farko,Auren Saurayi da Budurwa Sukayi.

Alhaji Usman Direba ne,wanda yake jan Babban Mota ta Kamfanin Dangote,Kuma Alhamdulillah ko acikin Direbobin Alhaji Usman na Dabam ne,Domin kowa Sana"ar ta karbeshi Cikin Lokaci kadan ya Tara Abun Duniya kuma yaje Ya Sauke Farali ne kafin yayi Auran Fari,kuma sai da ya Gina Babban Muhallinsa anan Babban Dodo Dake garin Zaria Lokacin Duka iyayansa Sun kare,Dama su Biyu Mahaifiyarsa ta Haifa Shida kanwarsa Habiba toh Tayi Aure a  Danja Dake Jahar katsina.

Ya samu Lakanin Alhaji Usman Direba ne saboda kwazonsa ga aikinsa kuma yafi Jin Dadi in ka Danganta Sunansa da Usman Direba Fiye da ka Kirasa Usman dinsa kai Tsaye Shiyasa Usman Direba yabisa Duk wanda ya sanshi da wannan lakanin nashi ya sanshi har yabar Gidan Duniya.

Ya auro Hajara Cikin Soyayya da kauna,Aka kuma kawomai Ita Zaria,agidan Daya gida Yan"uwan Hajara da Dangin Hajara Suka Tafi suna ta son barka Suna Fadin Hajara ta Dace,Hajara batayi Zurfi a karatun Bokonta ba iyakarta Jss3 ta Dakata da karatun sai dai Tana da Ilimin Addini Daidai Gwargwardo.

Zamansu ya Fara ne Cikin kwanciyar Hankali da kuma Soyayyah,Har na Tsawon wata Daya da wani abu Komai tace tana so Cikin Rawan jiki yake mata da Tattali sai dai Lamarin ya Sauya ne Lokacin da Hajara Ta Fara Laulayin Ciki kuma sukaje asibiti aka Tabbatar musu Da Tana da Shigar Ciki na Tsawon Sati Uku da wani abu wannan Dalilin Shine Sanadiyar Tabarbarewar zamansu wanda har yakaisu ga Rabuwa da Juna na Har Abada.

Hajara tayi mamakin Sanda Usman Direba ya nuna bayason Cikin Jikinta atakaice dai bai Shirya Haihuwa yanzu ba,ya Tada Bala"in sai an Zubar da Cikin nan ita kuma Hajara tace bai isa ba yayi Bala"in yayi barazanar Duk abanza Hajara tace bamai Zubar mata Cikinta,ganin haka sai ya Chanza Salo ya Daina sakarmata Fuska ba kalma mai Dadi,sai Harara da Habaice Habaice da Mganganu marasa Dadi,Daga karshe sai ya Fara mata Horon Yunwa Duk Hajara ta lalace ta Rame ga laulayin Ciki ga kuma Horo da yunwa Wajen miji kuma ba wani Saussauci Ballatana jin Dadin Dalilin Haka Rana tsaka Hajara ta Gudu ta koma Garinsu Wajen iyayenta ta kuma Fadamusu Duk Halin da akeciki Iyayenta kuma suka ce tayi zamanta agida kuma ciki Insha Allahu sai ta Haifeshi.

Wannan tafiyar ta Hajara itace Tafiyar ta Har Abada Daga Gidan Usman Direba Domin bata Dawo ba Sai dai Taga sakon Takardan Saki,Domin Tunda tatafi bai Bita ba kuma iyayenta suka ce bazata koma ba sai yazo har garin,shi kuma yaki Zuwa kanwarsa Habiba Taje har gidansu Hajara tana Rokon iyayenta da su barta ta Dawo ammh sukace Sai Usman yazo,Dole ta koma ba jin Dadi Domin Usman yamata Rantsuwa bazai je ba,Domin ma Ta gane Hajara bata gabanshi sai kawai ya Shiga neman Aure Wata Biyu da Tafiyar Hajara yayi Sabuwar Amarya mai Suna Sahura Ita yar zaria ce,Ranar kuma da aka Dauramai Aure ya Turama Hajara Sakinta Uku ta Cikin Akwatin Sirrin Wayarta Ranar tayi kuka kamar Ranta zai Fita ta kuma yi Nadamar wannan Auren na Usman wanda bai da wani Amfani iyayenta su suka Karfafamata Gwiwa suka kuma ce Tana Haihuwan Cikin Usman Bayan ta yayeshi Zasu maidashi Gidan Ubanshi Domin Itace Tasu bashi ba.

