Page Fifty Four

90 4 0
                                    

🌹 _*QADR*_ 🌹
( _The story of Rukayya_ )

Written by *Zeeneert* 💞

*Zeeneert*@wattpad

Page Fifty Four

Nida nake bama Yaya Lamido kwarin gwiwar segashi yau nina tashi da matsanancin faduwar gaba,senakejin wani irin nervousness dana rasa dalininsa hakanan minti minti nake zuwa inleka filing gidan ko Allah zaisa Inga isowar Yaya Lamido anma shiru,haka wata zuciyar tadinga rayamin wayasani ma ko sanda baki leka dinba yashigo harya wuce baki saniba.
Wuraren shabiyun rana su Yaya Aisha suka fito daura abincin rana dayake girkin Ummi ne,dole na hakura da leke leken nakoma main parlour dankada suyi zargin wani abu anma fah dukda haka gabadaya hankalina baya jikina. Sonake kawai wani yazo yasanar dani isowan Yaya Lamidon kokuma azo asanar dani komai yatafi daidai tsakaninsa da Kawu Sani anma kuma nasani ko karen haukane yacijeni basamun irin mutuminnan zanyi acikin gidanba dankuwa Yaya Salim dinma danakeda hope akansa bason batun auren yakeyiba.

***
Bin Rukayya da kallon tsana Aisha da Zaheera sukayi sanda tabar harabar backyard din harta shige parlour. tsaki Zaheera tasaki sannan tace "munafuka kawai! safa da Marwan merai takeyi tun dazu anan gurin" Aisha ne tace "dubawa takeyi kozata ga isowan masoyinta mana" harara Zaheera tawatsa ma Aisha sannan tace "Watoma ke fata kike yazama masoyin natane zezo neman aurenta Koh?" Aisha tayi dariya tace "bafata nikeyi ba Yaya Zaheera,it's just obvious,rashin damuwa da aurar da'ita daza'ayi da rawar jikin datakeyi tun safe kadai ya Isa ya tabbatar muku cewa Sir Isma'il ne meneman aurenta. Aike tareda ke muketa samata Ido tundazu so basai namiki dogon bayaniba" Zaheera tace "Komadai miyene you just can't be sure,kibari muganshi da idanun mu semu tabbatar" Aisha tace "toshikenan nayi shiru,Allah yakaimu anjiman sanda zai iso" Safiya dayanzu isowanta gurinsu taji last statement dinsu kuma tasan tabbas maganar bakon sukeyi seta samu guri agefen su tazauna tana fadin "toh inyazo din yaza'ayi musani? Kunsandai sashin Abba zashi direct kawai Koh?" Aisha tace "karki damu ai Yaya Zunnurain nanan kuma Ummi tace mishi daya iso yazo yasanar da'ita" Safiya tace "toh shikenan. Allah dai yasa ba Sir Isma'il din baneba dankuwa inshine inaga har zazzabi senayi wallahi. The girl can't be always lucky gaskiya" Zaheera tace "Kima bar maganarnan. Bashidin baneba dayardar Allah"

***

Karfe daya da Yan mintuna Auwal da lamido suka iso cikin garin Bauchi dankuwa Lamidon zuwa yayi ya ciccibo Auwal din a Azare,acewarsa bazai iya zuwa ganin Kawu Sanin shi kadai ba seya nemi dan rakiya. Dasuka baro tasha ganin lokacin sallar azahar yayi seda suka tsaya awani masallaci sukayi sallah sannan suka karaso gidan Kawu Sanin. Lamido baiwani sha wahalar gane gidan ba dayake yazo yafi sau biyuma shikadai.

Abakin kofa sukayi kicibis da Zunnurain yadawo daga masallaci ze shiga gida suma sun sauka a napep kenan,sallama Lamido yama Zunnurain din sukayi musabiha sannan Zunnurain yazuba ma Lamidon idanu yanason yatuna a Ina yasan fuskar(karku manta duk zuwan Lamido gidan da Zunnurain yake fara kicibis abakin kofah,sau dayane yahadu da Mai wanki har mai wanki ya je ciki yasanar ma Ummi zuwan shi zasu fita unguwa itada Zaheera) ganin irin kallon da Zunnurain din kema Lamido se Lamido yasaki murmushi yace "Baka ganeni bakoh?" murmushi Zunnurain yasaki yanadan shafa sumar kansa yace "wallahi nadai ga kamar nasan fuskar anma nakasa tuna a Ina nasan fuskar taka" Lamido yace "Allah sarki. I'm Isma'il,sau biyu muna haduwa dakai twice danazo gidannan kwanakin baya katuna yanzu?" take se abun yayi hitting kan Zunnurain,cikin sauri yace "yeah! natuna kaine kake zuwa neman Rukayya Koh?" Yar dariya Lamido yasaki yana gyada kai sannan playfully yace "but this time I'm here to your Dad,Allah dai yasa yana gida" Cewar lamidon. wani abune ya tsirga kirjin Zunnurain lokaci guda Jin abunda Lamidon yace,take se kwakwalwarsa tafara tuno masa hirarsu dasu Ummi da Aisha daren jiya,inda Aisha keta emphasising ita tasan Sir Isma'il ne ze nemi auren Rukayya ayayinda Ummi da Zaheera kemata fadan tadaina yimasu wannan fatan. Zunnurain besan sanda yadaga idanu yafara kallon Lamido daga sama har kasaba yana tuna sanda Lamidon yace masa sunan sa Isma'il. Cikin sauri zuciyar shi tafara raya mishi "this can't be...this can't be" because daga kallon yanayin yanda Lamido yayi dressing dakuma kyawunsa,nutsuwarsa dayanda yake magana kadai yasan indai Rukayya ta aureshi toh tabbas tayi musu nisa,zatayi musu nisan da bazasu iya taking revenge akanta ba.

Dostali jste se na konec publikovaných kapitol.

⏰ Poslední aktualizace: May 21 ⏰

Přidej si tento příběh do své knihovny, abys byl/a informován/a o nových kapitolách!

QADRKde žijí příběhy. Začni objevovat