Page Three

570 49 3
                                    

🌹 *_QADR_* 🌹
( _the story of Rukayya_ )

Written by *Zeeneert*💞

*Zeeneert*@wattpad

*Page Three - Visitors/ Earth enthusiasts 2*

***
Dayanma wuraren karfe biyar muna zaune ƙarƙashin wata bishiya dake gefen rumfar Baffa Ade(mahaifin Hari) a kofar gidansu. table yake kafawa kullum a ƙarƙarshin wannan rumfar tasa yana saida Goro,sugar irin ƴan kullin nan se alawar minti da lipton dadai ɗan abunda ba'a rasa ba yayinda daga gefen rumfar tasa kaɗan kuma masallacin da ake sallah a garin Babban buli ne. Carapke mukeyi abunmu gwanin ban sha'awa,inwannan tafaɗi tabama nagefenta tayi hakadai muke
rounding a tsakaninmu ayayinda Baffaananmu kezaune gaban masallacin suna hira abunsu. Hari ne tafara ganin mutanen su Lamiɗo cikin sauri tashiga yimana magana ƙasa ƙasa cikin harcen fillanci tace

"Gacan baƙin da mukayita gudunsu ranar yauma sundawo zasu koma shikin gari"

dasauri muka ɗaga kawunan mu muna kallon direction ɗinda suke.

Can muka hangosu tsugune suna gaida baffaninmu yayinda Uztaz me first aid box ke tsaye rike da kafaɗun Lamiɗo suma suna gaidasun. Baffa Ade dake zaune cikin sauran baffananmu naji yace "Ita wannan lafiyanta naga tana ingisa afaaa?" don daman cikin su yake zama se in anzo sayan abu yake tashi yaje rumfar tasa yabayar yakoma cikinsu acigaba da hira dashi.

Murmushi sukayi dukansu yayinda Uztaz dake riƙe dashi yace "ya taba karyewa akafar ne daman so in yayi tafiya mai yawa ciwon yakan tashi mashi, yanzuma tashi yayi shiyasa yake ɗingisawa" take Bappanaina suka shigayimai sannu cikeda tausayawa yana amsawa da "yauwa sannu" yayinda Baffa Haruna yadubesu yace "irin wannan aisai kufaɗa ma malaman naku abershi agida basai yatahoba tunda kunsan matsalarshi" Auwal yace "Aibazai yuyu ba Baffa" da mamaki Baffanaina sukace "miyasa?" wannan karan Uztaz ne yayi magana yace "atsarin makarantar duk wanda bai halarci wannan aiki akayi dashiba tosai yasake shekara ɗaya acikin shekarun da aka dibar masa nagamawa" Baffa Ade yace "Aiyooo. Ikon Allah,toh ai samari komai ɗan lafiya ne,akan kajima kanka shiwo bagwanda ka hakura kakara shekarar ba?" Lamiɗo wani irin zare idanu yayi yana wiƙi wiƙi dasu yace "Ehhh Baba?" kafin yashiga sosa kanshi ahankali funnily. dariya abokanan tafiyartasa suka saka yayinda Uztaz yace "Baffa yafison mugama tarene kuma muma bamwason mubarshi abaya" murmushi Baffanaina sukayi sannan sukace "Dawannan ma dan wannan anma aizaiyita wahala ne" Uztaz yace "aiyau bamutafi dashiba ƙarƙashin wata bishiya can gaba da ƙauyen ku muka barshi damuna dawowa ne muka biyomai muka tahonan tare" Baffa Ade yace "Allah sarki kunyi dabara mekyau kam. Allah yashigaba da haɗa kawunanku" sukace "Amin" atare kafin sukacema Baffanaina zasuyi sallan la'asar suwuce bakin hanya ankusa zuwa ɗaukansu.

Baffa Ade yace "bismillahn ku ga ruwa shan kuyi alwala" yakarashe maganar yana nuna musu rijiyar dake arewa da masallacin kaɗan. Uztaz taimaka ma Lamiɗo yayi yazauna bakin varender ɗin masallacin kafin yakarbi goransa daniyar ɗebo masu ruwan alwalan,sauran kuwa already harsun Isa bakin rijiyar sunfara ɗiba.

Dukansu agefen rijiyar sukayi alwalan suka cika gorunan su kafin suka dawo bakin masallacin munajinsu sunata santin daɗin ruwan garin Babban buli. Auwal yace "kaman ba ruwan rijiya ba wallahi" Hafiz yace "ga sanyi kuma. ni dagayau ma bazan sake sayan ruwa ba nan zanzo ina ɗiba kafin muwuce" Auwal dake gefenshi dariya yasaki tareda dafa kafaɗunshi yana faɗin "Yaro Laushi! laushi!" sauran ma dariyan sukeyi suna tsokanar Auwal wai "Yaji laushi" shima dariyar yayi sannan yace "laushi kai! ga inda kuɗi na bazai tabuba gakuma daɗi daga indallahi babu algus ɗin bature dole nikejin laushi" and I started wondering what's the meaning of this laushi? tunda ɗazuma naji suna tsokanar Lamiɗo da kalmar.

Abu ɗaya dai nalura dashi "Laushi" kalma ce dasu kaɗai sukasan mesuke nufi kuma tariga tazamo musu sara atsakaninsu. Lamiɗo kamar gaske hartaimaka mishi sukayi yayi alwala suka ɗagashi sukayi cikin masallaci dashi suna tambayarsa kozai iyayin sallar atsaye wanda daganan banji amsar daya basuba bankuma saniba ko a tsayen yayi ko azaune yayita. abu ɗaya nakeda tabbaci alokacin Lamiɗo makaryaci ne kuma dukda kankantar shekaruna bana tunanin yakamata yayi amfani da karyarsa wurin gudanar da addini.

QADRWhere stories live. Discover now