Kusan Abunda ya Faru da Hajara ne ya Faru da Sahura itama Auren ba Dadewa sai ga Ciki nan fa ya Tada Bala"i sai an Zubar tace bai isa ba Itama dai Bata Zauna ba ya Saketa ya Tura ta Gida da Ciki,Ba Dadewa kuma ya Sake Auran Wata Bazawara Karimatu sakin Wawa toh itace ma Tayi karfo Domin Daman Tunkafin ta Shigo Gidan ta samu Labarin Irin Halinsa sai ta Shigo da Shirinta na zama Dashi Domin bazata so ya saketa ba Tunda gaskiya Usman yana Kokarin kyautata iyalansa Shi matsalanshi Daya Rashin Son Haihuwa.

Ya auri karimatu ba Dadewa Aka kai ko masa Hajara ta Haifi Danta Namiji,Habiba tazo har gida ta Shaidamai cewa Mahaifiyar Hajara takirata ga waya tana Shaidamata Sai tayi ta gaske ya Bata Kudi 50k tatafi Dashi wanda za"ayi Hidimar suna da Shakika Ranar da Zata tafi ta matsamai wani Suna za"a sakama yaron Cikin Bacin rai yace asakamai kowani Suna Habiba dai Haka taje Zamafara ba wani kwarin Jiki takai Kudin Daya bata tana ta Ban Hakuri Iyayen Hajara basu bi takan Habiba ba,Domin komai Sunyi ma yarsu Usman yaci Darajan Musulunci ne da kuma Yaron Daya Hadasu kuma ko Sisin Habiba basu karba ba sukace ta maida mishi,sun dai karbi Atamfa da Rigan yaron data Rantse musu ita ta Siya da Kudinta Gudummmuwarta ne kana suka karba.

Sun basu Hakkinsu sukace wani Suna Za"a sakama Jaririn wanda yazo Duniya yana kama da Mahaifinsa sak sai dai ya Dauko Hasken Fatan Hajara,Habiba tace a sakamai Sunan Mahaifinsu Abdullahi batare da tayi wani Tunani ba,Haka ko akayi Ranar suna akayima Yaro Shakika yaci Sunan Abdullahi kwana Biyu Habiba tayi ta Dawo Danja Batare ma Data Biyo Zarian ba Saboda yadda yayanta ya Bata Haushi da Takaichi.

Hajara ta Cigaba da Kula da Danta da Taimakon iyayenta Abdullahi nada wata Shida Sahura ma ta Haifi yarta mace Wacce taci Suna Zanniratu,wanda itama sai da Mahaifinta ya zo yama Usman Tijara kana yaje yaga yarinyar ya mata Huduba kuma ya saki bakin aljihu akayi Hidima Da Shawaran karima da kuma Tsoron kada Mahaifin Sahura yakai kotu kamar yadda yace,Dole ya yardan ma kansa zai Dinga aika kudi Gidansu Sahura Duk Wata kudin Shayarwa Hajara kuwa ko ta kanta Bayabi Saboda yaga iyayenta Sun sakamai Ido.

Zamansu da Karima ya Daure Saboda Bata yarda tayi Ciki Ba ballatana Goyo,,ammh duk da Haka ko Shekara basu yi da Aure ba ya kara Auren wata Bafullatana Hure,wacce ita ba komai ya Rabasu ba sai Barauniya ce tana mai sata yasa ko Wata Biyu bata yi ba ya Saketa Daga ita sai Kuluwa Itama dai tana Samun Cikin ya kadata Gida,Ita Allah ya Tsareta Cikin sai ya Zube bata sha Wahala ba Sosai,Yayi Aure Aure bai san iyaka ba kuma Duk Da Ciki yake sakinasu,karima ce dai Matarsa Domin bata yarda tayi Ciki ba Ballatana Goyo Shiyasa Duk wacce ta Shigo Fita take ta Barta.

