Page Fifty Two

25 1 0
                                    

🌹 _*QADR*_ 🌹
( _The story of Rukayya_ )

Written by *Zeeneert* 💞

*Zeeneert*@wattpad

Page  Fifty Two
***
Lamido na kwance akan gadon Auwal ganin yakira Rukayya yafi a kirga,yayi massage ba adadi batayi reply ba kuma yanada tabbacin koya cigaba da kiran bazata daukan ba sekawai yayi wulli da wayar kasa wanda hakan yayi daidai da shigowar Auwal dakin,Kuma wayar adede kafarsa tasamu matsuguni.

Zare idanu Auwal yayi "Kai hankalinka daya kuwa? Ragargazamin waya zakayi?Ah to ba laifinka baneba laifina ne dana dauki wayata nabaka kuyi conciliating kaida budurwar ka asanda take fushi dakai" Auwal yayi maganar
ayayinda ya tsuguna yadauki wayarsa yana duba ko lafiyarta kuma alhamdulillah bai fashe dinba,battery da marfin wayan ne dai suka fita wanda atake yayi fixing dinsu.

Tsaki Lamido yayi ayayinda yatashi daga kwancen dayake yana massaging forehead dinsa sannan yadubi Auwal yace "I'm sorry Auwal,banmasan sanda nayi wurgi da wayarba wallahi. I'm just so angry with myself" Yar dariya Auwal yasaki ayayinda yazauna gefen Lamido yace "Angry with yourself ko angry with Rukayya taki picking wayarka?" Lamido yayi tsaki yace "Narasa me yarinyar nan takeso,I can't even understand her Auwal. dazu tana fushi danna ce Ina neman aurenta dakuma fadama Gogode abubuwan datake going through agidan Kawun ta yanzu kuma namata massage could you believe wai haushi takeji sabida nace bata sona?" Wannan karan dariya sosai Auwal keyi,yace "Kaima meyakaika fadan hakan?" Lamido yace "what do I do toh? Abubuwan datakemin ne suke sani jin kamar nikadai nake kidana da rawana inbahaka ba mesonka ai bazaiji haushinka dankace zakaje neman aurensaba,mesonka ai bazai yi fushi dakai ba dankanason cireshi acikin kangin rayuwar dayake ciki ba" Lamido yakalli Auwal a raunane yace "I'm scared Auwal. I'm scared kada wataran Rukayya tajuyamin baya intayi realizing may be basona takeyi ba" cikin sauri Auwal yace "kadaina irin maganar nan. waye yace maka Rukayya batasonka? Wallahi yarintace kawai ke damunta da rigima. Itakanta batasan metakeso yanzu hakaba. She's just scared of something wanda hakanne yasa take ganin kamar abunda kakeyi din ba gata kakeson yi Mata ba wahala kakeson jefata a ciki" wani irin nannauyar ajiyar zuciya Lamido yasaki sannan yace "I hope so" because koda Auwal din yabashi kwarin gwiwa seyake ganin kamar ya fadane kawai danya kwantar Mai da hankali, he still have that feeling nacewa may be Rukayya bason shi takeyi ba and this's making him loose hope akan cewa Rukayya bata reciprocating soyayyar dayakeyi mata.

Haka Auwal yadinga bashi baki,yace "just give her sometime itadakanta zata sauko" cikin sauri Lamido yace "I can't Auwal. bazan iya jira har saita saukoba infact I'm going back to see her tomorrow kuma innaje bzan tafi ba se ta saurareni. Fushinta is Killing me,it's making me go crazy about her so konace zantafi Gombe batareda munyi resolving issue dinnan ba gabadaya hankalina zaizama yana Babban bulin ne" Auwal yace "toshikenan inkana ganin hakan shine mafita. Allah yakaimu goben" Lamido yace "Amin ya rabbi Auwal. Thank you"

Auwal yace "U're welcome" Lamido kallon wayar Auwal yayi sannan yakai hannu zai karba. hararanshi Auwal yayi ayayinda yayi sauri yaboye wayar a bayansa yana fadin "Mezakamin da waya kuma?" Lamido dan hargitsa gashin kansa yayi  sannan yamika ma Auwal hannunsa yace "kabani please...i'll try calling Rukayya again,may be I'll lucky tayi picking this time" harara Auwal ya watsa masa yace "inbaka kaje taki picking call dinka kasake ratsamin waya a kasa?toh badani ba wallahi tallahi" Auwal yayi maganar yana sake boye wayar a bayansa wanda hakan yasa Lamido matsawa kusa dashi yana sa hannu abayan Auwal din yana kokarin ansar wayar. Sauri Auwal yayi yatashi daga zaunen dayake ganin abunda Lamidon keyi yace "bazan fah bakaba,ka hakura kawai. Ina gobema zaka je Babban bulin kaganta" pity face Lamido yayi ayayinda yatashi daga zaunen yabi Auwal din yana fadin "haba Man. Kabani Mana please Allah bazansake ratsa maka ita akasaba" Auwal seya tsaya yana kallon Lamidon yanadan dariya yace "Waikai wani irin so kakema yarinyar nan hakane wai?" Murmushi Lamido yayi sannan yace "Bansani ba wallahi Auwal. nidai kawai nasan komi zatamin,koni yakamata inyi fushin indai ita bata fara saukowa ba ni zanci girma in hakura because I can't go angry with her,konayima cutan kaina nakeyi" Auwal seyashiga yima Lamido dariyar shakiyanci yana nunashi daga sama har kasa...
Yace "Dubi yanda Yar ficiciyar yarinya tamaida ka Romeon dole" Lamido yasaki tsaki yana dariya shima yace "Eh naji kafadi koma me zaka fada bazanga laifin ka ba. Nidai kabani waya inkirata please" Mika Masa wayar Auwal yayi yana dariya yace "gashi anma Inka sake ratsamin waya wallahi seka biya" karban wayar Lamido yayi yace "Naji" sannan yakoma kan gadon yayi kwanciyarsa yana cigaba da kiran layin sa amma har lokacin Rukayya batayi picking ba. Daga karshe dole ya hakura yamayar ma Auwal wayarsa.

QADRWhere stories live. Discover now