Wasa wasa sai da Usman Direba ya Tara  ya"ya Biyar wadanda ya Saki iyayensu kuma aka Haifan masa,ana ciresu anono ake kawomai Cikin Gidansa Abdullahi na Cikin Jerin Wadanda iyayensu mata ke Dawo Dasu Gidan Ubansu,Ganin haka yasa Karima ta Daka Tsalle tace bai isa ba ba Yaron da zata Rike balle tama mata Wahalan Da,ita tana Zaune bata Haihu ba,Usman bashi da yarda zai yi Domin ya"ya dai nashi ne, kuma in bai karbesu ba Duniya zata kara Tur Dashi akan Wanda daman takeyi Ganin Haka ne yasa ya yarda Ita karima ta Haihu wannan Dalilin ne yasa Karima ta yarda zata Rike ya"ya Biyar din da aka Dawo Dasu gabanta Bayan Taje asibiti an Cire mata Abunda aka samata Saboda kada ta Dauki Ciki.

Acikin yaran Biyar da aka Dawo Dasu Abdullahi ne Babba sai Zanniratu,sai Subai"a,sai Auwal,sai Mariya sai karamarsu Hauwa Jidda kuma yawancin yan kai Daya ne Domin Abdullahi da Zannira da Suba"i Tsakaninsu yan shekara da yan watanni ne,,Cikin ikon Allah karima ta ma yaran Rikon Tsakani ga Allah Domin bata nuna ba ya"yanta bane komai ita take musu ganin haka yasa Usman yaji Dadi komai ya samu Na karima ne Saboda Farantamai Datakeyi.

Sai dai har wajen Shekara Biyar Karima Haihu Shuru Hankalinta ya Fara tashi ta Fara Damuwa Taje asibitoci da Dama ammh har tsawon wasu Shekaru Shuru,tayi kuka sosai kuma Tayi Tunanin Hakkin iyayen su Abdullahi ne ya kamata Domin Tana gani Usman yake Rashin Mutumcinsa da adalcinsa bata taba Hanasa ba,kila Allah ya Barta ne Domin yana Nuna mata Isharansa Shima Usman din yaso Haihuwan da karima ammh Allah ya Hanasu Dukkansu sun Gane kuskuransu alokaci Daya wannan Dalilin Yasa karima ta Rumgumi ya"yan Kishiyoyinta ta Rike gam Domin itace Uwarsu ayanzu Shima Usman yayi Nadama Sosai ya yi kokarin Bin Matan nashi Daya saka sai Dai Sahura kadai ya samu ya Roketa Gafara Har Lokacin batayi Aure ba Hajara kuma koda yaje zamfara Iyayenta suka ce ta Dade da Aure a garin Gusai Dole ya Dawo Mahaifiyar Subai"a kuma Allah yayi mata Rasuwa Itakuma Mahaifiyar Auwal,Ta Koma Niger wajen Yayar mamanta da Zama Mahaifiyar Hauwa Jidda kuma Tatafi Saudiya neman kudi Ganin haka yasa ya Dawo Domin ingantama yaransa Rayuwa Habiba tafi kowa Murnan Haka tana kuma tayashi Addu"an Allah ya yafemai kurakuransa.

Duka ya Sanyasu makarantan kudi ne,Abdullahi da Zanniratu suna Lawal aliyu ne,su kuma Sauran sai ya sakasu a Comtemporary life Sch Shi kuma yakai  kaisu a motarshi in yana Gida in kuma Baya gari sai su Hau mashin Din Haya Domin yana Barin musu Ishashen kudi a Hannun Karimatu.

*****

Bayan Shekara Ashirin da Takwas..

Shekarun sun ja abubuwa Dadama sun zo sun Shude ciki harda Rasuwar Alhaji Usman Direba wanda yan Fashi suka Tareshi a Hanyar Abuja suka Kasheshi Shida yaron motarsa Har Lahira,lokacin Abdullahi nada Shekaru Ashirin da Biyar aduniyar har ya kamallah Secondry Sch Dinsa yana Diplomansa a Poli Dake Cikin Zaria,Zanniratu kuma Tuni tayi Aure a Kaduna Har ta Haihu,Subai"a ne tana Shakaran Karshe a matakin Sankandiri sai su Auwal da Jidda da Suka Farkon Zangon karshe na Karatunasu.

Mutuwarsa ta Girgiza Iyalansa Gabadaya,jigon Gida ya Dawo Duka Hannun Karima wacce Suke Kira da Mama,Allah yasa Alhaji Usman yabar kaddarori da Dama Ciki harda Babbar Mota Daf,Tashi da kanshi da kanta da Gidaje da Filaye,Su aka Raba aka Saida wasu Domin inganta iyalansa Dashi aka Cigaba da Biya musu kudin Makaranta Har Suka kamallah.

Zuwa Lokacin da Abdullahi keda Shekara 28 aduniya ya zama Saurayi Kin kowa kin Wanda ya Rasa,Abdullahi Namijine, mara Hayaniya,mai kwazo da kuma Kokari,bayason Wasa acikin Lamarinsa kuma baya Harka da mai Son Wasa,,Mutum ne mara son Raini ga Son Girma yana da isa da Iko da kuma Takama,sosai yake da Dadin zama,yana Girmama Mama Duk da ba ita ta Haifeshi ba,kuma Duka kannensa suna Girmamasa,Domin ya Tsare Gidansa Baya Sakarmusu Ballatana Suga wajen Rainasu,Mama kuma Duk Cikinsu Tafi son Abdullahi Domin Jajirtattace ne kuma Tsayayye ne kan komai Haka Goggonsu Habiba Itama akoda yaushe wajen Yabon Abdullahi Take Shima kuma Dan Gidanta ne, Domin Duk Sati yana Wajenta Achan yakanyi Weeked Dinsa in babu karatu A makaranta Dayake Allah bai bata Haihuwar Da Namiji ba sai mata Kuma Duk Sunyi Aure sai Autar ta Kadai ta Rage batayi Aure ba.

Bangaren Hajara kuwa Wacce Abdullahi da Sauran ya"yanta ke Kiranta Umman Sadiq,Wacce take zaman Aurenta agarin Gusai tana Auran wani Dan kasuwa kuma Alhamdulillah suna Zaune lafiya ta Haihu Dashi,ya"ya Hudu Uku maza Daya mace Babba Shine Abubakar Saddiq,sai Halifa sai Umar Autansu ne Fatima Suna Kiranta Zahra,Abdullahi yana Zuwa wajen Ummansa in sun samu Hutu Lokaci bayan Lokaci kuma suna Mgana awaya Sosai Kannenasa Duka sun saba Dashi.

   Abdullahi ya gama karatunsa na Diploma sai ya Dora Hnd dinsa,yana kamallah sai ya samu wani karamin aiki a Kango Dake Zaria yana aiki a wani karamin Office anan Cikin kongo zaria yana Diban Albashinsa da bai gaza Dubu 70 ba,Dashi yake Taimaka kannensa da kuma Mama da Sauran Bukatu,Da albashinsa kuma ya Fara Gina Gidansa a Tukur Tukur Dake Zaria Lokacin ne kuma akayi Bikin Subai"a Inda a wannan Sha"anin Auren ne ya Hadu da Hafsat wacce kawa ce ga Suba"an tare sukayi makaranta da Ita.

Hafsat Haifaffiyar Garin Zaria ne a Anguwar Tudun wada Zaria Hafsat Itace ya ta Biyu a Gidansu Kuma ta karshe bata da kani ko Daya,Daga ita sai yayarta Hadiza wacce take Auran wani mai Kudi a Garin kano,Dan kasuwa ne,tsakaninta Da yayarta Hadiza Shekara Takwas Domin Har Hajiya Zinaru da Alhaji Hamza mai Guga Har sun Fidda rai da kara Haihuwa sai kuma Allah ya Basu Hafsah Daga Baya wacce tatashi Cikin Gata.

Hafsah yarinyace mai Sanyin Hali da Hankali Tashinta Cikin Gata baisa ta zama Sangartattaciya ba sai dai Sanyin Halinta uwa uba kuma tana da kawaichi da Hakuri,Hafsat Tana da kyau Sosai Domin Farace mai kunya Tana da Kokari Shiyasa a kananun Shekarunta Har ta kamallah Nce Dinta tana da Shekara 22 a Duniya,Hafsat bata cika Fita zuwa Gidajen kawaye ba Daga makaranta sai gida sai ko Inda Taje gidan yayarta Hadiza Hutu agarin kano achan take ma Kwana Da yawa Har sai Hutunasu ya kare take Dawowa Zaria.

Hafsat da Subai"a sunyi aji Dayane a makarantarsu ta Comtemporary,Da Farko ba kawaye bane Daga Baya ne suka Zama Good Friend Da Hafsat Saboda Sanyin Halinta da ita kanta Subai"an Data nemi Hafsatn Ta yarjemata suyi kwawancee Wannan Dalilin ne yasa Suka Fara Mutumci sai kuma Suka koma kawance ganin itama Subai"an bata da wani Banzan Hali Subai"a Tazo Gidansu Hafsat ba Adadi ammh Ita Hafsan Sau Daya Tataba zuwa Gidanasu Subai"an Sanda mama bata da lafiya Taje gaishesu,Sai dai Subai"an tagaji da Korafi Harta Ammin Hafsat sai da ta mata Tsiyan bata Zuwa Gidansu Subai"an

Dalilin Bikin Subai"an wacce Zatayi Aure acikin Zaria Zata Auri Dan Gidan mallawan Zazzau,Shine Dalilin Dayasa Dole Hafsat tayi Hakuri ta Shiga Sha"anin Bikin Tunda Subai"an ta sakata Dan Dole,Tare sukayi Hidimar Raba cingam kuma sukake Gudanar da Wasu Shirye Shiryen Bikin,kuma Hafsat da Abdullahi basu Taba Haduwa ba Domin Sanda zata zo Gidansu Shi Baya nan yana wajen aiki,sai dai Ita Hafsan tana ji Subai"an na yawan Zencen yayanta Abdullahi.

Basu Fara Haduwa ba sai ana Gobe Bikin Subai"a da suka Dawo Daga Gidan kunshi Suka Iske Abdullahi akofar Gidan suna Hira da wani abokinsa Nazifi,Wata Soyayyah ce ta kulla da ganin Farko da sukama juna Hafsat taji Jikinta ya amsa Tare da Zuciyarta,Shima Haka a Bangaren Abdullahi haka ya Wuni yana Fama da Faduwar Gaba Daya Tuna da Hafsat Haka Itama Abagarenta Haka ta koma Gida Jikinta Duk a sanyaye Domin Taki yarda ta kwana agidansu Subai"an Duk da Ammi ta barta.

Washegari Sai suka Hade wajen Dinner,wanda Abdullahi bai so Zuwa ba ammh Mama ta matsamai da lallashi Ita da Zanniratu yasa ya yarda yaje wajen sai wani Bata rai yake Shida abokinsa Nazifi yaje,Suna Gefe suna kallon Kowa Daidai Cikin kalle kallen nashi ne suka kara Hada ido wannan karon Dukkansu basu Dauke ido Da kan Juna ba,Nazifi ne ya ankare da Halin da suke Ciki ya kuma Bama Abdullahi Shawaran ya Tunkari Hafsat kada ya bari Garin kallo Ruwa kwado yamai kwafa.

Lokacin da Abdullahi yanemi Kebewa Da Hafsah bata ki ba,Kuma sanda ya Furtamata kalmar so nan ma batayi gaddama ba Domin a kallon Farko Zuciyarta ta aminta Dashi kafin atashi wannan Dinner Duka Zuciyoyinsu sun Aminta da Juna sanda Subai"a tagama Fahimtar Abunda ke Faruwa Farinciki ya Cika Ranta Domin Zata so Yayanta ya samu mace irin Hafsat.

Ranar Hafsah gidan Subai"a ta kwana Washegari ne ta koma Gida Cike da Farinciki,wanda yakasa Boyuwa saman Fuskata Ammi ta Tasata Da Tambaya Cikin kunya ta gayama mata komai ita kuma ta Shiga Tsokanarta,bata kasa a gwiwa ba Alhaji Hamza na Dawowa ta Sanar Dashi komai Shi kuma ya Kira Hafsah yace in Abdullahi ya Kirata tace yana nemansa.

Haka ko akayi Abdullahi ya gana da Mahaifin Hafsah kuma ya gamsu Dashi Lokaci Daya ya Bashi Daman ya nemi Hafsat,Cikin Soyayya da Muradi suka Fara Gudanar da Soyayyarsu Cikin Son Juna da kauna Zuwa Lokacin kuwa kowa Daya Shafi Abdullahi da Hafsat ya gama Sanin Soyayyarsu Hatta Umman Sadiq Taji labari wanda Abdullahi yaje har chan yamata Bayani kuma tayi Farinciki da Hakan watansu Hudu da Haduwa Alhaji Hamza yace Abdullahi ya turo magabatansa,Cikin Lokaci kankani akayi komai aka gama Aka Sanya Ranar Wata Bakwai masu Zuwa A inda aka bar Abdullahin zai kama Haya kafin ya karisa Gidansu.

Abubuwan da suka Biyo Baya kafin Aure,Abubuwa ne masu dadi Sosai,Domin Zumunci ya kulli Tsakanin Umman Sadiq da kuma Ammi,Kuma abubuwa suna Tafiya Daidai,Soyayyarsu Kuwa ba wani Targadan Domin Abdullahi mutum na gari kuma alokacin bai Taba nuna mata yana da Halin Fada ba wanda kuma Kowa baisanshi Dashi ba andai sanshi da Bayason Raini ko Kadan da kuma Tsare Gida Uwa uba kuma Rashin yalwar Fara"a ga Fuskarsa.

Biki ya karato kuma anyi Duka Shirye Shiryen Daya kamata wani Flat Abdullahi ya kama Ahaya a Gaskiya layaout suka Fara Zama Shida Hafsat Cikin Soyayyah da Muradi mai Girma zamansu ya Fara Cikin Farinciki ne Gefe Daya kuma yana ta kokarin Karisa Ginin Gidanashi Domin Bayaso Hafsat tayi Haihuwan Fari suna Gidan Haya.

Rana Daya Ko nace Rana Tsaka Abdullahi ya Farama Hafsah Wannan Halin nasa na Fada da Mita da korafi,Tun bayan da Alhaji Hamza ya samoma hafsah Koyarwa a wata Private School,Ammh sai Abdullahi ya Hana ya kuma Bada Idanuwansa Toka yace bai amince Hafsat Tayi aiki ba,Alhaji Hamza bai ja Mganar da Nisa yace Hafsat tayi Hakuri da aikin Duk da ta sakarai Ammh Tayi mamakin Yadda Abdullahi ya Hanata yin aikin Alhalin bata Zaci haka Daga Gareta.

Shi kuma Abdullahi ba komai yasa ya Chanza ba sai Zugan Abokinsa Nazifi wanda yaji labarin Case din aikin Da mahaifin Hafsah ya samo mata da kuma Hanawa da yayi Nazifi Shi yabama Abdullahi Shawaran Sakarma Hafsan da yakeyi ne yasa Take Tunanin komai Zata iya yi Ya kamata ya Fara Nuna mata Shima Namiji ne,ya daina Sakarmata akomai yadaina Nuna ta iya ko tayi Daidai Haka kadai zai sai Su Daidaita ta kuma Dinga Shakkarsa ta kuma gane Shine Mijinta tana karkashinsa ne,Da wannan Shawaran Abdullahi yayi amfani ya sauya Takun zamansa Da Hafsah Daga Zaman Soyayyah da kulawan da kauna mai Tsanani,ya koma zaman Kadahan kadahan Masifa,korafi,da kuma Mita komai kuma akayi ba"a mai Daidai Hafsah ta Daina Yin wani Abu Na Burgewa ga Abdullah ba, komai tayi Sai yayi korafi kuma ya Nuna Batayi mai Daidai ba.






*Shakira...*

Continue Reading

You'll Also Like

264K 25K 189
( Unicode Ver) သူမသည် ယခင်ဘဝက ရုပ်ပျက်ဆင်းပျက်ဖြစ်ပြီး သူမ၏ မိခင်သည် မတရားသဖြင့်သေဆုံးသွားခဲ့သည် ။ အဆိပ်ဝိုင်တစ်ခွက်က သူမကိုသတ်ဖို့မလုံလောက်တော့ တောက...
125K 5.8K 174
Bota e Mafies është një botë e errët ku jo të gjithë zgjedhin të jenë pjesë e saj. Ajo nuk kishte zgjedhur të ishte pjesë e asaj bote...ishte fati q...
44.3K 5.1K 74
Author _ Shuiqiancheng That's not my work.I am Just Translator
380K 69.2K 132
Special Case Files of Rebirth All Credit to - Original Author - 狂想之途 KuangXiang Zhi Tu Chapter - 132 English Translator - Vivian English Editor...